17

118 7 0
                                    

Zumuncin Zamani.

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

(Typing: Fad'ima Sabi'u D'ankaka. Allah ya raya mana Meenah Yasa musulunci ya yi alfahari da ita.)

Ko da asuba Yan'uwansa da suka tashi ba su ganshi ba Basu kawo komaii a ransu ba, saboda sun san shi da hanzarin tafiya masallaci don haka Abban yace yanzu haka ya tafi masallaci,malam Khalil kenan, akwai ibadah sosai zuciyarsa ta d'anfaru da son addini don duk ya fi ku." Babu Wanda ya ja da zancen Abba murmushi kawai su ka yi, don sun San gaskiya ya fad'a.

Hankalinsu bai fara tashi ba sai da 12:00 na rana ta yi ba khalil babu dalilinsa, don haka Abban ya d'an tashi hankalinsa don yasan Khalil din bai tab'a aikata haka ba, ya kira mahamud yace maza mu fita neman sa ko ma ina yake don Khalil bai tab'a aikata haka ba." sa'eed ne ya fito daga d'akin su a guje yana hawaye ya ce "Abba Y.Khalil guduwa ya yi ka ga takardar na ganii ina shara.
Abba hannunsa na rawa ya karb'a,ya fara karantawa, shi ma hawaye ne ya fara suntiri a fuskarsa su Saudat da Umma sak suka yi suna son su ji me Abban zai ce.
Yana gama karantawa ya goge k'wallar idanunsa ya kalli umma ya ce khalil ya ce ki yafe masa ya kasa jurewa ya tafi nema.
Saudat kuka ta saka ita ma haka umma.
Abba yace ku yi masa addu'a don Allah ku daina kuka, Allah ya kare min khalil a duk inda yake, ubangiji ka bashi sa'a a kan duk abinda yake nemaa Allah kada ka nufe shi da aikata mummunarsana'a, fashi,mafiya, ta'addanci zamba cikin aminci, ubangiji ka kare min Shi."
Umma ameen kawaii take cewa, hawaye yana bin fuskar ta ce na yafe maka Khalil, daman ba ka yi min komai ba, Allah yasa wa  abinda duk zaka je nema albarka." Saudat kuka take sosai, ita ma da nata burin a ranta.

*******

Babu inda Hisham ya yanke sawarar su had'u sai a makaranta, ya san tana da lecture yau don tunda yake kai ta makaranta ya samu time table dinsu
A jikin wata bishiya ya yi parking zuciyarsa nata bugawa don gani yake saudat d'in sam ba za ta saurare shi ba, Yana d'aga kansa kuwa bayan an fito daga lecture din ya hango ta cikin nutsuwa take tafiya, da sauri ya fito daga mota nan da nan idon y'an matan Jami'a ya fad'a Kansa,  sai dai sam Hisham bai lura da su ba, har sai da ya je gaban Saudat ya tsaya Yana ta zabga mata murmushi.
Saudat ta gimtse fuskarta don sam yanzu ba ta son alak'anta da shi . Tana son sa amman ba za ta iya aurensa ba saboda tana gudun tijara da wula'kancin danginsu.
Hisham ya zuba mata Ido ganin sam ba ta yi murna da ganin sa ba yace "My Angel lafiya? ko ba ki yi murnada ganina ba?"
Ta sake had'e rai sosai ta ce "Y.Hisham ina son gaskiya alak'armu ta tsaya daga nan saboda sam had'inmu da kai ba Zai tab'a yiwuwa ba, ni ma yanzu na yi nazarin haka, kowa ya tsaya a inda Allah ya ajiye shi."

Hisham ya k'ura mata ido zuciyar sa na zafi ya ce "Sauda kada ki yi min haka, na samu na shawo kan kowacce matsala sannan yanzu ki sake zuwa min da wata har kike cewa kowa ya tsaya a matsayin sa? Don Allah saudat kada ki k'ara min zafi."
D'aga masa hannu ta sake yi cikin zafin rai ta ce," Y. Hisham ka k'yale ni kaje ka auri zab'i n iyayanka ni ma zan nemi daidai da ni takala d'anuwana na aura"

Shiru Hisham ya yi mata yana mata kallon mamaki da jin furucin da yake fitowa daga bakinta Yana kallo har ta b'ace masa amman ya kasa katabus zuciyarsa ce take masa wani irin k'una, ko a mota ya dad'e shiru yana tunani,da kyar ya ja motar ya wuce.
Gidan su saudat d'in ya tafi ya sake dosar Abba da zancen.
Har cikin tsakar gidan ya shiga ya tarar da umma zaune ta zuba uban tagumi don tunda Khalil ya bar gidan ta rasa sukunin zuciyar ta, da sallamarsa ya shigaa umma ta d'ago kai cikin sakin fuska ta ce "A'a Hisham ne" shi d'in ma cikin murmushi yake ya ce Wallah Umma ya sake bin gidan da kallo yana sake jin rad'ad'i a  ransa.
Umma ta mik'e ta shimfid'a masa tabarma yana zama ya gaishe ta ta amsa cike da kulawa, sannan ta ce "Dafatan lafiya ko?"
Ya d'an rusunar da kai kafin ya ce  lafiya umma Abba yana nan ne?"
Umma ta girgiza kai kafin ta ce yanzu ya fita ina jin ya biya d'auko Sauda ka san yanzu adaidaita sahu yake ja"
Da sauri Hisham ya d'aga kai adaidaita sahu ummah?  Ido yana kawo ruwa ya fad'a. Umma ta ce  "To ya za'a yi Hisham, rayuwar kenan,duk ta yadda tazo wa mutum ya karb'e ta kawai mun gode wa Allah ma da ya bar mu da rai da lafiya wasu ma suna can cikin rashi Kuma ba su da lafiya ba magani babu abinci, su kuma su ce me Hisham?" Cire hularsa ya yi yana goge zufar da take keto masa daidai lokacin Abba mustapha ya shigo sanye da rigarsa ta shadda tsaf da shi mutum mai kamala, Saudat ce a bayansa,tana ganin Hisham ta tsuke fuskarta tsaf ta yi wa ummn sannu da gida, ta d'an kallo Hisham ta gaishe shi.
K'ura mata ido kawai ya yi ba tare da ya amsa ba.
Saudat ta shige d'aki ranta fal k'unci ita kam yanzu sam babu burin aure a ranta, burinta ta yi karatu mai tsayi yadda zata tallafi iyayenta.
Abba ya gyara zamansa sosai yace Hisham d'an albarka yau Kuma ranar aiki na ganka da rana haka?"
Hisham cikin sanyin jiki yace "Abba  ina wuni?"
Abba ya ce "Lafiya lau Hisham ya na ganka haka in ce dai lafiya ?" dariya umma ta yi tace ka ganshi Nan tunda nace masa kana jan adaidaita sahu yake Hawaye."

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now