29

212 8 1
                                    

Zumuncin Zamani....

Na

Nazeefah Sabo Nashe...

08033748387..

Hisham yana shiga gida harabar gidansa ya yi parking a wajen da ake ajiye motoci. Da kyar ya fito daga motar jiri na 'dibansa ha'de da ciwon kai mai tsanani. Ga kalaman Saudat da suke masa kara-kaina a k'wak'walwarsa. "Ka daure ka jure ka rabu da ni.." shine kawai abinda ya ke ji a kunnensa.

Tunani yake 'Ashe Saudat zata iya rabuwa da shi? Ashe har a yanzu soyayyarsa bata yi girman da za ta kasance tare da shi ko a mutu ko a yi rai ba. Da gaske Sauda bata fara masa SON MUTUWA BA? Son da zata ji ko za'a kashe ta ba zata iya rayuwa ba shi ba?

Farida na tsaye a bakin window tana ganinsa da tsawon lokacin da ya 'dauka a cikin motar, har zuwa sanda ya fito yana layi kamar ya sha kayan maye. Wani haushi ya turnik'eta ganin yadda ya zage ya lalace daga yau 'daya kawai. Tsananin tsanar Sauda ya sake shiga zuciyarta. Ta raya a ranta ko ta halin k'ak'a sai ta raba zuciyar Mijinta da soyayyar Saudat. Dubi ko tunaninta ba ya yi saboda an raba shi da Saudat.

Zuciyarta a zafafe ta fito daga 'dakin lokacin da ta fito Hisham ya shige 'dakinsa yana kwance flat a kan gado. Ba tare da sallama ba ta tura k'ofar 'dakin ta shiga direct. Da alama ita da kanta ta kawo kanta 'dakin mijin ba kamar kowace amarya ba da miji yake kai kansa wajenta a daren farko na aurensa.

Hisham ya bita da wani malalacin kallo tamkar zai yi magana kuma sai ya fasa, ya mayar da idonsa ya rufe.

A kufule Fareeda ta k'arasa cikin tsiwa ta ce "Hisham magana fa za mu yi ka ganni amma ka bawa banza ajiyata." Ta fa'da tana ka'da kafa'darta.

Ya bu'de idonsa da kyar ya zube a kan fuskarta ya ce "Please leave alone Fareeda, wallahi bana son hayaniya."

Cikin zafin rai ta ce "Ni ce nake maka hayaniyar Hisham?" Ba tare da ya tanka mata ba ya cije lab'b'ansa ya sake kulle idanunsa gaba 'Daya.
Fareeda ta da'de tana sababi kafin ta fice daga 'dakin cikin b'acin rai tana fa'din "Wallahi ka yi da 'yar halak, zan nuna maka Fareeda macece mai aji ba karabiti ba."


__________________

A sauri Saudat take shiri don tafiya makaranta saboda a ranar za su fara Exams, ta fito tsakar gidan bayan ta zura hijabinta "Umma zan tafi, sai na dawo na makara." Ta fa'da da sauri ha'de da saka kanta tana k'ok'arin barin gidan. Umman ta ce "Ga ruwan koko can ba za ki sha ba kike k'ok'arin tafiya?" Saudat tana murmushi ta ce "Umma kin manta yau ina azimi? Yau alhamis." "Haka ne fa, to Allah ya bada sa'ar jarabawa." Ta fa'da tana mik'a mata Naira 200 da ta kunto daga bakin zaninta Saudat ta karb'a tana godiya.

Hadarin da ta gani yana gangamowa a garin yasa take zuba uban sauri bata son ruwan sama ya zubo bata isa makarantar ba. Ga shi exams 'din da za'a musu mai zafi ce. Jin k'ugin mota ta yi a bayanta sam ba ta yi k'ok'arin juyawa ba ta sake jan k'afarta da sauri.

Hisham ne ya yi parking a gabanta sai a lokacin ta lura da shi, ya sauke ba'kin glass 'din motar sanye yake da pyjamas kayan barci da alama daga barci ya tashi cikin ha'de rai alamar ba wasa a tare da shi ya ce "Shigo"

Saudat ta 'dan yi jim kamar ba zata shiga ba,Hisham ya daka mata tsawa "Ki shigo na ce"

Ganin hakan da ya yi sai ya tsorata  da sauri cikin rawar jiki ta bu'de motar ta shiga. Da sauri ba tare da Hisham 'din ya kalleta ba ya ja motarsa. Har suka isa makaranta bai mata magana ba. Al'amarin da ya tunzira zuciyar Saudat ta dinga tunanin wane irin mulki mallaka yake mata. Ba tare da ta masa magana ba itama ta saka hannu ta bu'de motar.
Da sauri Hisham ba tare da ya kalleta ba ya ri'ke hannunta  cikin tsare gira sosai ya ce "Daga yau na sauke shiga adaidaita sahu, ban amince ba hak'kina ne na kai ki makaranta tunda har a yanzu da aure na a kanki. Kina ji na?" Da sauri ta ha'de rai tana kallon gefenta turo bakinta za ta yi magana Hisham ya yi saurin rik'e bakin ya had'e rai sosai kafin ya ce "Ba na son jin komai daga bakinki Saboda na san ba alheri za ki fa'da ba." Ya mik'a mata envelope ha'de da cewa "That's all kina iya tafiya." Ta ha'diye abinda zata ce ta fice cikin sauri tana mamakin Hisham wannan fa shi ake kira 'K'arfin hali murmushin yarda ya tsare gira take kamar wani sarki da baiwarsa.

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now