2

114 4 0
                                    

*✍️ Typing ✍️*
    
          *!!!💫Nana Firdausi💫!!!*

                 *Page 2*

            *Na*
                *Firdausi Wada Abdullahi   (Dearestfydooh😘)*

*CLEVERS WRITERS ASSOCIATION*

  Duk karar takun Daxeyi guda daya tare da xuciyar Nana yake bugawa
Tun kafin ya karaso Gareta ta kanKame jikinta ta fara Kuka tana Cewa dan Allah yaya kayi hkr baxan kuma Kin xuwa lesson ba,
Ko saurararta be ba yaxo ya kama hannunta yai tattaki xuwa bakin gadonsa ya xaunar da ita
yaje palor ya dauko tray din abincin data ajiye masa ya janyo table ya dora trayn akai yace Share hawayenki muci Abinci Snn ki Karbi hukunci dede da lefinki
tunda ke kin kasance me kunnan Kashi kinawa  umarni na zagon kasa. Nana ta marairaice tace
Wlh yaya na koshi ya wani Daka Mata Tsawa ba shiri ta janyo plate din daya Zuba Mata Doyan tana turawa do kyar kmr Zatae Amae
Shiko Gagan ya kafeta da ido Yana Kallon duk wani motsinta
Cikin nutsuwa yake cin abincin sa ba tare da tunanin halin da Nana xata Shiga ba Idan Taewa Cikinta lodi Can ta kallesa tace yaya dan Allah ka ajiyemun Cikin dare Idan Naji yunwa Xanxo naci ka Tanbayi mumy naci a binci daxu
ya wani kalleta ta gefan ido Snn yace Idan kuma Kinmin Karya fa,
da saurinta tace Kai kulikulin Kubra Dani
besan lokacin daya saki wani killer smile ba itama Kanta Abin Kallo ya xame Mata dan bata saba ganin murmushi atare dashi ba
Yana Gamawa ta Xabura xata dauke tray din Takai kitchen
Dan ta Samu hanyar guduwa yace xauna baby ban gama dake ba
      Ya tattara nutsuwarsa ya dawo da komansa Gareta ya kafeta da Ido yace baby Meyasa kika renani
Haka sauran sisters dinki suke ko ke dan mumy tana daure Miki Gindi
to ki saurareni duk randa kika Kuma Maimata abinda  kikasan na Hanaki wlh sena Miki Dukan da bantabawa wani ba Kuma ki tattaromun duk Tsofin uniform  dinki ki kawomun ya Daka Mata Tsawa yace ta Tashi masa Akan gado harta tafi da gudu ya dawo da ita yace waxe fitar Miki da Tray din
Ta tawo jikinta se karkarwa yake taxo dauka ya Kama kunnanta seda ta saki kara Sannan yace kici gaba da xuwa lesson da uniform Ko kidawo daga sch kice Kanki Yana ciwo Xakiga ydd xanyi dake, dama kince nayi Kuli Kuli dake ko
To ni har fura Senayi dake kisa aranki karatu nakeso Kiyi kuma dole ki cikamun burina ni da abbanah
Nana ta kuma Sakin Kara tace wlh yaya na tuba Nabi Allah ka cikamun Kunne Karya cire baxan kuma maka Lefi ba
Se Kuma tausayinta ya kamashi yace oya Bacemun dagani
sumsum Nana tayi waje Dakyar ta iya karasawa main palor Ko kitchen bataje ba ta dire ta dasa babin Kuka tana shure shure..........

mummy fitowanta kenan daga dakin alhaji ta dauro alwala xata hau sama tae sallah Shima alhaji ya fita ta Kofar baya ya tafi masallaci sallar isha'i nan tai toxali da Nana tana Kuka Tanbaya daya tae Mata tace jalal ne Ko
Nana tace Shine mumy Baya sona ya tsaneni nace na Dena masa lefi amman yayi ta murden kunne Ya kusan Cirawa Sannan ya cika
Mummy tae kwafa Jeki Dauro alwala Muyi Sallah a palon nan ydd xan ga shigowarsa ae dole xexo gaishe da Ubansa Idan nahau sama baxe ydd mu hadu ba Nifa bansan takura bafa haihuwarki yayi ba ya bari Idan ya haifi nasa yayi nan fa mumy ta Kama sababi ta Inda ta Shiga bata nan take fita ba

