48

7.7K 650 120
                                    



Adama tana idar da Sallah Maghrib ta karisa gaban mirrow ta fara make up. Step by step kamar yanda Jamila ta koya mata ta ke bi, bata yi mai yawa ba gudun kar ta kwaba fuskarta tun da bata kware ba.
Sai da ta gama ta bud'e wardrobe neman kayan da zata saka, ta jima tsaye kafin ta yanke shawarar d'aukar wani t-shirt mai layin orange da white, hannun rigar guntu ne iyakacin damatsanta, yayin da wuyan yake V-shape, sai wandonshi three quarter fari da ya kamata, ya kuma fito da hips d'inta. Kayan sun amsheta, ta yi kyau kamar ba ita ke da yara hud'u ba. Jujjuyawa ta dinga yi a gaban mirrow tana yabon kanta tana murmushi.

  Hijab ta d'auko, dogo mai hannu har k'asa ta rufe jikinta dashi, sannan ta d'auki cooler da ta sakawa Sa'adatu abinci ta tafi kai mata bayan ta rufe side d'inta

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Hijab ta d'auko, dogo mai hannu har k'asa ta rufe jikinta dashi, sannan ta d'auki cooler da ta sakawa Sa'adatu abinci ta tafi kai mata bayan ta rufe side d'inta.

Sallama ta yi a bakin k'ofar, kana ta shiga bayan Sa'adatu ta amsa mata.
"Kin cika alk'awari. Me na samu haka?" Cewar Sa'adatu tana kar6an cooler da Adama ke mik'a mata cike da jindad'i.
"Tuwo kika samu. Amma bansan ko kina ci ba." Adama ta bata amsa tana zama a kujera, da ganin fuskarta kasan ta fara sakewa da Sa'adatu.
"Ai kuwa ina son tuwo sosai. Nagode Maman Laila." Ta fad'a tana bud'e marfin, k'amshin miyar ne ya bugeta ta lashe baki tana cewa,
"Shiyasa Abban Laila ke yabon girkinki, daga jin k'amshi har na fara tunanin ya d'and'anonshi yake."
Adama dariya ta yi ta yarfe hannunta ta ce,
"Kyaleshi, neman magana ne kawai."
Itama Sa'adatun dariya ta yi ta tashi ta nufi kitchen tana cewa,
"Bari in d'auko plate kafin yawuna ya gama tsinkewa. I can't wait gaskiya."
Tana shiga wayar Adama ya fara neman agaji. Sunan _RUHEEY_ da ta gani, yasa ta d'an yi gyaran murya kafin ta d'auka.
"Hello, Assalamu alaikum ." Tace daga 6angarenta.
Amsawa yayi yana k'ok'arin bud'e motarsa da ke fake a gaban Plaza, yace
"Ya yinin yau? Hope kin yi missing d'ina?
"Da yawa ma, sosai Ruheey, yanda baka tsammani." Ta bashi amsa d'ai-d'ai a hankali, tana kallon Sa'adatu ta da fito daga kitchen. Hannu ta mata alamar zata tafi, Sa'adatu ma ta d'aga mata hannu, wanda gaba d'aya hankalinta na kan tuwon da take k'okarin bud'ewa. Da haka ta fita ta nufi part d'inshi, tace
"Ka ce me?" Don yayi magana bata ji sosai ba.
"Ina abun dad'ina?"
"Uhm, yana nan, amma da alama har yayi sanyi, tunda baka dawo da wuri ba." Ta fad'a tana duk'ar da kai k'asa kamar yana kallonta.
"Ba matsala, idan na dawo zan yi warming kayana, kinsan I'm damn good a hakan."
Murmushi ta yi cike da kunya tana jinta kamar a sararin samaniya tana yawo cikin gajimare. Tare suka yi ajiyar zuciya wanda kowa ya ji sautin na d'an uwansa.
"Hayateeh. Kin yarda?" Ya tambayeta cikin wata murya da tafi kama da rad'a.
Falonshi ta bud'e ta shiga ta nufi kan kujera ta zube a kai tana numfashi d'ai-d'ai.
"Kin yarda? Ya k'ara tambayarta a karo na biyu, ba tare da nuna k'osawa ba.
"I do. Nikam ka dawo gida." Ta furta a hankali, sai da ta fad'a ta rufe bakinta kunya kamar ta nitse k'asa.
Dariya sosai yayi sannan yace,
"Na san kaina Hayateey, sannan na fiki sanin kanki. Ki jirani nan da 5mins, I'm on my way home."
"Allah ya dawo min da kai lafiya."
"Ameen.

