13

105 7 0
                                    

Zumuncin Zamani (New update)

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

Typing: fadima Sabi'u Dankaka

(Allah ya baki abinda kike nema duniya da lahira.)

Zuciyar Hisham ta sake k'ullewa da tarin bak'in cikin maganganun Inna falmata. ya ilahi, ayi mutane sam babu Allah a ransu? Dubi dai yanzu duk wadatar da Allah ya bata ammn hangen abun wani take yi, ya kuwa za a yi imani ya ratsa mutum, shi yasa kullum mutane ba sa godewa Allah in dai za ka hango na samanka, yanzu falmata nawa ta fi wadatar amman hangen na wani take.
Ganin Hisham ya yi tsit, hakan ya sa Inna falmata ta gyara zamanta tana kallonsa, tace "Hisham kayi shiru?"
D'ago kai ya yi yace "Bakomai Inna dama wata magana ce ta kawo ni."
Inna falmata tace "to ina  jin ka,ga me da me?"
Hisham ya saki ajiyar zuciya ya ce da man mun yi magana da Abba akan mata biyu nake son na aura.to sam Abba  ya k'i ya amince min, kuma na riga na yi alk'awari  a gidan su yarinayr, ba nason na zama k'aramin mutum."
Inna falmata ta gyara zama kafin ta ce "Gaskiya babu dad'i, tunda da dai har ka yi magana a gidansu, ita kuma yarinyar wane ne babanta?"

Hisham ya d'an zunkud'a kafin ya ce "To kin ga Inna abinda nake gaya wa Abba kenan, sam ya kasa fahimta, bafa wata ba ce yarinayr, Saudat ce y'ar gidan Abba  Mustafa"

Da sauri Inna ta zaro ido ta ce " " 'yar gidan mustapha?  Lallai ubanka ya k'i amince maka, wa  zai so ya had'a jininsa da Jinin tsiya? Kai ma dai ka zama sakarai, bar ganin ana maka murna ka taso da nasibi wallahi idan ka had'a jini da jinin Mustafa tsaf za su tsiyataka, don tsiya a jininsu ta ke. Kuma tilas Babanka ya hanaka ana murna ka rab'i arziki, kana  rab'o wa kanka tsiya?"
Hisham mikewa kawai ya yi ba tare da ya sake cewa kanzil ba illa, "Sai anjima"

Falmata ta watsa masa wani kallo, sannan ta ce mu jima da yawa,banda abin ma yaran zamani ina tsiya ina y'ay'an Mustafa da talauci ya yi wa katutu?
Hisham ko da ya shiga mota sunkuyar da kansa ya yi a kan sitiyarin Yana mamakin mutane masu k'in jinin Y'an uwansu saboda talauci. Direct gidan wani abokinsa ya wuce wanda ake kira nejeeb ya yi sa'a kuwa ya same shi a gidan.
Cikin farin ciki najeeb ya tare shi. Bayan  son gaisa Hisham ya Sanar dashi halin da yake ciki, najeeb tsit ya yi yana son gano wa abokin nasa mafita, duk da shi yana ganin wautar abokin nasa na zab'ar d'iyar talakawa, akan y'ar  sanata, a sanatocin ma babanta shine senate president, tabbas abokin nasa yana shirin tafka babban kuskure, sai  dai hausawaa sun ce daidan wani karkataccen Wani, tunanin hakan yasa ya dubi abokin nasa ya ce "ina ganin fareeda zaka samu ka sanar da ita halin da kake ciki, kasan mata da tausayi musamman idan suna sonka,sai ka ga ta tausaya maka har ta lallaba iyayenka su amince da batun."

A take Hisham ya amince da batun abokin nasa. bayan sunyi sallama ya karkata akalar motarsa, zuwa gidan su Fareeda da yake nassarawa G.R.A Kano
Yana danna lambar wayarta bugu d'aya ta d'auka cikin tattausan kalami ya ce, "Ran gimbiya ya dad'e ga ni a k'ofar gidanku"
Mamaki ya kama fareeda don ta dad'e ba ta ji kalamii irin wannan daga gareshi ba. Sai  dai ta danne mamakin nata ta hanyar sauya mayafi ta fice harabar gidan.


A cikin motar ta same shi bayan sun gaisa ta ce "ya aka yi? Na  ga kana ta doka murmushi?"Hisham ya d'an lumshe ido ya ce, "Ina  kallo tsananin kyan da uwargidata tayine."
Fareeda ta saki murmushi jin dad'i ta ce "Uwargida kuma amarya ba, ka san ina da tsananin kishi, don haka daga ni babu K'ari"
Dam!! Dam!! K'irjin Hisham ya buga, don kuwa bai hango dacewa a wajen ba, cikin k'arfin hali ya daure ya ce "a haba ai yanzu mata kansu ya waye, sun daina wannan tsananin kishi........

"Ban dani Hisham, don kuwa zafin kishina ya wuce duk yadda kake zato." fareeda ta fad'a a hassale "Don kuwa wallahi da mace ta yi kishi dani zata gwammace ta fad'a rijiya ko ta rungumi transformers......

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now