9

136 8 0
                                    

Zumuncin Zamani
Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387

Pg. 9

(Sannu da jumirin typing Fad'ima Sab'iu Dankaka jazakillahu Bil jannatil Aaliyah.)

Da asussuba muka ji abba yana ta zabga "Innalillahi wainnah ilaihirrajiuna" A hanzarce muka fito daga d'aki kusan tare da Umma fad'i take "Lafiya Abbansu?"
Abba yace "Ina fa lafiya, yanzun nan Hisham ya yo waya ya sanar da ni mutuwar H.Amarya"
Umma ta saka salati ta ce "Allahu Akbar ubangiji Allah ya jikantaa."
Ni kuwa sam ban ji mutuwar a cikin raina ba. To ina ruwa na? Ta yi ta mutuwar mana. Matar da ba ta so sam ta ga y'ay'anta sun yi alheri don bak'in hali, ita duk ta koya wa y'ay'anta rashin kyauta da rashin alheri, to don ta mutu har abin damuwa ne? Ai ga shi nan za'a je kabari a girbi abinda aka shuka, idan ka aikata alheri kaga alheri, idan sharri kuwa ka aikata kaga sharri cikin kabari.
Kwanciya na sake yi akan gado, dama ina fashin sallah. Har aka idar da sallah ina jin su maimaita zancen mutuwar kawai ake yi, kuma ban ji wanda ya yi wa Abba waya ya sanar da shi zancen mutuwar ba tun bayan Hisham duk dai ba don komaii ba sai don an san ba shi da shi.

