31

117 6 0
                                    

Zumuncin Zamani

Ma sha Allah, Allah Ya dawo da mu dafatan an yi sallah lafiya? Ubangiji ya amshi ibadunmu.

____________________

Tsananin ru'dani da firgici ya ziyarci Hisham, ya dinga jin gabansa na luguden daka gani yake tamkar mafarki yake, shin da gaske Baffa yake da Ya ce dole ya saki Saudatu, abinda yake ganin tamkar da kamar wuya... Ya dinga ha'diyar wani abu mai 'daci da Ya tokare masa mak'ogaro. Ya sani sarai duka abinda Baffan Ya fa'da ba son zuciya a cikinsa an cuci Abba Mustafa matuk'ar cuta, babu kuskure a cikin abinda Baffan Ya fa'da ya yi hukuncinsa a kan gab'ar data dace. Tabbas TALAUCI BA HAUKA BA NE.. abu 'daya da ba zai iya ba Sakin Sauda ko da kuwa ya sha giyar wake. Yana son Saudat son da shi kansa ba zai iya kwatanta shi da komai ba, sai dai zuwa lokacin shi da kansa ya san ba shi da mafita Baffa ne yake tunanin zai zama mafitarsa to ga abinda Baffan Ya ce, ba ya goyon son zuciya da zalunci baya goyon bayan k'arya a koda yaushe yana turbar gaskiya...

A wannan karon kasa bin umarnin Baffan ya yi duk da kiran da yake k'walla masa ya fice da sauri bayan ya yi burus da kiran Baffan, sam ba ya gani ga jiri da yake 'dibansa Amma ina burinsa kawai ya sulale Ya gudu kafin Baffan Ya cim masa ya shiga motar ya figeta da gudun tsiya.

A daidai gadar wudil mummunan Hatsarin Ya afku, duk da k'ok'arinsa na kaucewa hatsarin sai dai hakan bai faru ba don ya kasa controlling 'din kansa. Har wata mota k'irar Bus ta zo ta doka masa ya fa'da cikin wani rami ha'de da dukan wata bishiya.

Gurin ya cika damk'an da mutane kowa yana salati da taslimi da tunanin koma waye a ciki ba k'aramin rauni Ya samu ba. Sam babu alamar numfashi aka ciro shi hankalin jama'a a tashe aka kinkimeshi aka saka cikin wata mota sannan a sukwane aka nufi da shi babban asibitin da yake cikin garin wudil 'din. Babu wanda zai tsammaci akwai sauran ragowar numfashi a jikinsa.

Sai dai ana zuwa asibitin likitocin suka yi rufdugu a kansa nan suka gano da ragowar numfashi a tare da shi. Suka rufu a kansa tsawon awoyoyi biyu kafin su ceto rayuwarsa da ikon subhana.

Da salati Ya bud'e idonsa da k'yar kansa ya masa nauyi sosai  matsananci ciwo kan nasa yake masa in da anan ya samu buguwa sai k'afarsa da ta samu gociyar k'ashi. Daidai lokacin likitan ya shigo cikin murmushi Ya ce "Alhamdulillah Lafiya ta samu ko Yallab'ai?"

Hisham ya 'dan saki murmushi kafin Ya ce "Alhamdulillah mun gode Allah, Amma likita waye Ya kawo ni nan?"

Likitan ya dafa shi yana fa'din "Cool down, accident ka samu a hanyar wudil 2 hours back hope you remembered shine aka kawo ka nan, Alhamdulillah sanda aka kawoka ko numfashi ba ka yi baka ji wani mummunan rauni ba sai k'afarka da ta samu gociyar k'ashi. Yanzu ka bada numberr da za'a samu family 'dinka a sanar da su."

"Ina wayoyi na?" Ya fa'da yana laluben aljihunsa inda anan yake tsammanin ganin wayoyin sai dai wayam babu su ba alamarsu.
Murmushi Doctorn ya yi kafin ya ce "Gaskiya ba a kawo ka da komai ba, ka San sharrin mutanen mu yanzu jira suke a yi hatsari su yashe mutum tas. Saboda rashin Imani da tausayi."
Takaici ya kama Hisham da Allah wadai da halin jama'ar mu ta yanzu ya dinga murza hannunsa kafin ya ce "Allah ya kyau ta, yanzu bani Aron wayarka akwai numberr Mommy a kaina na kirata."

Likitan ya mik'a masa sannan ya cigaba da rubutunsa.

Hajiya Laraba na zaune ta ji wayarta na k'ara, haka kawai sai gabanta ya fa'di hakan yasa ta 'dau wayar a sanyaye "Hello waye?"

