4

84 3 0
                                    

*✍️ Typing ✍️*
    
          *!!!💫Nana Firdausi💫!!!*

                 *Page 4*

            *Na*
                *Firdausi Wada Abdullahi   (Dearestfydooh😘)*

*CLEVERS WRITERS ASSOCIATION*

Karar fashewar glass cup din Hannun mumy ne yasa jalal saurin karasawa gareta Yanawa mumyn Sannu amma dae Baki kone ba ko? mumy da hannu ta masa alamar Karya Karaso gareta ta Tsallake fasassun glass cup din tayi part dinta,,,,  juyowar da Jalal xe yaga Nana ajikin bilal Yana lallashinta,
Karasawa yayi ya dakko mata hijabin data jefar Yaxo ya cirota daga jikin bilal Yasa mata hijabin... da hannu ya Nuna Mata Kofar parlo hakan yana Nufin ta tafi kenan Kwayar Idansa kawae ta Kalla taga ta Canxa launi tasan ba sauki sum sum ta fice tabi ayarin yan'uwanta Suka tafi tahfiz
duk Abinda yake bilal na Kallonsa yasan dae jalal bason Nana yake ba dan sunyiwa junansu alkawarin aure Shida Amrah kuma Nana tayi yarinta game da raayin abokinshi Yasha fada masa In'suna hira Bayasan auren mace me kuriciya''''
Yana Cikin zancan Xuci yaji saukar Hannun abokin Nashi a kafadarsa da murmushi akan fuskarsa ya Juyo ya Kama hannun abokin nashi yace guy ya hakane gaba daya ka firgita mumy da Yarta jalal ya sauke ajiyar xuciya ya fesar da wani huci wdd ya fito daga karkashin xuciyarsa.....ya Kalli bilal yace bawae banason Nana taxo gareka bane aa kawai na mata tsawane dan tayi girma da irin wnn gaisuwar idan kowa xata masa haka Ko mace Ko Namiji wani xe iya anfani da hakan ya bata Mata goben ta...... bilal ya kece da dariya yace na fahimceka guy tinaninka Kullum Kara zurfi yake amma kmr ran mumy ya baci Kodan batasan meye dalilin firgicin Yarta bane ya kamata kai Kokarin fahimtar da ita manufarka...... ba damuwa guy baxan tare ta da mgnr ynxu ba se alhaji ya dawo xatafi gane bayanansa akan nawa........
Kaxo muje part dina nadan sake watsa ruwa semu fita ...
aa gsky Muje na gaida mumy tukunna semu wuce,
haba guy ka rabu da mumy ae anan Xamuyi lunch da dare  Kwa gaisa time din Kasan ynxu fishi take nasa Nana Kuka.....a ina Xamu hadu da Suhailan ne....I thing kmr British tace mun Xamu hadu Koma dae meye ka shirya mu fita baga waya ba,,,,, kaga ydd ta hadu kuwa sau daya Na taba ganinta yau shine haduwa na biyu pix dinmu da take gani ta matsamun naxo dakai wae Kana burgeta da a club  tace Xamu hadu nace wlh baka zuwa club in dae tanaso ta ganka sedae a can xa guri shine tace mu hadu a British...... Jalal yae murmushi Yana Kokarin cire botir na rigarsa
Yace kace zaxxafa ce  wannan..... bilal yace me karfin gaske kuwa har tana konani.....  sukasa dariya Suka tafa Snn jalal yace
Nima fa nest week Amrah xata dawo Nigeria gabadaya kewarta na damuna ba xan kuma ydd nakae 3 month ba tare da ita ba inajin fa nesa taxo kusa  meyt be se na rigaka aure kai ka tsaya ruwan ido daga me Sanyi ka dawo xaxxafa gaba Suka bushe da Dariya hade da tafawa Sakai part dinsa...... suna shigewa yalwa Taxo ta gyara gun da custard ya xube ta kwashe fasassun glass cup din ta dakko Mopper to goge gurin tas san nan ta Koma Kan aikinta''''''
Bayan ya gama shiryawa suka fito se suka shigo ta Parlon mumy Dan suyi Mata Sallama dan jalal baya fita ba tare da adduar mumy ba suna Shiga Suka ganta xaune tana karanta Jarida nan bilal ya gaisheta Cikin sakin Fuska ta amsa masa tare da tanbayar Mutanan gidan su yace kowa lpy suna gaisheku Snn ya tashi xasu tafi..... Se jalal  yace mumy xamuje unguwa ki mana addua tace Allah ya kiyaye har Yayi taku biyu ya juyo yace mummy kisa Nana ta mana lunch Nida Bilal da dare xamuci Idan mun dawo pls..... Ko kala mumy batace ba.... da yaga Baxata kulasu ba se sukai  murmushi Suka fice.......
suna fita bilal ya daki kafadar abokinsa yace Sannu da kokari Guy Kawae muyi lunch din'mu a waje mumy fishi takeyi dakai fa...... rabu da ita guy gani take kmr tafini san Nana  soyayyar Nana acikin Jinina take yawo ita mumy Batasan Matsawa yaro su Kuma Yaran ynxu seda haka xata sakko ne bari mu dawo ka gani.....

