28

111 7 0
                                    

Zumuncin Zamani.

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

_________________

Ya da'de zaune a cikin motar ba tare da ya yi yunk'urin tafiya gida ba. Har zuwa sanda Abba Mustafa ya fito da niyyar tafiya masallachi, mamaki ne ya kamashi ganin Hisham 'din zaune a cikin mota daf da Adaidaita sahunsa. Yana isa jikin motar ya hangoshi zaune ya kifa kansa da sitiyari ta cikin glass 'din motar.
Hankalin Abba Mustafan a tashe yaje jikin motar ya fara k'wank'wasawa.
Hisham a firgice ya 'dago da birkitattun idanuwansa. Yana duban Abban. A ki'deme Abban ya ce "Subhanallahi! Hisham me zan gani haka? Kada kace min tun awanni uku da suka gabata kana nan a zaune?"

Hisham ya ha'diye wani abu mai 'daci da ya tokare masa mak'oshi. Bai iya furta komai ba illa 'daga kai da ya yi.

Abba cikin tausayi da jimamin halin da ya gan shi a ciki ya ce "Allah ya kyauta maza ka tafi gida, gobe ka dawo za mu yi magana a nutse"

Cikin sanyin jiki ya ce "Nagode Abba." Sannan ya ja motar a hankali ya bar layin zuciyarsa ta 'dan samu nutsuwa ka'dan gani yake a goben Abban zai ce Saudan ta bi shi, ya amince ko wani gidan zai samar mata ko da a wani garin ne kuwa. Yarda ya hango Abban yana shiga Adaidaita sahunsa ya ji ransa ya sake b'aci tsanar danginsa ya ji sosai a zuciyarsa. Maganar gaskiya duk arzikin danginsa ya tashi A banza matuk'ar sun kasa fitar da Abba Mustafa daga yanayin da yake ciki.

*********
Da Daddare....

Duka Ahalin gidan Abba Mustafan suna zaune suna cin tuwon dare. Tuwon masara miyar kub'ewa 'danya, duk da babu nama miyar ta yi da'di sosai ko don an zuba mata wake ne, kasancewar Umman gwana ce wajen girki musamman na gargajiya.
Duk da ransu a jagule yake da b'acin rai sai dai ba zaka gane ba kasancewaru masu cire damuwa daga zuk'atansu masu tawakkali da dogaro da kai.

K'amshin turaren Hisham ya fara gauraya cikin hancinsu kafin sallamarsa ta biyo baya. Sanye yake cikin tsadaddiyar jallabiyarsa ruwan toka (Ash colour) silifas black colour a k'afarsa sam fuskarsa babu walwala ko ka'dan. Sallama ya yi cikin sauk'akkiyar murya. Gaba 'd'aya suka 'dago suna kallonsa kowa ya kasa amsa sallamar idan ka 'd'auke Abba da ya amsa masa yana sakin murmushi sosai cikin karsashin murya ya ce "Malam Hisham ne tafe da darennan wato da na ce ka bari sai gobe ba ka ji ba kenan? To Allah ya mana muwafak'a. Bismillah shigo zauna." Yana nunawa Hisham 'din daf da shi.

Hisham ya zauna nauyin da k'irjinsa ya yi yana sauk'ak'ewa gani yake Akwai alamun sassauci tattare da Abban sab'anin Umma da ta kasa ko dubansa. Ya dubi su Muhammad da suma ba fuska a tare da su ya mik'a musu hannu. Sai sannan kunya ta kama su suka dinga gaisheshi, ban da Sauda da ta yi kicin-kicin da fuska kamar ba a tab'a halittar dariya a fuskarta ba. Ji take zuciyarta kamar ta fashe saboda takaicin iyayensa duk da har a yanzu tana jin Feeling 'don son sa a zuciyarta amma bata ji koda son zai kasheta zata sake amincewa ta komawa auren sa.