Kallon agogo take yi na fuskar wayarta, gani take lokacin baya tafiya yanda take so, tun d'azu minti biyu aka cire daga biyar d'in da ya bata.
Saboda rage lokaci, ta tashi ta shiga kitchen d'auko plates da cups, tana tafiya tana jin kanta kamar ba ita ba. Ita kad'ai ta san yanda take ji, burinta kawai ta ganta kusa da mijinta tana shak'ar k'amshin jikinshi.
Knocking da ake yi a k'ofar falon ya saka ta daskarewa a in da take na seconda uku, juyowa ta yi tana kallon hanyar da zata ga Ruheeynta, hakan kuwa yayi dai-dai da shigowarshi tare da sallama a d'an bakinshi mai zagaye da quarter million. Rufe k'ofar yayi da k'afarshi ya tsaya kallonta kamar yanda itama take kallonshi.
Daga tsakar kanta ya fara sannan ya sauk'o da idonshi har k'afanta, finally ya dawo da kallonshi kan fuskarta da ya tabbatar masa da yanayin da take ciki.
Rik'e take da plate a hannunta tana neman gurin ajiyewa, dariya yayi ganin rikicewarta kamar nashi, ajiye stuffs dinshi yayi a kan kujera ya nufota yana ware hannayenshi alamar ta zo.
"Ina jakar Latop d'inka?" Ta tambaya bakinta na d'an rawa, don tsabar bata ma san me zata fad'a ba.
Sai da ya jita a jikinshi sannan ya fara jin gajiyar da ya kwaso yana tafiya. Ajiyar zuciya ya sauk'e sannan yace,
"Good question, dalilin sauri in dawo gida gareki na mantashi a office. Ke fa? Ya na ganki rik'e da plate? Ko kin rasa gurin ajiyewa?"
Dukanshi ta yi a k'irji tana murmushi, kana ta raba jikinsu tana ajiye plate d'in a kan dinning.
"Yunwa nake ji." Ya fad'a yana mata wani irin kallo mai narka zuciya.
"Nahh, sai kayi wanka kafin kaci abinci." Ta fad'a a yayin da yake jawota jikinshi.
  "Ba yunwar Abinci ba." Ya bata amsa yana sunsunar wuyanta lokaci guda kuma yana cizon wuyan a hankali.
Sunyi minti biyar a haka suna abunda ya kamata kafin ya raba jikinsu ya mata kallon up and down yace,
"Kin yi kyau Hayateeh. Bana tunanin akwai wata halitta da ta fiki kyau."
"Thanks." Ta fad'a tana hard'e yatsunta tana murmushi kanta kuma a k'asa furkarta gaba daya tayi ja.
Bata barshi ya sake magana ba ta jashi kan ya tafi yayi wanka, don muddin suka kara wasu seconds din baza aci tuwon ba. Binta yayi amma bai yarda suka had'a kafad'a ba yace ta yi gaba zai bita a baya, dariya ta yi ta juya ta fara tafiya, shi kuma ya bita a baya yana cewa,
"60, 70, 80, 90."

Bayan sun shigo d'aki ta barshi yana cire kaya, ita kuma ta wuce toilet saisaita masa ruwa a shower zuwa d'umi.
Da kyar ya barta ta fito, don nacewa yayi wai ita zata masa. Sai da ta yi alk'awari kan zata mishi gobe sannan ya yarda ta fito.
Bayan sun gama cin abinci, suka dawo falo zaman kallo,
"An kawo miki motarki, tana can parking space." Ya fad'a yana gyara musu zama, da yake tana kan cinyarsa ne yana shinshinar wuyanta wanda hakan ya zame masa tamkar dabi'a.
"Kasan mantawa na yi ban fad'a maka ba, sorry."
"Na rigaki sani ai. Gobe zan fara koya miki, in kuma kina da tsoro in kyautar dashi." Ya fad'a yana dungurin kanta.
Hararanshi ta yi cikin wasa ta mak'e kad'afa alamar bata yarda ba. Murmushi yayi ya ce,
"Ina abun dad'ina?"
Diff lagon jikinta ya mutu na seconds kafin ta yi jarumtar dawowa hayyacinta, daidaita muryanta ta yi sannan tace,
"Kunun aya ne, kuma ka shanye."
"Kinsan illarshi a gareni amma kika bani. So, you have to be my Doctor tonight." Ya k'arisa maganar yana cizonta kad'an a fatar wuyanta.
Daga nan bata samu daman magana ba sai jin lips d'inshi da ta yi kan nata. Haka labarin ya canja suka raya Daren da zazzafan soyayya. Ko da suka yi bacci k'arfe uku na dare ya tasheta wai maranshi na ciwo, tana gigin bacci ta yi murmushi don tasan in da zancen ya kwana,
"Ka manta I'm your Doctor? Zo in duba abunda ke damunka Ruheey." Ta fad'a tana rufe filin dake tsakaninsu.