Hisham ya 'dan saki ajiyar zuciya kafin ya ce "Mommy Hisham ne."
Ta dubi numberr sosai kafin cikin takaici ta ce "Toh, kace Isashshe ne, ai na zata ka canja Iyaye."
Bai kula maganar tata ba ya 'dan yi yak'e kawai kafin ya ce "Na samu Accident ne a hanyar wudil shine na kira na gaya muku. Ina asibitin Wudil."

A razane Mommy ta ce "Na shigesu hatsari kuma? Yanzun kana ina hope dai da sauk'i?"

Ya 'dan saki ajiyar zuciya kafin Ya ce "Kada ki damu Mommy, ban ji ciwo sosai ba da sauk'i, ki sanar da Fareeda don Allah don babu waya a hannuna, a taho da mota don ina son na nemi transfer zuwa asibitin k'ashi."
Mommy ta ce "Ai kuwa yanzu zan sanar mata, da ikon Allah yanzu zamu taho, Bari na yiwa Abbanka waya."
Tana kashewa kafin ta kira Abban nasa sai da ta kira Fareeda tana 'dagawa ta ce mata "Mijinki ya yi hatsari yana babban asibiti na Wudil, sai ki maza ki shirya mu tafi."

Tashin hankali sosai ya riski Fareeda zufa ta dinga keto mata tamkar an sanar mata da mutuwar Hisham cikin tsoro da firgici ta dinga shirin tafiya asibitin a ki'dime.

Mommy na gama kiran Fareeda ta kira Daddyn Hisham 'din shima ta sanar masa, sannan ta mik'e bayan ta Kira Mahmoud suka fice a babbar motar gidan Jeep ce. Sai da suka biya suka 'dau Fareeda sannan suka wuce.

Gudu sosai Mahmoud ya yi don cikin mintuna Arba'in suka isa cikin wudil 'din, ba su sha wahalar gane 'dakin da yake ba.

Sai da suka shiga suka gan shi a zaune sannan hankainsu Ya kwanta. Shi 'din ma duk da k'afarsa tana ciwo haka ya dinga jifansu da murmushi don son ya share musu damuwar da ya gani b'aro-b'aro kwance a fuskarsu.

Ba su jima ba aka ba su transfer don wucewa da shi asibitin k'ashi a cikin ambulance 'din asibitin saboda yarda k'afarsa take masa ra'dadi kasancewar ba a d'aure ba sai sun je can. Fareeda ce agefensa sai shafa kansa take tana furta "Am Sorry Love zaka samu sauk'i yanzu In sha Allah.

Suna isa babu b'ata lokaci aka gyara masa k'afar, Ya kam ci azabar gaske don Har ihu ya yi duk jarumtarsa sai da aka rirrik'eshi. Fareeda na rungume da shi damuwa ta bayyana sosai a fuskarta. Tausayin Hisham da Soyayyarsa ne kawai suke damalmala zuciyarta.

Kafin kace me? Tuni asibitin Ya cika da dangi na kusa da na nesa. Kowa burinsa a ce ya zo. Shegiya Naira yanzu da talaka ne da baka ga wannan dandazon ba, mutane k'alilan zaka gani wa'danda suke abu don Allah ba don ace sun yi ba sai don sauke ha'k'ki in zumuncin Allah.

Kowa zai shigo k'atuwar leda ce a hannunsa Har Mommy da Fareeda suka rasa inda za su zuba kaya don Sun musu yawa k'arshe Mommy tasa aka dinga rage wasu ana rabawa ma'aikatan jinyar da masu jinya a asibitin wasu kuma aka dinga kai su mota.

Da Hisham Ya gaji da ganin hidimar da mutane suke yi da shi da kansa ya aika sanarwa a group 'din dangin a kan duk wanda zai zo duba shi ba sai Ya kawo komai ba ya gode da kulawa, tunda shi da kansa ya san ba don Allah suke ba idan don Allah ne me yasa ba su yiwa Abba Mustafa ba da sauran mabuk'ata a cikin dangin?

Sai da ciwon ya lafa masa sannan ya saka Mahmoud ya je ya siyo masa manyan wayoyi don duk abin nan Saudat ce a ransa ya san bata san ya yi hatsari ba don ba su da darajar da za'a sanar musu a dangi. Yana son kiranta Amma ba hali saboda Fareeda da tazo ta nanik'e masa tun abin yana burgeshi Har ya fara ba shi haushi.

K'arfe 10:30 na dare Mommy ta tafi gida, Ya rage daga Fareeda sai Mahmud, shi ma Mahmud 'din 'Dan fita ya yi ya basu waje saboda ya lura sam Fareeda ba kunyarsa take ji ba. Ta wani rungume yayan a k'irjinta tamkar yaro tana ba shi abinci. Shi kansa Hisham haushi ne ya kama shi da sauri ya 'dan zame ya kwanta ya lumshe ido kamannin Saudat kawai yake hangowa.

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now