35

5.8K 537 24
                                    


Abunda ya faru ya hargitsa sauran shiryayyun kwakwalwar Anwar, tunda yake a duniya zai iya rantsewa bai ta6a shiga halin jindadi kamar na yau da Sa'adatu ta masa wasa ba. Kawar da kunya tayi gefe da masa wasannin da zai iya shek'e mai k'ararran kwana har sai da ya samu nitsuwa.
Sai da komai ya lafa ta juya tana rufe fuska wai ita kunya. (Ga abunda yawancinmu bamu sani ba. Yes, Namiji yana son mace mai kunya sannan kuma yana son fitsararriya amma a d'aki. A waje ki nuna masa kinfi kowa kunya in lokacin wanga abu yayi ki nuna baki san kalmar kunyar ba. Ehee.)
Jawota yayi jikinshi tana sussunne kai a kirjinshi ita fa lalle kunya take ji. Murmushi kawai yake yi ya ma kasa magana, a zuciyarshi kuwa godewa Allah yake da ya bashi Sa'adatu a matsayin matarsa ta sunnah.
Sun fi minti 4 a haka sannan ya samu ya dago fuskarta dake 6oye a kirjinshi ya manna mata kiss a goshi.
"Thank you." Ya furta a hankali yana ganin yanda ta runtse ido tak'i had'a ido dashi.
Tashi yayi yana jin kanshi kamar an yaye mishi duk wani bakin ciki da nauyin da ke zuciyarshi.
Kallonta yake yi yanda ta dukunkune a kan gado ta hanashi kallon kwayar idon wannan shahararriyar jarumar mai tafiyar da damuwa a cikin mintuna kalilan. Toilet ya shiga yayi wanka ya fito, ya samu ta gyara kan gadon ta shimfideshi ga sassanyar iskar dake shigowa ta window yana kada turaren da ta fesawa d'akin. Nan da nan kasala ta rufeshi ya kwanta nan d'aure da towel a k'ugunshi. Ko minti biyu bai cika ba bacci yayi awon gaba dashi, wanda gajiyar daren Angonci da kwanan Asibiti da rashin baccin safe da bai yi ba suka hadu suka sakashi nannauyan baccin da har Sa'adatu ta shigo bai sani ba.
Tsayawa tayi tana ganin yanda yayi nisa a baccinsa cikin kwanciyar hankali. Quarter million dinshi ta zubawa ido wanda tun kafin su yi aure yake burgeta ba kadan ba. Murmushi ne ya su6uce a bakinta da ta tuno da sambatun da yayi ta yi a lokacin da take gigitashi.
"Watarana zan tuna maka me ka fad'a." Ta ayyana a zuciyarta tana dariya a hankali.
Cikin sand'a ta taka ta ja glass din window tare da sauke labulen sannan ta kunna mishi AC.
Boxer dinshi ta dauko ta isa kan gado tana tunanin yanda zata saka mishi ba tare da ya farka ba.
"Baza kaji dadin bacci da towel a jikinka ba." Ta fad'a tamkar mai rad'a.
Cikin dabara ta yaye towel din ta fara zura mishi boxer din, da yayi motsi zata tsaya har sai ta ga ya kara komawa bacci sannan taci gaba. Sai da ta gama saka mishi ta lullu6eshi da bargo kana ta fito falon k'asa ta hakimce tana kallo, zuciyarta kuwa cike da kewan gidansu nan ma d'azu tayi waya dasu.

Kiran sallah da aka fara yayi dai-dai da shigowar Nana da Laila kowacce dauke da kulan abinci.
Ba sallama suka shigo suna ganinta suka ajiye abincin a bakin kofa suka rugo zuwa gurinta, tsayawa suka yi a tsakar kanta suna kallonta baki a washe. Ita kuwa shigowansu ba karamin tsoritata yayi ba har tana shirin gudu amma ganin murmushi a fuskarsu yasa ta dake ta tsaya.
"Kece Amaryar Abbanmu?" Laila ta jefo mata tambaya.
Sai yanzu ta gane ko su waye ne, 'yayan Anwar da uwargidansa Adama. Ba shakka yaran suna kama da ubansu musamman karamar wacce hatta kalar fatarsu d'ayane.
"Ehh nice. Me sunanku?" Sa'adatu ta tambayesu tana kamo hannunsu murmushi shimfid'e a fuskarta.
"Ni sunana Nana Aisha Anwar Bankud'i ita kuma Lailah." Cewar Nana tana nunasu da yatsa.
"Karya take yi, nima sunana Lailah Anwar Bankud'i, ko a class d'inmu haka ake kirana a Register."
Dariya Sa'adatu tayi suma din dariyar suke yi amma tasu bata da tushe.
"Yanzu kuzo muje side d'ina muyi hira. Abbanku yana bacci kar mu tasheshi ko?" Tace dasu tana tashi tsaye.
"A'a, Momy tace kar mu zauna idan mun kawo miki abincin." Cewar Nana.
Ita kuma Sa'adatu sai yanzu ta lura da abunda suka shigo dashi a can bakin k'ofa. D'aukowa tayi ta ajiye bisa Dinning Table sannan ta jasu suka fita bayan ta kashe kallon da ta kunna.
A hanya take jansu da tad'i har suka iso part dinta ta bude musu suka shiga, abunka da yaro sun ma manta uwarsu tace su dawo kar su zauna.
Adama dake bakin window tana jiran su dawo ta hangosu tafe suna hira. Sake labulen tayi ta zauna tana fatan Allah yasa Sa'adatu bata da matsala kamar Nazifa.

