8

144 11 0
                                    

Zumuncin Zamani
Na

Nazeefah Sabo Nashe

Typing Fad'ima Sabi'u D'ankaka

8

Daga ranar da ya yi min wannan maganar,  Y.Hisham bai sake tunkara ta da xancen ba, duk da koda yaushe muna had'uwa don kuwa shi yake kaini ya kuma d'auko ni, Ko  ya sa direban office d'insa ya d'auko ni, saboda ya rok'i Abba kuma yayi masa wannan alfarmar don yaji dad'i sosai.
Tsahon sati biyu bai sake tada maganar ba. Yau ma da wuri na tashi saboda 7:30 zuwa 8:00 muke da lecture, yaluwar riga na saka, kamar koda yaushe da addu'ar umma na yi sallama daga gida. Ina fita na tarar da motarsa na bud'e gidan gaba na shiga fuskata a had'e na ce "Ya Hisham ina kwana"?
Ajiyar zuciya ya saki kafin yace "lafiya lau sweetheart" yarr naji wani iri a jikina, na ce "Ya Hisham dan Allah ka bar maganar nan"
Murmushi ya saki bayan ya juyo ya dubeni  yana tsare ni da ido har da d'aga gira d'aya ya ce "Me yasa zan bar ta? Ko  ba kya so na ne Saudat?"
Na d'ago da kaina ina dubansa. Kafin na ce "Ya. Hisham ba wai maganar so ba ce, maganar masalaha ake, kai kanka ka san tarin bak'in jinin da muke da shi a family d'in  nan duk a dalilin rashi. Ka  sani ba yarda za su yi  da wannan ba, idan ba so kake tsananin kiyayyar da ake nuna mana ya sake ninkuwa ba dan Allah ka yi hak'uri"
" Ba xan iya ba Saudat,
Yana daga dalilin da ya sa zan  sake jajircewa har na ga na cimma burina na auranki, saboda ina so nuna wa dangina kuskuran su, a yau ma zan  samu Abba akan maganar saboda tafiya zan  yi next week, ina so in ga matsayar zancen" hawaye ne ya kwaranyo daga idona cikin tsananin rud'ewa nace. "Dan Allah Y Hisham ka taimake ni" k'ura min idon ya yi kafin ya ce "Saudat bakya so na ne?"
Kallon sa sosai ya gigita ni don haka na kasa katab'us, sai murza  yatsun hannuna nake.
Murmushi ya saki ya ce "Saudat kina so na, wani banzan dalilin ne zai saki k'warar kanki," daga haka ya tayar da mota bai sake magana ba sai dai jefi_jefi yakan kalleni ya saki murmushi.
Ko da daddre ina jin sallamar sa na shige d'aki. Na ji yana gaisar da Abba, sannan duk su  Yaya sa'eed suka gaishe shi kuma, yayi k'asa da muryarsa sosai ya ce "Abba na zo ne yau a kan wata magana."
Gabana ne ya fadi sosai na yi saurin mik'ewa zaune ina zare idanuna. "Me Y.Hisham yake nufi ne?"
Abban yace "Ina jin ka Hisham menene ya faru?"
Tsit ya yi har sai da na ji Abban ya sake ce masa "Kai nake saurare Hisham, ka yi magana mana ka ke sosa k'eya, kada fa ka manta kai da su sa'eed d'aya na dauke ku fad' ko ma mene ne ina sauraron ka."
A zuciyata na ce "Ai dole ya ji kunya, shi kansa ya san ba abu Mai yiwuwa zai fad'a ba, sai kuma naji ya ce, "Abba dama a kan saudat ne, don Allah Abba aurenta nake so ka bani."
Tsit na ji kowa yayi shiru a wurin, da alama dai Hisham ba zai  yi sa'a  ba,hakan ya sa farin ciki ya ratsa zuciyata.

Abba ne ya yi gyaran murya ya ce "Hisham ba zan hanaka auren Sauda ba saboda ina alfahari da kai kuma uba nagari zai so 'yarsa ta samu miji nagari kamar ka. Matsala d'aya nake tsoro, ba kowacce matsala ba ce sai matsalar danginmu masu fifita kud'i fiye da zumuncin, don haka abin da zan ce maka ka je ka gama da mahaifanka, idan  har sun amince maka auren Sauda, to ni a shirye nake na aura maka ita"
 
Hisham ya saki ajiyar xuciya ya ce "Shi kenan Abba, zan je na same shi amma ina so ka yi min izini na ci gaba da neman auren ta, kafin mu ga abin da hali zai yi"
Abba ya ce "Bakomai ai Sauda "yar uwarka ce Kai mai iya d'aura mata aure ne, fatanmu dai Allah ya tabbatar da alheri."
Hisham ya ce "Shikkenan Abba, bari na je gida"
Gaba d'aya farin ciki ya ratsa ni, saboda na san ba yadda za'ayi Babansa Hamza ya yarda da wannan auren.
Yayanmu na ji yana cewa "Ai kuwa a gidan su da kyar za'a yarda da wannan had'in su da ba sa auren kowa sai yar wane, yanxu ya je yace saudat yake so ai B. Hamza sai ya kusan kashe shi."
Y Sa'eed ya ce "Hmmn kai dai Allah ya kyauta amman dai za'a b'allo ruwan bala'i a dangin mu
Abba ya ce "Ni  kam zan so ba shi aure don Hisham nutsattsen yaro ne, Abu d'aya nake tsoro, sam sauda ba zata iya jurewa bak'in hali irin na danginmu ba, don kuwa ba ta da sanyin hali kwarai, zuciyarta tana da zafi.
Umma dai cewa ta yi "Allah ya kyautaa, ya kiyaye fitina."
Nidai na yi lamo kan katifata, can na ji Ya sa,eed ya ce "wallahi Abba ba ma za su yarda Hisham ya aureta ba saboda yadda yake tashen naira yanzu ba zancen wanda ake yi a dangin nan da ya wuce Hisham, don kuwa ya tako arziki.
Abba yace "Wai ina saudat d'in ne?"
Umma tana murmushi na ji ta ce "wacce saudat? Ai ita tuni ta yi barci"
Yayanmu yace "Wa  ya gaya mata karatun jami'a irin na secondary ne? Musamman ita da take medicine karatu ma sai nan gaba"
Abba ya ce "wace irin magana ce wannan? Madadin ka yi mata addu'a, Allah sarkiii auta Allah ya ba da sa'a"

Jikar Nashe

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now