Abba ya sake kai dubansa kansa bayan ya ture kwanon tuwon da yake gabansa ya ce "Ban tsammaci ganinka yanzu ba Hisham, tunda mun Riga mun yi da kai sai zuwa gobe zaka dawo."
Ya sunkuyar da kansa kafin ya ce "Abba na kasa jurewa ne gani nake kamar raba ni da Sauda za ku yi gaba 'd'aya, wanda tabbas idan hakan ya faru tabbas ban san ya zan samu kaina ba don any thing can happen. Abba ko abinci na kasa ci ruwan malt ne kawai a cikina."  Cikin tausayi Abba ya ce "Subhanallah lamarin har ya kai haka Hisham? To da ace mutuwa ta yi fa." "Zan rok'i ubangiji nima ya 'dau raina." Ya bawa Abban amsa direct kuma fuskarsa kawai zaka kalla ka tabbatar da gaskiyar zancensa. Abba ya hau jijjiga kai "Hukumullahi ka ajabun wato haka Allah yake lamarinsa, su Iyayenka suna k'in auren kamar su mutu, sai kuma Allah ya jefa maka matsanancin sonta irin son da sai a littafi nake jin sa. Sai dai zan ja kunnenka duk tsananin bak'in cikin da mutum yake ciki ba'a son ya hora kansa da yunwa kuskure ne babba yin hakan." Ya kalli b'arin da Saudat take ya ce "Maza Saudatu samo masa tuwo, Allah yasa ka iya cin cimar ta mu ta yaku bayi." Da sauri ya ce "Zan ci Abba ba abinda zai fito daga gareku na kasa cin sa komai kashinsa ka san ba hali na bane." Ya fa'da yana duban Sauda ya ga irin reaction 'din da zata bayar. Ranta a b'ace kamar ta kurma ihu ta mik'e ta je zubo masa tuwon. Abban Ya kalleshi ya ce "Sai ka ci abincin maza ka tafi gida gobe ka zo mu yi maganar kamar yarda na ce ai ba da'di ka ga ka shiga hak'kin waccan matar yanzu haka ko lokacinta baka bata ba?"  Hisham ya girgiza kai shi tuni ya wurgar da lamarin Fareeda a gefe da tunanin ita ce matsalarsa a rayuwa. K'asa ya yi da kansa kafin ya ce "Nagode Abba amma ina neman alfarma a bar ni na ga Sauda ko da na mintuna ne." D'an Jim Abban ya yi kafin ya ce "Bakomai ba zan hanaka ganinta ba, tunda har yanzu tana amsa sunan matarka, amma don Allah ina so na baka shawara, kada ka bi son zuciyarka ka bi umarnin mahaifanka don samun rabauta duniya da lahira, hakan kuma shine abin alfahari a gurin duk wani mutum da ya amsa sunansa 'da na gari."

Hisham runtse idonsa ya yi yana jin kamar ya fashe da kuka da yana tunanin samun sassauci A wajen Abban ashe har yanzu yana nan a kan bakansa. Sam ko ka'dan ba ya buk'atar jin wa'dannan furucin daga bakin Abban gani yake ma kamar ya k'osa ne burinsa kawai ya sakar masa y'a kamar yana masa kora da hali.

