14

114 9 0
                                    

Saeed ko girgixa kai ya yi ya zabga tsaki kafin ya ce',ba ma tilas ta hakura da auren sa ba, ai ko shi ne autan maxa ba xata aure shi ba.

Umman su kuwa tana daki ta zabga uban tagumi Abba mustapha ya girgiza kai " yanxu fisabillah umman sauda ba xa ki yi shiru da hawayen nan ba? Kada kii manta,ita fa rayuwar nan yanzu haka take sai kana dashi sananan kake xama mutum.idan kuwa ba xa ka da shi kare ma yafi ka daraja. Shi yasa yanxu mutane idonsu ya afu da Neman kudi ko ta wace hanya wanda nake rokan Allah ya kare ni daga fadawa sharrin zuciya. Ina son don Allah ki jajirce ki zama mace jaruma kada wanann abun ya dame ki...

Girgixa kai umma ta yi tace "Abba sauda dubi fa irin cin mutunci da mutumin nan ya yi mana.ya ilahi me mutane suke son su mayar da xumincin ne?
Abba ya girgiza kai ya ce'"babu komai,kansa ya yi wa. Ina rokon Allah Kuma ya ganar da shi gaskiya"daga haka ya juyo carbinsa ya ci gaba da laziminsa hakan ya tabbatar wa da umma da ba ya son magana a lokacin

Jikin umma a sabule ta mike ta bar dakin zuciyar ta cikin xafi da mutukar Kuna,
Shi kuwa Hisham tunda ya yi parking ya dire mahaifinsa a sukwane ya ja motar ya bata wuta,bai zame ko ina ba sai wani park,flat ya kwanta a kan ciyayi,zuciyar sa naci gaba da yi masa wani tukukun bakin ciki idan ya tuno kalaman da mahaifin nasa ya yi amfani da su wajen cin mutunci bayin Allah nan me suka yi masa? Kawai dalilin talauci sai mutum ya zama tababbe?

Ya rintse ido kafin ya ciro waya ya kira wayar saudat sai dai haka tayi ta ringin ba a dauka ba shi kenan ya sani saudat ta rabu da.soyyarsa , ko wacce ce ma kuma xa ta aikata haka,ya ayyanaa hakan a ransa tabbas idan har bai auri sauda ba shi kenan farin cikin sa ya kare a rayuwa, ya zai yine? Kuma a ina zai samu mafita

Alhaji hamza kuwa ko da ya shiga gidansa dariya ya shiga kyakyatawa tamkar wani zararre.matarsa.balaraba ta dube shi kafin ta ce "lafiya alhaji??
Ya yi tsaki hade da cewa" ni da wadannan matsiyatan mutanan ne su sun zata da gaske neman aure na je har da wani malala min tabarma. Ni kuwa na zage su tass na ci musu mutunci

Hajiya laraba ta saki murmushi ta ce "ai ni na zata da gaske kake ina nan ina ta tsuma ina jiran ka dawo naji dalilinka na aikata haka.
Alhji hamza ya ce ni mahaukacine ina ne zan yarda dana ya jajibo min tsiya dangi ke ko a mafarki aka ce miki zan yarda za ki amince? Wai ni na yarda Hisham ya auro min dangin tsiya.
Hajiya laraba tace " ai shi na gani ,abin ya yi mukutar daure min kai, da naji kai ne ka amince
Alhaji ya girgiza kai " yanzu abin da zaa yi,tashi zakiyi kije ki bawa mahaifiyar yarinyar hakuri,ki sanar da su maganar banza yake ki dai san yadda kika yi kika shawo Kansu.
Hajiya ta ce yanxu kuwa, ai ba a bori da sanyi jiki

Alhaji hamza ya ce"A to, kin dai sani da bazarsa muke taka rawa,idan Hisham ya ki auren yarsu na tabbata duk wasu kwangiloli da suke shigo min dainawa zai yi,yadda yake ji da yar nan tasa tamkar gold