Tunda mumy ta Idar Sallah tana xaune kan Sallaya Nana ta Kwanta Cikinta suna jan carbi har alhaji babba ya shigo ya samesu
Mumy Data bi bayanshi da kallo taga bata ga jalal ba ta Kara hade rae.....
da gudu Nana ta Tashi ta Tareshi tace abbana yaushe ka dawo yace ban jima da shigowa ba Ko mamanki Batasan da saukata ba surprise nae mata ya kai hannu ya Shafa fuskarta yace wane ya saki Kuka Ko jalal ne naga ran mamanki a hade
Nana tayi murmushi tace shine ya Kusan ciremun Kunne
to Kidena Rashin jin mgn kinsan jalal Bayasan wasa
au haka zaka ce Ko alhaji to yayi masa kyau Dama Yana samun Daurin gindine daga gurinku kaida su alhaji Karami  to ina nan zezo ya Sameni alhj babba yayi murmushi axuciyarsa yace Halima da Yarta ya Kalli Nana da Hannunsu ke hade yace Nana maxa Taje ta dauko tsarabarsu ita da yan uwanta  ta Xabi colour dayayi mata ta Kai musu nasu
Da gudu Nana ta tafi tana Murna dan Tasan tsaraban abbanta dogayen Riguna ne masu kyau 
Sannan ya Juyo yace hajiya Halima dama kin hkra da jiran jalal muna fitowa sallah ya tafi gun Ubansa Yasan ya taba miki diya baxe shigo ynxu ba
kinsan Ko Be Miki Lefi ba Idan yaje gun Ubansa bakyasanin  lokacin dawowarsa Gara kixo ki samar min abinda xanci  Me dan Ruwa Ruwa ki Dena wnn fishin Ko Kema Kin samu tsaraba Me Kauri kmr ta yar taki mummy dako faraarta taki bari alhaji babba ya gani tayi kwafa ta Mike ta shiga kitchen

Bakajin kome se sautin dariyar su... ummi da tun shigowanta take sallama basujita ba har ta karaso Inda suke ta Ajiyema alhaji Karami fura da kilishinsa da yace Idan ya dawo Sallah Akawo mishi..... Ta Nemi guri ta Zauna tana me Farin Cikin ganin danta jalal
Cikin girmamawa jalal ya gaisheta ta Amsa cikin  sakin Fuska tare  da tanbayarsa mumy yace tana Can tana Xaman Jirana a palo Danma alhaji ya dawo ba xe Barta tayi Xaman Jiran ba
Ummi tayi murmushi daya Kara fito da ainihin kyawunta tace too.......
Ice ko ka Tabo Mata jikakkiyar yarta ne
nan fa Ummi ta Kama fada ni wlh bansan Meyasa yaya take haka ba ace yaro ba xaa masa Tsawaba se ta Kama Fadan Rashin gsky....
Kaine Baka taba Mata Dukan da bakinta baxe iya fada ba daka huta dakai Korafi ae
Shi dai jalal  kunyar Ummi ne ya kamasa yae Kasa da kansa se Sosawa yake Yana dariya Kasa Kasa yace haba umminah ynxu seki janyo akoreni daga gidan nan seka dawo nan dakinka Yana nan ae girma kayi ka gudu Part dinka Amma ban da abun yaya ta Samu Kana tsaye Kan wnn yartata Me kwalelen Ido ae Godiya Xata maka.......
Alhaji karami da tunda Suka fara hirar Besa Baki ba se ya tintsire da Dariya ya Kalleta yace ae Kamar kumbo kmr katanta har kece Xaki Cewa Swthrt me kwalelen Ido kin manta yarki Gatacan yayi nuni da Hibbah datake Jikin jalal a xaune tana cin kilishi abdurrahman da abdurraheem Da suke gefan jalal Suka kwashe da dariya suna tsokanar ta suna gwalo yar' Ummi Me Katon Ido ummi ta Tashi ta dau Yarta data fashe da kuka tace da Alheri nidae tinda kun hademun kai kuma Kuna neman sawa autah na Damuwa alhaji Karami ya tsagaita da Dariyar yace kiyi ahankali de Hafsa dan yartaki naga ta xama giwa kamr Kara Mata Nauyi ake ummi tae sama Abinta tana lallashin diyarta