Jin shirun nasa ya yi yawa hakan yasa Abban dafa kafa'darsa ya ce "Be calm My boy, ka zama namiji mana mai dakakkiyar zuciya mai 'daukan k'addara ko wace iri ce, rashin Sauda ba shine k'arshen farin ciki ba, kana da wata matar idan ka yi biyayya ga iyayenka sai ka ga ta zame maka sanyin idaniya. Ina sake fa'da maka rashin Sauda ba shine zai zama yankewar farin cikinka ba."
Da sauri Hisham ya hau girgiza kai yana fa'din "Abba da gaske Sauda itace farin ciki na kuma idan na rasa ta wallahi na rasa farin cikina, tsananin son da nake wa Sauda rashinta zai iya zama barazana ga lafiyar jikina da ma rayuwata gaba 'daya. Ko a yanzu ji nake kamar zuciyata zata fashe ina ga na rubuta mata takardar saki da kai na, ya rabbi kada ka nuna min wannan ranar. Don Allah Abba ka amince min mu bar k'asar nan da Sauda, ba zai zama aibu ba don na bijirewa iyayena akan wannan abin babu bi ga abin halitta cikin sab'awa mahalicci. Cikin tsananin tashin hankali yake furucin, ga duk mai imani idan ya gan shi a lokacin dole ya raunana zuciyarsa ya baka tausayi. Harta Sauda da Ummanta sai da ya karyar musu da zuciya. Sauda ta cusa kanta cikin filo tana kuka ji take kamar ta tashi ta bi Hisham 'din da gudu su bar garin.
Ga mamakinta sai ta ji Abban yana cewa "Hakan ba zai yiwu ba Hisham, a wannan karan ya kamata nima na nuna an b'ata min rai cin kashin ya yi yawa. Annabi (S.a.w) ya umarcemu da mu yi hak'uri amma kuma miciji baya sarin mutum sau biyu a rami 'd'aya sai ka zama bagidaje. Ya kuma ce idan an b'ata maka ya kamata ka nuna. Ka bi umarnin mahaifanka ka ji Allah kasa mu dace." Ya fa'da yana k'wallawa Sauda kira "Zo Sauda ki kawo masa abinci bara na 'dan fita wajen su Malam lawal."
Jikin Hisham a sanyaye ya mik'e ya ce "Ki kawo min mota." Ta 'dan zumb'uri baki kamar ba zata ba Abban ya ce "Maza mana Sauda, hanzarta ki kai masa a wannan gab'ar dole sai an lallashi zuciyar Hisham tana dabaibaye da rauni. Kafin a samu ya sakeki idan aka yi masa da zafi abin ne zai masa yawa ya rasa ya zai saka kansa abinda bahaushe yake cewa rana zafi inuwa k'una. Don haka ki bi shi ta lislama abu 'daya na sani nima a wannan karan zan nuna k'wanjina ba zan amince da komawarki gidansa ba kamar yarda iyayensa basa so." Umma ta gya'da kai cike da tabbatarwa ta ce "k'warai kuwa Malam, dama nima abinda nake so ka gane kenan, ya kamata mu ma a wannan karan mu nuna musu mun san mutuncin kanmu"

Saudat jikinta a sanyaye ta dinga jan k'afa kamar wacce k'wai ya fashewa a ciki. Sam jikinta babu laka ta fita da kwanukan tuwon zuwa wajen motarsa.

Hisham yana kwance a cikin motar ya mik'ar da kujera ya ji tana k'wankwasawa. A hankali ya sauke glass 'din motar ya zuba mata tsumammun idonsa duk da ba kwalliya bace a fuskarta ta masa kyau matuk'a da gaske. Cikin dauriya ya ce "Shiga mota a bu'de take." Saudat ta cije ta tsaya ha'de da 'd'auke kai ta ce "Ba buk'atar shiga nake ba, ga abincin." Hisham ya mayar da kansa ya kwanta ya ce "Idan ba zaki shigo ba, mayar da abincin bana ci ai na san yanzu ba so na kike ba nine nake hauka na a kan ki." Ya fa'da wata mak'alalliyar k'walla tana shirin zubo masa. Tausayinsa ne ya kamata sosai sai dai sam bata amince hakan ya bayyana a kan fuskarta ba. Ta ce "Maganar so ko rashinsa duk wannan ba mahallinsu bane, tunda abu ne sananne da ka riga ka sani iyayenka sun gindaya katanga mai 'karfin gaske tsakanina da kai bana son ka sab'awa umarninsu, don haka don Allah ka daure ka jure ka rabu da ni."
Cikin zafin rai Hisham ya tashi motarsa ya bar Sauda da abinci a hannu. Ta san ya kai matuk'a a fushi don haka ta runtse idanunta hawaye suka fara mata ambaliya. Da sauri ta shige gida.

Da mamaki Abbanta yake dubanta "Ya naga har kin dawo? Har ya ci abincin?"  Ba ta iya amsawa ba sai 'daga kai da ta yi ta dire kwanukan abincin ta fa'da 'dakinta da sauri.
Murmushi kawai Abban ya yi ganin ita ma har yanzu tana son mijinta.

Ita kuwa zaman 'yan bori ta yi a kan gado ha'de da runtse idanunta Hisham kawai take hangowa lokacin da hawaye yake zubo masa ta dinga jin kamar ta tashi ta bi shi gidan ta rarrasheshi tausayinsa kawai take ji. Sai dai ba zata amincewa komawa gidansa ba ta sha alwashin nunawa iyayensa ba kwa'dayin abin hannunsa take ba....


Daga Taskar Jikar Nashe.❤️❤️🙏😊

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now