Haj laraba cewa ta yi," to ba dole ya ji da ita ba ita kadai ce fa tamkar ajali

Alhaji hamza ya girgiza kai kafin ya ciji baki ya ce don haka ki sake jawa yaronki kunne a game da yarinyar nan.don wallahi makutar ya ki bin umarina sai dai ya sake wani uba amman ba ni hamza ba " ya fada Yana sake nuna kansa..
Hajiya laraba kuwa cewa ta yi insha Allahu ma ba zai ketare umarinka ba, ai Hisham tun Yana yaro bai dai muka saka masa doka ya ketare na
Ya sake girgiza kai hade da cewa " Ah to, na dai fada miki,bin umarin Hisham shi ne kwanciyar hankalinsa a gidana.sabanin haka kuwa ke ma kin san sauran daga haka ya mike ya shige daki hajiya laraba kuwa mikewa ta yi ta nufi gidan su fareeda don ta ba mahaifiyar ta hakuri...Fareeda na zaune ita da maminta,daidai lokacin hajiya laraba tayi sallama cikin kwantar da murya saboda ta san gidan da ta zo daman haka lamarin yake kafi wani wani ya fika.
Maman fareeda a wulakance ta amsa sallamar saboda ita sam ba ta san dalilin da da yasa mijinta son auren ba, sam a nata tunanin ba su da dukiyar da har za a yi rububin hada zuria da su.to ka ji fa.gaba da gabanta!! Aljani ya taka wuta.ita a son ta a nemi wani hamshakin mai kudi a bashi ko ma dan shugaban kasa,amma ba wanann ba wanda mahaifinsa yake samu daga tsakar mijinta.

A shagube ta amsa gaisuwar daa haka ta ja bakinta ta tsuke.ita kuwa fareeda ko kallonta bata yi ba,ta mike ta shige daki.
Hajiya laraba ta sake rusunar da kai ta ce "hajiya daman hakuri nazo na baki tabbas na san Hisham ya bata muku amma a yi hakuri yaran yanzu ne ka haife su ba ka haifi halinsu ba"

Da saurii hajiyar ta dakatar da ita,fuskarta a hade sosai ta ce,"wasu yaran pa" wadanda ba su da tarbiyyah to ki sanar da shi in dai fareeda ya ce to daga yau na haramta masa aurenta.kuma za ki san na isa da 'yata dama duk alhaji ya jawo,idan ban da haka ai wannan hadin sam bai yi min ba.to me na sama ya ci balle ya ba nakasa? Ai babban goro sai magogin karfe,don haka ni na yi farin ciki da abinda ya faru,ya je can ya karata.Allah raka Taki gona yo ma banda iskancin wane ne Hisham da har zai wulakanta min ' yah, to an fasa yace ya auri ko wacce ce amma yata ba kalar kishiya ba ce." Daga haka ta shige daki
Hajiya laraba na sake ba ta hakuri amma ko waiwayen ta bata yi ba haka nan jikinta a sanyaye ta mike ta bar gidan an zuciyar ta cike da tunanin tsagwance rashin kirkin mamin fareeda
Ko da ta koma gida alhaji hamza yana nan yana tsimayin ta.fuskarta babu walwala ta shiga gaya masa yarda suka yi da mamin fareeda
Alhaji hamza ya girgiza kai ya ce mata kenan rabu da ita shu honourable din zan samu na san zai fahimce ni
Hajiya laraba ta ce ai kam matar nan tasa bata da mutunci wallahi ko kadan.alhaji hamza ya girgiza kai ya ce "duk ba kowa ne ya jawo wananan matsalar ba sai Hisham"
Tun da safe da ta mike take ta share- share a gidan, zuciyarta sai matukar suya take mata, ga shi umman tata ta tafi asbiti kasancewar ba ta jin dadin kanta ya matsa mata da ciwo sai karfe goma ta gama share_sharen sananan ta shiga wanka,da sauri take komai kasancewar karfe 11 safe take da (lecture).
Bayan ta kimtsa tsaf duk da ba wata shahararruyar kwallya take ba, yanxu ma riga da zani ne na wata koriyar atamfarta ta kamfanin NOUVA , ta yafa wadataccen mayafinta mai kaurin gaske, sananan ta shiga dakin mahaifinta yana zaune yana lazimi har kasa ta durkusa ta sanar dashi zata tafi makaranta.
Addaua'yayi mata sosai, sananan ya ce "Àllàh ya bada saa sai an dawo saudat.
Jikin ta a sanyaye tafito daga gidan don ko ficika ba ta da shi na shiga mota. Don suna da test ne yau kam da babu abinda zai sata zuwa makaranta.to wa yake ta karatu ana ta abin da zaa saka a ciki?gaba dayan su yau azumin suka tashi da shi saboda babu wadataccen abincin da za a iya yin ci biyu da shi a rana bama uku ba.