Tun Fitarsu jalal mumy na xaune .....
a nan parlon tayi lunch na rana tayi sallah har su nana suka dawo daga tahfiz Suka Sameta
tace sanunku da dawowa sukace Sannu da gida mummy..... dake gaba dayansu Suka shigo....
Shukhra Surayya da Nana anan mumy ta rikesu sukai lunch sukai sallah Sannan sukace mummy xamu Shiga ciki se mummy tace ku fadawa hajiya anjima Kadan Idan rana ta Kara Sanyi kuxo xan aikeku gidan hajiya Jamila
Suka amsa da to mummy se mun fito
Bayan Fitarsu mumy ta Janyo Nana jikinta tace mene ya hadaki da jalal Daxun Kuka kusan sawa na kone da custard
Nan Nana tace Tafiya nayi da gudu xanyiwa yaya bilal oyoyo shine ya dakamun tsawa kiyi Hakuri mummy Nima bansan nayi wannan karar ba gaba daya firgitani yayi.....
Ba kome my doughter amma daga yau ban yarda Ko jalal Kina yiwa  irin wannan oyoyon ba kefa ynxu ba yarinya bace Nima duk randa na kuma ganin kinyi hakan to tamuce nida ke ki kiyaye hakkin Allah akanki Shima seya kiyayeki...... to mumy in Allah ya yarda baxan kuma ba.....
yawwa daughter na  idan ya dawo kije ki bashi hakuri aa mumy ki bashi da Kanki kice injini inajin tsoron xuwa Karya ciremun Kunne
mummy tae Murmushi tace baxe miki kome ba tunda yaga kinsan Kin Aekata Lefi Kuma kin nemi afuwa to mumy xanje Yana daki ne ......
aa baya nan sunfita da bilal Idan ya dawo kyaje ynxu kije
ki Shirya banasan suxo su jiraki kujemun gidan hajiya Jamila ku karbo mun sako Idan Kunje Karku xauna kixo ki shiryawa su jalal abincin dare Shida bilal kinsan Bayan magrib yake lunch Karkuje ku xauna Yaxo Yana miki fada......
    to mumy ba naje na shirya....har Nana tahau sama ta Sakko da gudunta taje ta bude Cabinet  ta Dakko gaban ta data ajiye da daita xata tahfiz se kuma yaya deen ya firgita ta ta Manta Bata dauka ba......
               !!!Nana na shiga daki ruwa Kawae ta watsa ta Dan shafa lotion kadan ta dakko sabuwar doguwar rigar da abbanta ya Kawo musu jiya tasa ta daure gashinta da ribon tayi Mata kyau sosae to Dakko Gyalan rigar ta yafa tasa lips Kadan dan ko powder bata sa ba dake ita Batasan make up rigar ko ta xauna Mata ajiki dasss.... tadan fesa Spray Kadan tasa takalminta Kalar rigar ta janyo Kofarta ta fito tun tana sakkowa daga stairs mumy ke Cewa Masha Allah diyata seme Jirgin sama xan bawa Nana ko se murmushi take tana rufe fuska da gyalanta..... tana karasowa gurin mumy suma su shukrah suna shigowa parlon kmr hadin baki suma doguwar rigar sukasa Wacca Abban ya Kawo musu mumy tace Masha Allah Yan'matan mumy Allah ya Kawo maxaje nagari duk kunya ta kamasu Suka Kama rufe fuska nan sukai wa mummyn sallama Suka tafi Gidan hajiya Jamilan...

