43

129 13 3
                                    

Zumuncin Zamani..

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

Me neman sa daga farko ya duba wattpad. @Nazeefah381. Na gaji da Jin y'an please daga farko.

____________________

Gaban Hisham ya dinga fa'duwa Jin sallamar Abban Saudan da ta kara'de cikin majiyansa. Murya na rawa ka'dan ya ce "Wa alaikassalam Abba Ina yini?"

Abban yana murmushi ya ce "Lafiya lau Hisham, y'an gudun Hijra masu tafiya babu sallama, kuna nan lafiya ko?"

Hisham ya saki ajiyar zuciya Jin Abban ya amsa masa cikin walwala da farin ciki. Hakan ya saka shima cikin karsashi ya ce "Lafiya lau Abba, a yi mana afuwa tafiyar ce ta zo bagatatan."

"Babu komai Hisham, na daina jayayya da hukuncin Allah haka Allah ya k'addara Saudatu matarka ce, kuma dama ni ban tab'a k'in aurenku ba masalaha dai na nema muku, fa tana ni dai ka rik'e min Saudatu da amana ka tuna a can inda kuke 'din bata da kowa daga Kai Sai Allah, Ubangiji ya yi muku albarka, Ina ita Saudatun?"

Hisham ya ji da'din kalaman Abba, hak'ik'a ya sake tabbatarwa da nagartar kalaman Abba, dattijon arziki mai sauk'in hali Wanda ya d'au duniya ba a bakin komai ba.

Cikin ajiyar rai ya ce "Gata nan Abba, ita ce ma take ta son Jin muryarka."

Abba yana dariya ya ce "Y'ar nema bata wayar mu gaisa." Hisham ya kara mata wayar a kunne shima yana sakin murmushi alamar cin nasara yanzu ya gama da babin Abba tunda ya fahimceshi saura su Daddy uwa ubar da basu San har yanzu yana tare da Saudatunsa ba.

Cikin muryar kuka Saudatu ta ce "Ab.....ba na Ina yini." Abba yana murmusawa da tunanin har yanzu Saudatu ba zata bar sangarta da shagwab'a irin na y'an fari ba da kuma zamowarta y'a k'walli guda a cikin yara maza ya ce "To menene na kukan Saudatu na, share hawayenki ya bak'unta?" Ta share hawayenta da take jin sake zubarsu kamar ruwan famfo da gaske tana jin kewar y'an gidansu gaba 'dayansu "Ba zaki shiru ba Saudatu, ki godewa Allah da ta baki jajirtaccen namiji da yake son ki don Allah, ba abinda za kiyi ki burgeni a duniya irin ki yi masa biyayya iyakar iyawarki da jikinki da zuciyarki, ki tuna aljannarki tana tafin k'afarsa sai ya so za ki shiga, kada ki zubar da mutuncin gidan mu Saudatu duk matar da ba tawa mijinta biyayya iyayenta zata cuta, su mijin zai ga basu inganta tarbiyyarta ba kina ji na?" Ta 'daga kai don idan haddace tuni ta haddace wannan nasihar ta Abba "Na ji Abba In sha Allah." "To Allah Ya yi miki albarka." "Ameen Abba." Ta amsa kafin ta masa tambayar da ta so saka wayar ta fa'di a hannunsa "Abba Ina Yaya Sa'aduna kullum sai na yi mafarkinsa yana sanye da fararan kaya yana 'daga min hannu alamar Bye-Bye yana tafiya. Gaba na yana fa'duwa Abba yana nan lafiya ko?"

Tsit ya yi sanin cewa idan ya sanar mata da mutuwar zata gigita k'warai ga shi ba ita ka'dai bace, Sa'adu shine mafi soyuwa a cikin zuciyar Saudatu a kaf cikin Yayyenta. Shine sak'onta Amma ta su ta fi zuwa 'daya. 

Hawaye ne ya kawo idonsa kafin murya a dake ya ce "Sa'adu yana nan lafiya ki cigaba da masa addu'a bakomai kin ji, baya kusa da na bashi wayar." Ta saki ajiyar zuciya "Alhamdulillah Har na ji da'di Abba, Umma fa?" Ya kai dubansa kan Maryama da take ta sakin hawaye kasancewar wayar a hands free take kuma duk ta ji abinda Saudatun take cewa toshe bakinta kawai ta yi da hannayenta tana kuka.

"Ummanki tana nan lafiya zan saka ta kiraki anjima ka'dan." "Tom Abba ka gaisheta da kyau." Ya yi saurin amsawa yana rejecting call 'din baya son ta sake masa wata tambayr da zata k'ureshi y'a dinga mata k'arya. "Akwai tashin hankali duk ranar da Saudatu ta fahimci Sa'adu ya mutu."

A hankali Saudatu ta fa'da kan Hisham ta rungumeshi cikin tsananta farin ciki take cewa "Alhamdulillah, yanzu komai ya yi daidai tunda na ji Abba baya Fushi da ni, da komai nake yi daurewa kawai nake wallahi." Hisham ya kamata sosai yana ha'de goshinsu waje 'daya "Thank God yau Babyn tana cikin farin ciki fatana wannan farin cikin ya 'd'aure Har bed time mu ragargaji amarci." Da sauri ta turo baki tana magana k'asa-k'asa "Kai Yaya Hisham ka dinga bari ina hutawa mana." Hisham ya ja leb'enta ya mur'de ka'dan "Istigfari maza kafin mala'ikun rahma su ji ki, aikin ladan ne ba kya so? Ko so ki ke na dawo da Fareedah nan?"

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now