5

144 13 0
                                    

Zumuncin Zamani.

Na

Nazeefah Sabo Nashe

Littafin kyauta ne

📄 5
(Sannu da jimirin typing Fateemah Sabi'u Dankaka. Ina godiya k'warai da gaske, ubangiji ya fi ni yabawa.)



Kad'an- kad'an d'in na zuba masa, na mik'e na bar wajen, d'akina ma na shige kwanciyata nayi sosai flat, ina tunanin irin wula'kancin  da muka sha wai k'iri-k'iri da d'an uwan ka sai ka na  da shi sannan yake kallanka da daraja da k'ima. Sosai zuciyata take bugawa, yanzu dai dubi mu da muka je muka sha uwar rana, wai da pure water aka sadamu. Shikuwa da yaje a cikin mota mai AC an sada shi da garar abinci da na tabbatar ba zai iya cinye wa ba, duk a dalilin shi mai kudine zai rama abinda ake yi masa ko ma fiye da haka. Mhmn! Duniya kenan makaranta ce!

Ina ji da zai tafi umma tana cewa bari ta kira ni na kai masa ragowar abincin mota. Ya ce "Haba Umma me Zan yi da shi? yau dai kin huta da yiwa gwaurayen gidan girki."
Umma dariya tayi tana sake zuba  masa godiya.
D'aga labulen d'akina ta yi ta ce "Ke sai ki zo ki d'ebi abincin kici don nasan kina jin yunwa.
Da sauri na girgiza kai ta ce, "ke kika jiyo, wallahi Sauda ina raba ki da wannan shegiyar bak'ar zuciyar, ba inda Zata Kai ki don kuwa ynzu wannan duniyar haka ta rikid'e ta koma, ba a komai don Allah, mai shi abokin mai shi ne, talaka abokin talaka d'an uwansa. Kuma daman bahaushhe yace k'warya  ta bi  k'warya, daidai ruwa daidai gari, ba a ganin ka da gashi wannan zamanin sai idan  kana da shi. Don haka nake son ki sanyawa zuciyar ki salama. Kina jina?
D'agawa Umma Kai nayi da k'yar don kam ba ni da bakin magana.
Umma ta juya tabar d'akin, ni kuwa sake runtse idona na yi wasu zafafan k'walla suna zubo min, sosai nake jin zafi da radadin abin a  cikin raina.

Tun safe na shirya don son zuwa na karb'i results d'ina a makaranta, burina tun a can baya ya ta'allak'a  a kan na samu karatu mai zurfi, na tallafawa mahaifina,Akwai hakan a cikin raina da wannan burin kuma na taso.

Cikin atamfa ta k'aramar super mai k'aramin kud'i sosai, koriya na shirya na saka hijabi da zai dace da atamfar bayan na nad'e  gashin kaina da ya zama kamar na sanya ribbon din a cuci maxa, powder kawai na sanya a fuskata sai man leb'e na zizara gazal a idona, don ni Sam ba ma'abociyar son kwalliya bace.
Ina Shirin fita daga gidan naji sallamarsa. Tsaki na zabga masa, don ni sam ban ga dalilin yi mana zarya a gida ba. Koda yaushe a yanzu kam na tabbatar da nagartar halayansa. Sam shi baya daga cikinsu.
Anutse na kalli umma na furta  "Umma sai na dawo a yimin addu'a"
Umma tasaki murmushi  ta dafa kaina ta fara yi min addu'ar da ta saba in dai zan fita ta neman tsari daga sharrikan zamani. Ta na gamawa ta saki kan ta ce "Allah yaba da saa."
Da k'yar na kalli Yaya Hisham fuskata a d'an had'e na ce "Ina kwana?"
Shima a nutse ya ce "Lafiya" batare da ya kalle ni ba
Na fita ina tab'e baki a zuciyata na ce, kai ka jiyo..