Suna tafe suna hirarsu kowa ya gansu se yayi shaawarsu kayansu iri daya Amma kowa da colour tasa rigar
sannu a hankali suka isa gidan hajiya Jamila dake ba nisa gidan bayan layinsu ne...
sun gaisa Cikin girmamawa nan ta daukesu da hira in Sukai yin'kurin tafiya seta hanasu tace ba ynxu ba su kara hutawa suna nan tana Jansu da hira har Kusan magriba Sannan sukace xasu tafi se ta dakko sakon mumyn ta basu Sukai Mata Sallama Suka tafi........
Tun fitowarsu daga layin gidan hajiya Jamila Sakai Kacibus da wata Motor xata shigo Layin wani kyakkyawan matashin yaro yake tukin motor ganin Kallon da ya kafe Nana dashi Yasa Suka falla masa harara Sukai gaba abinsu
suna tafe Yana binsu Basu Sani ba har Suka shigo Cikin Layinsu Kawae se hango motor sukae na bin bayansu da Yaxo kusa dasu Seya fito daga motor yake binsu da Kafa
Yana karasowa gurinsu yace amincin Allah ya Tabbata agareki ya maabociyar haske gaba daya Suka Kama Kallo Kallon surayya tace dawa Kake mgn anan se yayi nuni da Nana Shukrah da Surayya se Suka dan matsa gefa Kafin ya firta wata kalma su Surayya Sun fita da gudu sakamakon ganin motor yaya Deen na tunkarosu ita Kuma Nana Baya ta bashi ba taga shigowar motor layin ba sejin muryar Shukra taji na Cewa Nana ga yaya deen nan kixo mu tafi Kafin ya Ankara duk sun bacewa ganinshi sun shige wani make Ken gida........ da gudu Yaji wucin wata Motor ta giftashi ta tinkari wnn katan gidan
Ya sauke wata nannauyar ajiyar xuciya ya Kalli Inda Nana ta shige ba abinda ya Karu dashi se sunanta !!Nanaa!! kmr haka Yaji sisters nata sun kirata ya saki murmushi yana Sosa kanshi Se kuma ya juya ya Koma ya Shiga motarshi ya bar layin.......
       Ko gama Parking na motor bilal Beyi ba jalal ya bude motor ya fito Yana wuci yayi part din Mumy
Da wuci ya shiga Parlon kmr mahaukacin Zaki Tashi daya Idansa ya Canxa kala yana Kallan ta Inda zega su Nana bega kowa ba se karar takun mumy daYaji tana sakkowa daga stairs Cikin bacin Rae da zafin xuciya yace mumy da izinin wa su Nana suka fita waje....
Mummy ta Kalleshi ta watsar tace dole na fada ma gskya ubana tinda kaxo ka tsareni da ido ae yakamata nae Kokarin Sanar dakae to ka karkade kunnanka da kyau Kaji da izinina Suka fita se me...............
    *✍️Edited by Maman shukhrah✍️*

Nana FirdausiWhere stories live. Discover now