Umma naji tana kwala min kira.
Nayi saurin amsawa na kuma fito. Bi na ta yi da kallo "Yi ki d'auko hijabinki mu tafi gidan mutuwa nan su Abbanki har sunyi gaba kada mu rasa jana'iza.
Na zumb'ura baki  ina cewa "Umma ban yi wanka ba fa?"
Bi na tayi da kallo ta saki baki ta ce "Wanka! Wanka fa ki ka ce? Sai kin yi wanka za ki je gidan mutuwar.? Matsayin uwa take fa a wurin babanki."
Na sake Zumb'ura ba ki na ce "Umma don Allah ki je zan taho idan gari ya yi haske,su ma da idan sune ko Abba ne ya mutu babu mai zuwa gidan nan da asuba.
Umma ta hade rai ta ce "To uwata, gaya min abindaa ya dace na aikata ki ke,ke ma ai kin zama su wallahi ba ku da banbanci ko ki d'auko hijabin mu tafi ko ranki ya yi matuk'ar b'aci.
Ganin yanayin fuskarta ya sa babu shiri na tafi d'aki na zira hijabi harda nikab na saka muka tafi.
Gidan mutuwar dank'am yake, a d'inke da mutane kai da ganin wasu ba don Allah su ka zo ba,ana ta kuka ni dai na ja nikab na rufe fuskata. Ina daga gefe cikin ya ku bayi, jiga - jigan kuwa suna cikin k'aton falon. Abinda ya ba ni mamaki ganin kafin asuba aka yi mutuwar nan amman kafin kiftawar ido har gidan ya cika damkam da jamaa tun kafin garin ya yi haske. Kowa ya shigo da kukansa burinsa dai a ce ya zo
Hajiya amarya ba ta da y'a mace duk y'ay'anta maza ne su Baffa Umar. Ba a samu fita da gawar ba sai k'arfe goma saboda ana jiran manyan baki da za su zo daga garuruwa daban- daban, tamakar  idan babu su Allah ba zai mata rahama ba.
Bayan an kai ta kuwa nan gidan ya zama gidan party don dai lemuka iri iri aka dinga shigo dasu katan _katan da ruwan roba. Abincin breakfast kuwa doya da kwai, dankali da kwai sai dangin su farfesu da waina masa, funakaso da su sinasir. Tabbas wanda ya mutu shi ya mutu.
A gidan mutuwar ma sai an banbance tsakanin talaka da mai kud'i domin kuwa gurin zaman masu kud'i daban ne tamkar yadda cimar su take daban, ya illahi me wannan zamani yake son  ya zama mutane sun makance sun kurmance saboda kud'i? Kowa zancensa kudi!!! Kudi!!!kudi¡!!!! Babu abinda yafi kud'i daraja da k'ima a idon jamaa.
Duk zaman gidan ya gundire ni, ba don komai ba sai don yadda ake ta Hira, duk wanda aka gani kuma da wata irin shiga kallon banza ake yi masa, amman naga alama Umma ba ta da niyyar tashi mu tafi, sai  ma tattre kwanuka suke yi wai za su wanke ita da wasu ya ku- bayi y'an  uwanta A xuciyata nace "Ya ubangiji Allah ka azurta mu ko iyayenmu muma sa zama masu daraja tamkar kowa.
Sai bayan magariba sannan umma ta ce na mik'e mu tafi, zuwa lokacin na galbaita da yunwa don banci komai ba sakamakon wariyar launin fatar da na ga anyi a wajen rabon abincin.
Y.Hisham yana ganin mu ya taso da saurinsa daga rumfar da ake zaman makokin, har k'asa ya gaida Umma, sanann ya ce "Gida za ku tafi ne?"
Umma tace "Wallahi,dare ya fara yi gwara mu tafi gidan." Y Hisham ya ce "Gaskiya kam, bara na sauke ku dama ni ma tafiya zan Yi"
Umma ta girgiza kai kafin ta ce, "Ba mu takura ka ba kuwa Hisham?"
" Ba komai umma, wallahi daman ni ma zaman ya gundire ni"
Yana sauke mu gida na fad'a don ba na k'aunar ya yi min magana, hasali ma kunyar sa nake ji.
Ko da muka shiga su Abba tuni sun dawo, su ma maimaita zancen budurin da aka sha kawai suke yi. Ni dai kicin na shiga na dafa abincin . Ko fitowa ban yi ba daga kicin din sai dana xauna na take cikina da abinci sananan na sami nutsuwar kaina.
Kashe gari kuwa tun safe Umma ta tafi ni dai rok'on Allah na yi ta bar ni a gida na ci saa kuwa ranar ta barni babu mamaki ita ma ta hango babu alfanun a zuwa na zaman makokin.
Hakan ce ta ci gaba da kasancewar har aka yi sadakar bakwai, zuwa na biyu kad'ai gidan mutuwar.
Tun bayan ranar aka yi mutuwar ban saka Hisham idona ba sai bayan sati guda. Ko makaranta direban kamfaninsa ne yake sa wa ya kai ni ya d'auko ni.
Da yammah ya shigo gidan cikin shigar k'anann kaya da suka amshe shi sosai, fuskarsa a dan had'e idanunsa a kaina ya na gaida Umma ta mik'e ta shiga d'aki, ni kuwa daman ina daga gefe gyran farcena nake yi.
Ya matso daf da ni ya zauna , kamshin daddadan turarensa ya ziyarci hancina. Muryata ta yi k'asa sosai na ce Y.Hisham ina wuni."
Wani kallo ya jefe ni da shi, wanda ya saka jin bugun k'irjina ya tsawaita.  "kin kyauta Saudat, yanxu fisabillahi abin da kika yi ya yi daidai? Kwana nawa ba ki gan ni ba Amman ko ki neme ni duk a dalilin rashin so."
K'asa na yi da kaina sosai,don kam ban san amsar da zan ba shi ba sai na ce "kayi hakuri Y.Hisham ban san hanyar da zan bi na neme ka ba, saboda ba ni da number wayarka."
Kura min ido yayi sosaii,kafin ya ce "Saudat wanann ba hujja ba ce, saboda su khalil duk su na da number ta." nayi murmushi kawaii don babu abin cewa.
Y Hisham ya ce "shi kenan nagode sosai daman sallama na zo yi miki, gobe zan yi tafiya ne sai na ce sai na dawo."  Ya fad'a yana mik'o min wata babbar leda mai tambarin ShopRite cike take taf da kaya,daga haka ya juya ya fice.
Na lura jikinsa a mace yake sosai, na mik'e nima jikina a sanyaye Umma na kai wa ledar, har zan juya ta ce "Zo ki bud'e mu ga abinda ya ke a ciki, shi baya gajiya da hidima duk da na tabbata iyayensa ba bari za suyi ya aureki ba."
Kayan kwalliya ne designers masu d'an karen kyau, sai turarika da wata shegiyar waya umma ta ce "Ban da matsalar danginku Hisham mijin kwarai ne kowacce mace za ta yi murna da farin cikin samun sa a matsayin miji abu d'aya ake guje miki matsalar danginku, da ba sa ganin talaka da k'ima da mutunci."
Na saki ajiyar xuciya bayan na mik'e na koma d'akina, kwanciya na yi sosai a kan katifa cikin zuzzurfan tunani, don so kamm yanxu na hak'kake wa raina ina son Hisham amman na san aurenmu da shi na mai yiwuwa ba ne.

Daga nan labarin da na karanta wanda ta mik'o min a wani dogon littafi ya tsaya,na d'ago ina duban ta, kafin na ce"Saudat labarinki ya d'auko dad'i sai dai banji k'arshensa ba"
Tayi murmushi kafin ta ce" Anty Nazeefah ba ni da jumurin rubutu ne, zan gaya miki da wanda na sani da wanda ni ma labari aka bani." Na d'aga kaina kafin na ce, "Ni ma hakan zai fimin sauki"
Sauda ta gyara zama, sanann ta miko min takarda da biro,ta kuma ci gaba da ba ni labarin***************

Jikar Nashe ce!

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now