A can side d'in Nazifa kuwa tana can tana ramakon baccin da ta hana kanta jiya, tun lokacin da Anwar ya kamata tana shirin satar fita ta samu ta gudo d'aki, anan bacci ya sureta ba tare da ya shawarceta ba.

Sa'adatu kuma alwala tasa suka yi a toilet dinta na falo sannan ta shiga d'akinta tace in sun gama su shigo. Bayan sun gama cakud'edd'en alwalarsu suka banko kofa suka shigo d'akin nata.
Kallonsu tayi tana murmushi tace,
"Ba kuyi sallama ba da zaku shigo. A Islamiyyah fa malamai suna koyar da yara cewa in za'a shiga gida, d'aki ko falo a yi sallama."
"Nikam an koya mana." Cewar Lailah.
"Nima tun muna rabin aji aka koya mana." Nana ma ta fada.
"To meyasa bakwa yi?" Sa'adatu ta tambayesu tana rik'e ha6a irin mamakin nan idanunta a kansu.
"Muna yi fa." Suka had'a baki wajen fad'a.
"To ni dai tun zuwana ban ji kun yi ba. Maza ku koma ku yi inji ko kun iya."
Da gudu suka koma bakin k'ofa suka rangad'a tatacciyar sallama amma kafin ta amsa sun shigo. Dariya tayi har wushiryanta na bayyana tace,
"A'a ba haka ake cike hukuncin sallama ba. Idan mutum yayi sallama sai an amsa an bashi izinin shiga sannan zai shiga. Oya ku koma ku gwada ko yaran nawa sun iya."
Dariya suke yi cikin jin dadin kiransu da tayi da YARANA, suna ture juna suka fita sannan suka tsaya bakin kofa tare da yin sallama.
Amsawa tayi sannan tayi shiru ta gani ko zasu shigo. Suna nan dai tsaye basu shigo ba tace,
"Ku shigo."
Shigowa suka yi ta shimfid'a musu sallaya sannan tace wa Lailah taje ta d'auko musu hijabansu a gurin Momynsu.
Da gudu Lailah ta fita ta wuce side d'in Adama. Har zata shige room din Momynsu ta tuno Auntynsu tace su yi sallama, don haka ta bud'e murya ta fara kwada sallama.
Adama da fitowarta kenan daga toilet bayan tayi alwala ta ji Lailah na sallama a bakin kofa, tunaninta ko wasansu suke yi da Nana shiyasa ta share ta karisa bakin wardrobe dinta tana neman hijabin sallanta.
"Momy ko bakya nan ne?" Ta jiyo muryan Lailah na fad'i.
"Ina nan Lailah. Menene?"
"Tun d'azu ina miki sallama baki amsa ba kuma baki min izinin shiga ba." Cewar Lailah tana buga kafa a kasa.
Baki bude Adama ta amsa sallaman da Lailah ta sake yi, sannan tace ta shigo kamar yanda Lailan ta bukaci a fad'a mata.
Ai kuwa tana shigowa tace,
"Momy Aunty Sa'adatu tace in zamu shiga gida, d'aki ko falo mu dinga Sallama sannan mu jira in an bamu izinin shiga sai mu shiga. Yanzu ta aikoni tace ki bamu hijabanmu zamu yi sallah ne."
Adama dai tunda Lailah ta fara magana ta zuba mata ido, tana jin yanda take mata bayanin da ya dace a matsayinta na Uwarsu ita ya kamata ta nuna musu hakan tun farko amma ta kasa. Jiki a sanyaye ta nuna mata inda wankakkun suke, Lailah tana d'auka ta fice a guje bata son Auntyn nasu ta gaji da jiranta su yi sallan babu ita.
Tana fita Adama ta mere baki tace,
"Ita kuma nata salon kenan? To Allah yasa ya d'ore."

Dariya na yi nace,
"Nan ma baki san me aka yiwa Mijinki ba!. Gashi can a kwance yana baccin dadi, wanda rabon da yayi irinshi tun yana jariri."

Mum Fateey👌🏽

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now