Nazifa ce zaune kan kujeran tsugunno a k'ofar gidansu tana hura wuta a murhu, sosai wutan ya bata wahala da hayak'i kafin ya kama, dalilin itacen sun yi katti ga basu bushe da kyau ba.
K'anwarta Bilki da ta dawo daga markad'en wake ta ajiye roban kullin a gabanta tana cewa,
"Ki koma cikin gida, zan karisa had'awa kafin Ma'u ta fito."
"A'a ki barshi. Ina ga kin manta jiya an sakaku a makaranta ko? Kije ki shirya kafin bakwai ta yi." Cewar Nazifa tana saka ludayi cikin kullin ta fara bugawa.
Ba yanda Bilki ta iya haka ta koma cikin gida ta barta nan zagaye da tsiraran mutanen da suka fara taruwa siyan kosan.
A falo ta samu Mamansu na aunawa wata yarinya Mangyad'a a galan d'in jarka, sai ta ta bari yarinyar ta tafi sannan ta dubi Maman da damuwa a fuskarta tace,
"Mama, nikam da kin hana Aunty Nazifa fita tuyan kosai a waje, wallahi baki ji yanda ake maganarta a unguwan nan ba, yanzu ma sai da nayi fad'a da Laraban Yari. Ni bana son zuwa makarantar ma, ta zauna a gida sai ina taya Ma'u da tuyan."
Shiru Mama ta yi na sakonni, kafin ta dubi Bilki 'yar shekar 19, tana karantar damuwar da ya bayyana a fuskarta.
"Kije kiyi shirin makaranta, karki manta yau zaku fara zuwa. Ita kuma zan mata magana mu ga abunda zai yiwu. Amma batun zuwa karatunku babu fashi Bilki." Ta fad'a tana goge hannunta da wani tsumma.
Bayan Bilki ta fita, ta zauna kan d'aya daga cikin kujerun falon, masu barazanar huda k'ashin mutum tsabar rashin taushinsu.
Tun dawowan Nazifa suke cikin wani irin hali na tsegumin makwabta, duk da hakan basu fasa tausaya mata ba na rabuwa da gidan mijinta da tayi.
Duk wasu kud'inta da ta tara, ta siya musu abinci, sannan ta saka k'anenta a makarantan masu kud'i dai-dai yanda zata cigaba da biya da sana'ar gwanjon da ta fara.
Kullum da asuba zata tashi ta gyara waken da za'ayi kosai dashi, daga nan Bilkisu ta kai markad'e sai ta fara suya kafin Ma'u ta fito. Da rana kuma su yi shinkafa da wake da miya, sai d'an wake. Awaran siyarwa da Ma'u take yi da dare kuma ta sokeshi, a cewarta shi ke fara illata tarbiyyar yara mata.
Da kyar ta lalla6i Ma'u aka sakata a makarantar Yak'i da Jahilci Arabi da Boko, wanda zata dinga zuwa k'arfe 1 zuwa 5 na yamma. Ma'u a shekarunta da take da 22 a yanzu cewa ta yi ta yi babba da shiga makaranta. Sai Bilki da d'an autansu Nazir d'an shekara 17 shima da farko ya k'i, daga baya ne ya yarda.
Nazifa ta fara neman maganin lalurarta, don tunda ta dawo ya fara mata kaikayi yana zubar da ruwa, sosai hankalinta ya tashi da na Mamanta suka tafi asibiti, bayan gwaje-gwaje aka d'aurata kan magunguna ta fara sha.

Wani yaro ne yazo ya tsaya gefenta yace a bashi k'osai na 50, sai ta ta gama d'iga wasu a kasko sannan ta zuba mishi a leda tana binshi da murmushi. Naira D'ari ya mik'a mata ta bashi canji, sannan ta soka a cikin ledan da suke tara kud'i. D'ago kanta da zata yi ta hango mutum tsaye nesa da ita jingine da mota yana kallonta.
Ido ta zuba mishi, zuciyarta na lugude kamar zai fad'o cikin cikinta, bata yi tsammanin zata sake had'uwa dashi ba, sannan mamaki ta ke me ya kawoshi gurinta kuma a wannan lokacin? Ko dai ya biyota ne?

Shin waye Nazifa ta hango?😜

Please Vote, Comment, Share and Fan.😍

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now