48

102 6 0
                                    

Zumuncin Zamani...

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

Ya zama cikakken namiji babban mutum, Kana ganin Khalil zaka kira shi da matashin Alhaji, saboda yarda Naira ta bayyana a jikinsa k'uru-k'uru, daga kayan sa yake sanye da shi zuwa motar da yake cikinta sun bayyana matsayinsa a wajen mutane. Ya ajiye k'asumba sosai a gefen fuskarsa.

Gidansu da suka koma a ranar da ta gudu ya bar gidan ganin ba zai iya zama iyayensa na wahala ba, nan ya dinga bulayin nema, Allah ya taimakeshi ya gane gidan, sai dai yana zuwa aka sanar da shi iyayen nasa Sun ta shi 'dan su Khalil ya siya musu gida. Mamaki ya kama shi jin abinda mutumin ya ce wai shine ya siyawa iyayen nasa gida, gabansa ya dinga fa'duwa ya dinga addu'ar Allah yasa ba wani ne ya yi amfani da sunan sa ba ya sace masa iyaye. Ya kalli mutumin "Yallab'ai ko ka San gidan da suka koma?" Mutumin ya girgiza Kai "K'warai kuwa, ai Malam Mustafa mutumin ne, an yi zaman lafiya da shi a unguwar nan, kaf unguwar nan ba Wanda zai ce maka bai San mahallin da Mustafan ya koma ba, sai dai ko y'an hassada, mu je maza na raka ka." Khalil cikin Jin da'din yabon da mahaifinsa ya samu ya ce "Mu je Baba ka raka ni, nagode sosai."

Ko a mota sake yabon Abba Mustafa Malam Lawal yake duk da bai San waye Khalil 'din ba a wajen Abba Mustafa, ya San dai yana ganinsa Sun ha'da alak'a tabbas da Abba Mustafan don zahirin kamanninsu sun nuna hakan.

Suna parking ya dinga bin gidan da aka ce na mahaifin su ne da kallo, duk da kasancewarsa matsakaici Amma yana da kyau ainun. Jiki a sanyaye ya shiga k'wank'wasa gate 'din, cike da murna da zakwa'din son ganin wani daga cikin ahalin gidan da yake mafarkin gani ya fito.

Umma Maryam tana gyara y'an shukar da suke tsakar gidan ta ji bugu, da 'dan hanzari ta k'arasa bakin k'ofar tana fa'din "Wanene?" 

Farin jin muryar mahaifiyarsa ya hana shi magana, sai zabga murmushi kawai yake sai Wanda suke tare ne ya ce "Mune, Maryama bu'de bak'i ne."

Umma da sauri ta Zare sakatar jin ya ambaci sunan ta duk da bata shaida muryar ba ta San dai Wanda ya Santa ne.

Yawan bakinta ne ya kusa 'daukewa ganin Alhajin mutumin da yake tsaye a bakin k'ofa mai kama da Khalilunta. Ta dinga murtsika ido tana son ta tabbatar da gaske ne ko kuwa gizon da Khalilun ya Saba mata ne. "Wa nake gani wannan kamar Khalilu na."

