49

112 7 0
                                    

Zumuncin Zamani...

Na

Nazeefah_____Nashe.

............

Ga mahmud lamarin ya fara jirkita tunaninsa kullum cikin nadama da tausayi yake, duk da har a lokacin zuciyarsa bata daina Jin tsananin son Fareedah ba, ji yake kamar ma yanzu ne son nata yake sake bunk'asa a zuciyarsa, hakan yasa zuciyarsa ta dinga tunanin Allah yasa Hisham 'din ya sako masa Fareedan shi kuwa da ko ta wane hali sai ya mallaki Fareedan a matsayin matarsa. Shi a karan kansa ya san abinda ya aikata 'din bai kyauta ba, Amma ya kasa tuge Fareeda daga cikin ransa. Ya lumshe ido hawaye na bin idanunsa bai San wace irin k'addara ba ce mai girma take bibiyarsu shi da Fareedan da Allah ya saka musu matsanancin son junansu.

Ya dinga tunanin ko Hisham ta gayawa iyayensu ko kuma ya saki Fareedan kamar yarda yake fata. Ya ji zuciyarsa tana k'arfafa masa gwiwar ya je ya tambayi Mommy a wajenta ka'dai zai San gaskiyar zancen.

__________

Jin wani abu ya fa'do mai 'dan girma daga gabanta ya tabbatar mata ta samu miscarriage, ta runtse idonta tana addu'ar samun sauk'in azabar da take ji. Da k'yar ta bu'de idonta tana kallon 'd'an tayin da ya fa'do daga cikinta har an soma masa halitta, ta bi jinin da kallo gaba 'd'aya Ya b'ata mata k'asan toilet 'din Allah yasa ta yi dabarar shiga toilet 'din da haka 'dakinta zai yi kaca-kaca da jini. Ta na'de 'dan tayin a zani tana fa'din Allah nagode maka da bai zo a raye ba, da da wani idon zan dubi jama'a?

_________

A tsaye ya tarar da Mommyn tana gyara 'dan kwalin kanta a jikin mudubi. Da ido Mommyn ta bi shi ganin jikinsa a salub'e ba k'wari sam a tare da shi. "Kai Moody lafiya na ganka haka sukuku da kai?" Ta fa'da tana k'are masa kallo daga sama Har k'asa ganin sam baya cikin kwanciyar hankali, sai yau ma ta lura da irin ramar da ya yi.

Ya 'dan girgiza Kai "Bakomai Mommy ina Jin headache ne ka'dan."

Tab'e bakinta ta yi don idan duk jikinta kunnene ba zata yarda ba, murya a sark'e ta ce "Idan ta yi wari ma ji ai."

"Yaya Hisham kuwa ya zo gidan nan?" Ya jeho mata tambayar yana k'ok'arin saka nutsuwa a ransa.

Tana cigaba da abinda take a jikin mudubin ta ce "Yazo, har ya koma inda ya fito.. wani abin ne?"

Ya girgiza Kai "A'a na zata ba ya gari ne? Matarsa fa?" Ta sake juyowa tana kallonsa da mamaki a fuskarta "Ina ruwanka da matarsa kuma?"

Ya 'dan ji fa'duwar gaba "Kafin ya ce a'a na zata tare suka tafi ne, akwai kaya na da nake son 'daukowa a gidan." "Ba tare suka tafi ba, ta ce ba zata bi shi ba.." wata kyakykyawar ajiyar zuciya ya saki da yasa har Mommy ta juyo tana kallonsa. Ya yi saurin ficewa don kar ta Jeho masa wata tambayar da zai kasa amsa mata.

Kansa tsaye shai'dan yana sake ingiza shi ya ja motarsa sai gidan Hisham. 

Tun daga falon k'asa yake k'wala mata kira "Hello Sweety na."

Jin muryarsa ya sa gabanta fa'duwa ta jefar da comb 'din da ta gama take gashin kanta da shi... cikin taraddadin an ya ba gizo muryar Mahmud 'din take mata ba? Idan banda haka me zai dawo da Mahmud gidan nan ko giyar wake ya sha?

Har saman ya hau cikin karsashi da k'warin gwiwa, wannan karan ya shirya tsaf ko da Hisham zai gan shi ba zai gudu ba zai tsaya ya bayyana masa irin son da ya kewa matarsa, waye ya ce ya sake ta wasarere? Ya barta kal mu'allak'ati?

Ya tura 'dakinta da ya san nan ne mallakinta, da sauri ta waro ido tana ja da baya cikin firgici.

Yana murmushi ya dinga bin ta, har suka dangana da bango cikin shauk'i kawai ta ji ya ha'da ta da jikinsa."

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now