Ummi na fita alhaji Karami ya maida hankli Kan jalal yace matso my son muci Abinci se Muyi mgnr da xamuyi
Jalal dake Akoshe yake Dakyar ya daure Yaci kilishin Kadan sbd Idan yace ya Koshi fishi xeyi dashi dan Yasha fada masa Koya Koshi Idan Yaxo ya sameshi Yana cin abinci yasa hannu suci hkn yana tuna masa da kuruciyarsa su abdurrahman ma Basu sha furar ba kilishin kawae Sukaci alhaji ne Yasha furarsa Sosae dansu kmr gadon shan fura Sukai gun hajiya Goggo

Bayan sun Kammala ne Suka tattauna matsalolunsu daya shafi asibitinsu wdd alhakin Kula dashi Yana karkashin jalal din Tunda shi alhaji Karami ba Maxauni bane dan haka ya dora jalal kan duk abinda ya Shafi asibitin....basu Suka gama Kammala tattaunawarsu ba se Wajan goman dare Sannan yama Abban nasa Sallama ya tafi........
Yana tafe a hanya Yana murmushi besan Me yasa ba Yana tsintar kansa Cikin matsanancin farin ciki Idan Yana tare da Abbansa yanajin soyayyar umminsa acikin xuciyarsa fiye da mahaifiyarsa Yakara murmushi a Karo na biyu dan tunawa da yayi seda akayi da gske Kafin Ummi ta dena Goyashi sbd kulawar data Bashi a rayuwa ya kaunacesu ita da Abbansa Wato alhaji karami........
Da a part din ummi yake Dalilin Nana ta gudu gun mummy shine Shima Dalilin komawarsa gun mummy Amma shi yafi jin Dadin xama gun Abbansa sbd soyayyar Nana ajininsa take tun yarinta tare Suka Renata Shida umminsa kmr ydd Ummi ta Bashi kulawa Shima hkn yake bawa Nana ........

Kansa tsaye ya shiga part din mumy
Alamun Motsin Dayaji ne yasa shi tsayawa Cak yake Jira yaga Ko mummy ke Xaman jiranshi ta masa fada Kan Nana se yayi shiru ya maida hnklinsa Inda Yake jin Motsin Seya fahimci mumy ce ta Shiga part din Alhji babba ta rufe kofa ya Sauke Ajiyar xuciya Me karfi yayi sanda ya haye sama
A hankali ya Murda handle na dakin Nana ya Shiga ya Nemi makun'nar fitila ya Kunna ya Rage Mata Karfin AC  Nana Ko Idanta biyu Tana karanta wani English novel jin xaa shigo dakinta ta boye buk Din tinaninta mumy ce
Sannu a hankali ya taka Yaje Kanta ya tsaya ya Kare Mata Kallo Yana ta Saka Abubuwa masu yawa acikin xuciyar sa
Ya saki wani murmushi daya karama fuskarsa kyau ya tsuguna ya shafi gefan fuskarta ya gyara Mata abun Rufa ya sann ya shafa goshinta  ya kashe makunnar fitila ya juya ze tafi dakinsa zuciyarsa na masa sake sake kar ya hadu d mumy......
ya murda handle na Kofar Ze fita Yaji karar takun mummy ta tawo sama gun Nana.................

    *✍️Edited by Maman shukhrah✍️*

Nana FirdausiWhere stories live. Discover now