Ji ta yi kawai ya rungumeta yana sakin hawayen farin ciki "Ni ne Umma, Khalilunki ne ba wani ba." Da sauri UMMA ta shiga furta "Alhamdulillah, dama Khalilu kana raye? Ashe zaka dawo Khalil? Ashe zan sake gani fuskarka? Allah nagode maka, Malam fito ga Khalillulahin ka ya dawo." Yarda take maganar da k'arfi ne ya bawa Abba Mustafa daman ji, don haka da sauri ya fito har yana cin tuntub'e. Khalil ya bi shi da sauri ya tare kafin ya kifa, ya ja Abban jikinsa ya rungume cikin tsananin farin ciki da murna. Shekaru biyu ai ba wasa bane, Khalil ya sake cika kamanninsu da Sa'ad ta sake bayyana sosai da sosai. Kullum zancen Sa'ad yaushe 'dan uwansa zai dawo? Ashe ba zai gan shi ba, Ashe Ubangiji ya raba ganawarsu. Tunanin da Abba Mustafa yake yi kenan a ransa sai ya ji k'walla na son zubo masa musamman da ya tuna shak'uwa irin ta Khalil da Sa'adu, don shi Sa'adu mutum ne mai barkwanci baya fa'da da 'y'an uwansa kowa na sa ne, kulawa yake ba su da soyayya mai tsayawa a rai, mai sanya a kasa mantawa da mutum ko bayan rasuwar sa ko da kuwa shekara nawa ya yi da rasuwar (Da wannan damar nake cewa Allah ka ji k'an mahaifina da D'anuwana Daddy ku yi musu addu'a da bakunanku masu albarka tukuicina kenan gareku masoyan Jikar Nashe. NAGODE Allah yasa ku yi min wannan karar.)

Khalil suka zauna gaba 'daya kan daddumar da Umman ta shimfi'da musu har Malam Lawal da ya rakosu.

Malam Lawal 'din ya dubi Abba mUstafa yana Murmushi ya ce "Malam Mustafa ina tayaka murna da dawowar 'dan mu."

Abba yana murmushi ya ce "Nagode Malam Lawal, Nagode sosai da sosai." Suka sake gaisawa sosai kafin Umma ta kawo musu kunun zak'i da kunun ayan da take siyarwa. Malam Lawal ya sha kunun sosai kafin ya  kalli Khalil ya ce "Ikon Allah kamanninsa da marigayi Sa'adu har ta b'aci don da Kai suke kama sosai da sosai."

Da sauri a kuma razane Khalil ya 'dago yana kallon Malam Lawal Jin abinda yake fa'da, ya mayar da kallonsa kan Abba cikin rawar murya ya ce "Ab.....ba....Sa......Sa'aduna ya rasu?"

Abba cikin tausyawa ya janyo shi jikinsa murya a raunane ya ce  "Khalillulahi Sa'adu ya rasu watansa biyu cif da rasuwa, sai dai baya buk'atar kukan ka, domin Sa'adu ya yi shahada ciwon ciki ne ya kashe shi."

Ina ya saurari wannan bayanin Na Abba, tuni ya kifa Kansa a kafa'dar Abba ya sakar  masa wani kuka mai cin rai. Umma k'asa ta yi da kanta itama tana sakin nata kukan.

Khalil ya sha kuka sosai duk Annurin da yazo da shi tuni alhinin mutuwar Sa'adunsa ta 'dauke shi tsaf, ya tuna irin abubuwan da ya siyowa Sa'adun kasancewar sa ya San 'dan gayu ne yana kuma son cimar k'asashen k'etare hakan yasa ya siyo masa tarkacen abubuwan cimaka iri-iri, Ashe Sa'adu an zama samarin aljanna.

Jikin Malam Lawal a sanyaye ya musu sallama, bayan Khalilun ya ba shi ku'di duk da Dollar ce sai da ya masa bayanin a kan ya je a canja masa kuma idan aka canja su ku'din zai Kai kimanin dubu 'dari da ashirin.

Jikin Khalil ya mik'e a sanyaye ba tare da ta bi ta kan abincin da Umman ta ajiye masa ba. Ya nufi can 'dakin da yake gefen tsakar gida da ya San nanne na samarin gidan.
So yake ya watsa ruwa ko ra'da'din da yake ji a zuciyarsa da sassan jikinsa zai ragù.
Abba da Umma suka bi shi da kallon tausayi, Abba ya ce saura Saudatuna ko ya zata ji idan ta ji mutuwar nan?"
Umma tayi k'asa da kanta kawai tana addu'a a ranta Akan Ubangiji ya la'ddafa musu gaba 'daya.

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now