A makaranta tun daga bakin gate duk malamin da na had'u da shi cikin farin ciki yake cewa "Saudat congrats" Anutse nake amsawa cikin murmushi duk da ban san dalilin wannan congrats da ake yi min ba.
Da sallama na shiga office din examiner. Yana gani na shi ma ya saki murmushi. Babbar "k'waruwa barka da zuwa."
Ni dai na saki murmushi na gaishe shi, ya nuna min wajen zama yace,  "Zauna mana Saudat daman ina da niyyar idan baki zo ba  ni na je har gidan na sameki, saboda abin alherin daya sameki. Saudat kin lashe sakamakon jarrabawar ki duk with an excellent results, wannan dalilin ya saka gwamnati ta d'auki nauyin karatun ki a duk inda kike son karatu a fad'in duniyar nan,tare da scholarship mai nauyin gaske."
Cikin tsananin farin ciki na d'aga hannaye sama ina yi wa ubangiji Godiya.idaniyata na kwararar da siraran hawaye. Malam Umar murmushi ya saki ya ce "Dole ki yi kuka saudat don kam abin musamman ne na farin ciki ake wa hawaye"
Na d'ago kaina cikin lumsassun idona na ce "Malam nagode, ubangiji ya fi ni yabawa, bari na yi sauri na isa gida na sanar da su Umma wannan abin alherin da ya samemu."
Malam ya gyad'a  Kai ya ce "Maza ki hanzarta kam, Amman kafin ki tafi ki biya office din principal ta ce idan kin zo na tura mata ke."
Na gyad'a  kaina had'e  da karb'ar kwalin results d'ina.Na rungume shi a k'irjina cikin tsananin farin ciki.
Da sallama na isa office d'in principal, tana gani na ta mik'e tana murmushi ta ce "Welcomed gifted"
Da sauri na durk'usa na gaishe ta. Ta xagayo ta kama hannuna tana fad'in," Ina alfahari dake sauda na yi burin ina ma a ce daga jikina ki ka fito" haka tayi ta nuna murnar ta a zahiri, da zan tafi ta sanar da ni akwai taran da makaranta ta shirya min sati mai zuwa tare da fatan zan zo.
Na d'aga mata kai had'e da fad'in "Insha Allah mah"

Da gudu na shiga gidanmu na fada kan cinyar umma ina cewa "Umma na,ki taya ni murna na cinye jarrabawar duka, har gwamnati ta dauki nauyin karatuna duk k'asar da nake so a fad'in duniyar nan.
Da sauri Umma ta mik'e tana cewa " Alhamdulillah, Allah mun gode maka sauda da gaske kike ko wasa?"
Na ce "Wallahi umma da gaske nake, na nuna mata takardar ta sake cewa "Alhamdulillah Alhamdulillah,mun godewa Allah.
Ranar har dare zancen makaranta kawai a gidan yayyena kuwa, kowa  da k'asar da yake cewa in je. Abba dai yana jin su ya yi musu Shiru bai ce komai ba sai da aka gama mahawarar ya dubeni ya ce "Saudat  ki na son ki fita waje karatu?"
Da sauri na d'aga kai da nufin jaddada masa ina son zuwa.

Abba yayi murmushi ya ce "Saudat a wannan karon gaskiya sai dai ki yimin hak'uri Zan tauye ki kad'an Sauda ba Zan iya barin 'yah mace ta k'etare  zuwa wata k'asar karatu ba, a cikin garin nan ma a dole zan bari,sabida haka ki za b'i  d'aya daga cikin makarantun da suke nan garin na kano, ba ma wani garin ba. Dafatan ban tauyeki ba, ba zan take umarnin musulunci ba saboda burace-buracen duniya."

Da sauri na girgiza kai don sam ni ban ga abin tsanantawa ba na ce "Abba ba komai, duk d'aya ne da nan da can d'in, fatanmu ubangiji ya bamu albarka a cikin ilimin.
Abba ya girgiza kai yana cewa Masha Allah, madallah da haihuwa y'a ta gari."
Na ce,"Nagode Abba"Ina kallon yayyena sam ba su ji dad'in  hukuncin da ya yanke ba sai dai ba yarda za su yi.

Daidai lokacin sallamar Yaya Hisham ta ratsa kunnenmu, cikin farin ciki suka tareshi ni d'in ma ba yabo ba fallasa na gaida shi. Abba ne ya rattabo masa labarin jarrabawa ta.
Da sauri ya juyo ya kalleni Yana murmushi yake fad'in"Masha Allah, ashe kina da k'ok'ari?"
Murmushi kawai na yi na mik'e  na shiga d'aki haka kawai sai na ji bana son zama kusa da shi sau tari sai na ji zuciyata tana lugude a duk sanda zan ji muryarsa ko na gan shi ko na shak'i k'amshin turarensa. Sai naji yana cewa "Lallai zamu fara shirin ai na zata  tsiwar ce kawai ba k'wak'walwa.
Abba ya ce Saudat kenan kowa yana fad'in  wannan tsiwar ta ta,sam ba tada sauk'in hali da sau'kin zuciya.
Hisham ya ce "Lallai kam, sai dai da sau'kin ta tunda dai tana da k'ok'ari."
Ni dai ina daga cikin d'aki ina jiyo hirar ta su ban san barci ya dauke ni ba. Zuciyata cike take taf da farin ciki marar misaltuwa.

Jikar Nashe ce.

❤️❤️❤️❤️❤️🙏

08033748387

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now