20

114 9 0
                                    

Zumuncin Zamani

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387

(Continuation. A yi hak'uri da aka ji ni shiru kwana biyu dalili mai k'arfi ne ya rik'eni. Nagode da jumurin saurare)

Cikin tsananin zafin zuciya Hisham ya dafe kai  cikin ransa ya ce "Shikkenan tawa ta sameni wata Sabuwa Sauda bata son kishiya." Ya lumshe idanunsa shi kansa bata san a dole zai had'a mata biyun don hakan baya cikin tsarinsa.

Saudat kuwa cikin gigitar Lamarin ta fad'a cikin gida ta ci sa'a Abbanta yana nan bai shiga d'akinsa ba. Da sauri ta zube a gabansa ta fashe da wani irin kuka na tayar da hankalin duk mai saurara ta. Da sauri Abbanta ya mik'e yana sake dallareta da torch light yake fad'in "Lafiya Sauda? Me ya faru?" Kukan sosai take kafin ta saki ajiyar zuciya idanunta jajir ta dubi Abban cikin sark'ewar harshe ta ce "Abba na fasa aurensa, na shiga uku Abba kuna sane Abba za ku kaini gidan da za'a kashe ni da bak'in ciki wayyo Allah....."

Takaicinta ya sa Abban ya kasa ce mata komai illa zuba mata ido da ya yi yana tunanin irin amsar da ya dace ya bata. Don bai zaci zata yi irin wannan wautar da shirme har haka ba. Sai da ta d'an nisa daga kukan sannan ya ja ajiyar zuciya bayan ya kawar da kwanon abincin da yake gabansa ya ce "Kin gama kururuwar? Ashe zuciyarki bata sakankance da cewa duk inda kike ubangiji shine wanda ya kamata ki nufa da lamari mai girma irin wannan ba? Imanin bai kai ki gane cewa ba bu wanda ya isa ya cutar da ke ba matuk'ar kin yi rik'o da addu'a Sallah da karatun Alkur'ani da salatin Manzon Allah, kin ba ni mamaki kishiya ki ke tsoro Saudat? Kishiyar da take mace kamar ki?"

Da sauri Saudat ta girgiza kai "Ba kishiya nake tsoro ba Abba, sharrinta,kaidinta da makircinta nake tsoro, da kuma matsalar da zan fuskanta da danginsa tunda zuciyarsu ta Riga ta fifita kud'i fiye da zumunci." Abban ya dad'e yana nazarin kalamanta tabbas ya san tana kan turba sai dai baya son ya nuna mata tasa gazawar hakan yasa cikin kwantar da murya ya ce "Kada ki manta Ubangiji da kansa yake maganin Makircin mutane tunda da kansa ya ce "Wa makaru wa makarallah Wallahu Khairul makireen, ki rik'e Allah a ranki Sauda ba abinda zai sameki In sha Allah ki tattara kaidin nata da makircin da na su gaba d'aya ki mik'awa Allah ki sha mamakin yarda ubangiji zai yi yak'i da su akan zaluntarki da suke son yi, ai shi ya fad'a idan bawa na ya rik'e ni ya kusanceni ya kuma yarda shine mai yi to shi Ubangijin zai zame masa jin sa da yake ji da shi ganinsa da yake gani da shi takunsa da hannayensa gaba d'aya sai Allah ya zama shine yake yak'i da dukkan wanda zai zalincesa ki yi rik'o da Sallah da Alkur'ani ko bayan raina zaki tuna da ni nace ba abinda zai sameki matuk'ar kin zamo mai jajirtacciyar zuciya wajen ibada. Amma ina tabbatar miki babu maganar fasa aurenku, a zuciyata ina so ki zame musu aya ki zame musu abin misali ko sa hankalta su kuma fad'aku."

Tsaf Cikin d'akikai kad'an Sauda ta shanye kukanta, zuciyarta ta sanyaya matuk'a da gaske da kalaman mahaifinta, tabbas samun mahaifi na gari ya fi samun mahaifi mai tarin dukiya a yau kam tana alfahari da zamowarta tsatson Mustafa. Ta share hawayenta sannan ta yi k'asa da kanta tana antayawa mahaifinta godiya da ya kub'utar da ita daga sharrin shaid'an mai tunzira zuciyarta. A zuciyarta ta hak'kak'e cewa lokacin barci tuni ya k'ure mata ya zama dole ta jajirce da addu'oi da k'iyamallaili da azumi gami da nafilolin dare da rana dafatan Allah ya mata katangar k'arfe daga dukkan abin k'i da idanu ababen zargi.