Gabadaya rayuwar tasu ta sake canjawa,tun bayan da Allah ya sake saukar da iftila,in gobara.bayan Hisham babu wanda ya kawo makudan kudi ya ba su sai ko inna Maryam da ta kawo musu kayan abinci su ma din tafi_tafi sun cinye su kaf.
Tafiya take kawai ba tare da ta san inda take jepa kafarta ba,saboda tunanin da ya cushe mata kwanya.ji ta yi ana yi mata wani mahaukacin horn,hakan ya sa ta yi saurin juyowa,don ta ga dalilin, tunda dai ita ta san ba a kan hanya ta ke bab,cak ta tsaya ganin Hisham ya fito dga motar cikin suit bakake fuskarsa saye da bakin gilas.

Tamkar ta juya ta ci gaba da saurin,sai dai sam ta kasa, ba don komaii ba sai don tuna halaccinsa gareta.a hankali ya iso har inda take fuskarsa dauke da mayalwacin murmushi.ita kuwa sam kasa sakin murmushi tayi saboda tunanin da ta yi yanzu shi kenan ta rasa shi, tana tsananin kaunar sa amman samm ba za ta iya jure wulakanci danginsu ba
Cikin slow voice yace " zo na kai ki mana please
Da sauri ta girgiza kai ta ce" uhm_uhm Hisham ka bar shi kawaii.
Zare gilas din idonsa ya yi cikin wani salon kallo ya ce "why sauda?me ya sa za kiyi min musu duk da tarin soyayyar da muke wa juna,? Ko kuna nufin an raba mu?

Dago Kai ta yi tace"y Hisham kenan rabuwa kam ai ta zama dole tunda dai kana jin furucin da mahaifanka ya yi a gidan mu.y Hisham ta ya ya kake tunani bamu iya auren juna?
Hisham ya girgiza kai yace,no saudat,da ikon Allah nine mijinki babu abunda Zai rabamu ina nan ina neman mana solution. Yanzu kixo muje mu karasa maganar a mota.
Jikinta a mace ta bi shi ta shiga motar don sam ba za ta iya yi masa musu ba.
Suna tafiya ya sake dubanta sosai kafin ya furta kalamansa," sauda please ki taimaka min don Allah ki min alkawarin komai  rintsi ba za ki rabu da ni ba, wallahi sauda ina miki wata irin soyayyah mai matukar wahalarwa.ko da ya sauke ta kalamin da ya dinga jaddada mata kenan.
Da kai take amsa kawaii don ta san abu ne mai matukar wuya har ta fita ya kira ta ta juyo a hankali,ya yi mata nuni da son ganin Jakarta.
Kin ba ba shi tayi.
Ya dan dube ta me yasa saudat  so nake na ga kin a mayar da hankali a makaranta."
Hakan da ta ji ya sa ta mika masa jakar.rafar yan #500 ya zuba mata a cikin jakar.
Sam ba ta lura ba, har ya miko mata.yana murmushi yace " A sha karatu lapia.
Ita din ma da kai ta amsa masa don ba ta son ta sake kwallafa shi a ranta , ta san aurensu abu ne mai makutar wahala saboda su kansu yan gidansu sun dauki zafi musamman yayyenta

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now