45

105 12 2
                                    

Zumuncin Zamani.

Na

Nazeefah Sabo Nashe

08033748387.

____________________

Jikinta rawa ya kama yi sosai ta kasa 'daga ido ta kalli Hisham da Ya kafeta da ido baya ko k'iftawa idanun nan sun ka'da sun yi jajir da su.

Hannunta ta 'dora a kai don ita kanta ta san ta gama yawo bata da abinda zata kare kanta ga Hujja zahiran b'aro-b'aro.

Bai mata magana ba don ba shi da k'arfin yi mata maganar ya juya jikinsa a salub'e ya fice daga 'dakin janye da akwatinsa da Ya shigo da shi.

D'akin da ta b'oye Mahmud nan ya nufa don ya san nan 'din ne kawai bata fiye shiga ba balle ta ajiye shirgi. Sauran kam tuni ta yi bake-bake da su suka zama nata kuma ba wani tsaftace su take yi ba.

Hannu ya saka Ya mur'da handle 'din da niyyar shiga amma ya ji shi gam a b'ame alamar an yi locking 'dinsa da mukulli. Mahmud da yake ciki tuni ya hau zare ido y'an hajinsa suka mur'da gumi ya cigaba da dita daga sassan jikinsa, Ya sani shikkenan tasa ta k'are don fes Hisham zai iya kashe shi, Har fitsari ya fara yi a wando don razana.

Fuskarsa a ha'de Ya juya ya kalli Fareeda da ta fara sakin fitsari a wando ya mik'a mata hannu "Give me the key." Bata da wani abin Yi da ya wuce mik'a masa Key 'din.

Yana bu'de 'dakin ya ga k'aninsa da suke Uwa 'daya uba 'Daya al'amarin da ya sake firgita shi, duk da ya da'de yana zargi da hasashen hakan amma bai kawo lamarin nasu ya girmama haka ba. Dalili kenan da ya bi kowane lungu na gidan ya saka secret camera musamman 'd'akinsa ba tare da ita Fareedan ta sani ba. Tun a asibiti ya fara kafa ayar tambaya a kansu sannan d aya dawo gida a ranar da ya dawo ya tsinci zoben da shi ya kawowa Mahmud tsarabarsa a tsakiyar gadonsa.

Jingina ya yi da bango yana jin zuciyarsa na masa wani irin suya. Mintuna biyu yana kallon Mahmud 'din Kafin ya lumshe ido ya nuna masa hanyar waje da hannunsa cikin tafasar zuciya.

Mahmud ya durk'ushe a wajen ya fara kuka "Don girman Allah Yaya Hisham ka yafe min, Wallahi sharrin shai'dan ne.

Wata irin tsawa da ya sakarwa Mahmud 'din ita ta saka shi ficewa da gudu ba shiri ya bar gidan.

Sai a lokacin Hisham ya samu damar zama dab'as a k'asa numfashinsa yana fita sama-sama tamkar ransa zai fita, ya fara tunanin wannan wane irin zamani Allah ya kawo mu mai cike da ru'dani, k'aninsa uwa 'd'aya uba 'd'aya shine yake mu'amalar matarsa suke aikata zina da aurensa saboda son zuciya. Tuni zafafan hawaye suka shigo masa ya dinga dukan kansa da hannunsa yana kaico da sanin Fareeda da ma amsa sunan matarsa da tayi.

Fareeda kuwa tana 'dakinta kuka kawai take  gaba 'd'aya duniyar ta juye mata nadama ce fal a ranta. Bata san wani hukunci Hisham zai mata ba, duk da dai ta san ba zai wuce hukuncin saki uku cur ba..  game da mahaifinta kuwa ta san ta ka'de har ganyenta ba mamaki ma ya tsine mata. Abu na gaba ko menene makomar yaronta? Sai a lokacin Wani irin kuka ya kece mata kukan nadama, Da na sani da kaico."

Da k'yar ya mik'e Ya fice daga gidan bayan ya yi wanka ya sake kayan jikinsa. Gidan su  Sauda yake son zuwa ya isar da sak'on Sauda da ya barta a abuja ko ya samuya rage ra'da'din da yake zuciyarsa amma sai ya ga gwara ya fara zuwa gidansu tukunna ya ga mahaifansa.

*****
Duk da ta yi farin ciki da ganinsa bata nuna masa akan fuskar ta ba ta ja fuskar ta tsuke tamau, so take lallai sai ta nuna masa kuskurensa na tafiya ya bar matarsa tsawon lokaci ba tare da ya waiwayeta ba. Mommynsa kenan da take zaune akan kujera hakimce a falo tana amsa gaisuwarsa kamar bata so.

Ya 'dan saki murmushin dole yana kama hannayenta. "Afuwa Uwa ta gari na san Mommy na sarai bata son Allah ya yi fushi da ni sakamakon fushin ta."

Ya san lagonta duk fushin da take da shi da zarar ya mata hakan ake neman fushin a rasa don da gaske bata son ganin y'ay'anta cikin fushin ubangiji.

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now