Shi kuwa Hisham har tsakar dare ya kasa samun nutsuwa da sauk'in zuciya wani irin So ne yake dagargazar ransa na halitta d'aya Sauda. Ga shi duka k'ok'arin kiran wayarta da ya yi ya gaza samunta, duk bayan mintuna sai ya gwada kiranta sai dai amsa d'aya wayar take ba shi a kashe take. Yana jin wani iri a ransa duk a dalilin yanayin da ya barta ya san tana ciki matuk'ar damuwa musamman kasancewarta mace mai zafin kishi. Fatansa d'aya Allah ya sassauta zuciyarta ya saka Mata ha'kuri da juriya. Shi kansa ya san aurenta da zai yi abu ne da zai janyo mata matsaloli a rayuwa Ba daga danginsa ba masu k'wad'ayin Naira ba daga dangin kishiyarba masu tak'ama da arziki. Abu d'aya ya sani ba zai bari a wulak'anta ba zai jajirce matuk'a da gaske wajen ganin ya k'watar mata y'an cinta, zai kuma zama mai share mata hawaye In sha Allah a duk yayin da wani ya cusguna mata zuciya.

***************

Hajiya laraba sun dawo daga dubai d'auke da kaya masu d'inbun yawan gaske tamkar wanda za'a kaiwa y'ar shugaban k'asa. Shi kansa Alhaji Hamzan sai da ya yi mamakin yawan kayan, sai dai duka zuk'atansu ba su kawo tunanin a raba a bawa Sauda ba. Ita da Inna Falmata suka dinga waya had'e da sanar da shi ya zo ya ga kaya don gobe suke saka ran kai kayan. Cikin siyayyar har da mota wanda Hajiya Laraban da Inna Falmata ne suka had'a kud'in motar a matsayin ta su gudumawar mota y'ar gaske da ta amsa sunanta na mota k'irar rav 4.

Bayan gajiya da nacin kiran wayarsu ya shiga cikin gidan fuskarsa babu wata walwala. Idanunsa ya zube akan tsibirin kayan da ke gaban mahaifiyarsa tamkar wanda za'a bud'e shago. Bai dai yi magana ba ya d'an tab'e bakinsa had'e da k'arasawa ya zauna yana gaishesu. Daga haka ya ja bakinsa ya tsuke Inna Falmata ta dubeshi da murmushi "Hisham ka ga kaya Ma sha Allah ba kace komai ba." Hisham ya mayar da idanunsa kan kayan a shagub'e ya ce "Ai ba sai na ce komai ba, in dai sun muku shikkenan, amma ina ganin kamar kayan sun yi yawa mai zai hana a raba musu da Sauda?" A zabure gaba d'aya suka d'ago suna kallonsa kamar su rufeshi da duka Inna Falmata da ta tunzira da takaicinsa ta jefeshi da filo "Ka idonka wannan kayan ya yi kama da kayan da za'a kai gidan Mustafa? Wai hauka ne a kanka Hisham, ka san adadin dukiyar da aka kashe kake cewa a d'auka a kai inda ba'a san darajarsu ba balle a mutunta su? Kayan da ko gidan shugaban k'asa aka kai sai sun jinjinawa k'ok'arinmu kake cewa a kai wannan akurkin gidan?" Mommynsa kuwa tsaki ta ja kafin ta ce "Ke kika kula shi Hajiya, yo wannan gidan ya fi a kai musu akwati uku da d'an kit, dubu d'ari uku ma tsaf zata had'a lefen gidan nan kuma a kai su yi murna had'e da zakwad'i su nunawa jama'a." Dariya sosai Inna Falmata ta yi kafin ta ce "Wallahi kam, to dangin uwa duk talakawa ai Mustafa ya cucemu da ya auro y'ar matsiyata ko da yake kansa ya cuta ga shi nan tsiyar tana ta binsa a guje." 

Tsananin mamakin lamarin su da son zuciyarsu ya saka Hisham sakar baki yana kallonsu a zuciyarsa yake tunanin tabbas idan ka na duniya zaka sha kallo' har ya kasa jurewa ya magantu ta hanyar cewa "Amma kuwa idan na bari aka aikata haka tabbas na tabbata mara adalci, ita wannan an mata lefen miliyoyi ita kuma sai a mata na dubu d'ari uku haba Mommy kada son zuciya ya kai ku halaka mana, su ma fa talaucin nan ba su suka d'orawa kansu ba kuma babu wanda yafi k'arfin Allah ya jarrabeshi kamar yarda ya jarrabi Abba Mustafa."  Ba wani tasiri da kalamansa suka musu cikin confidence Inna Falmata ta ce "Ai kuwa hakan ba zai zama rashin adalci ba, kuma ko tsarin musulunci ma aka bi shine daidai tunda cimarsu ma ba d'aya zaka dinga ba su ba, kowa zaka ciyar da ita ne da irin cimar da take ci a gidansu ka kuma tufar da ita da kalar ta ta tufar...." A zafafe kamar ya kai mata duka ya ce "Ba dai tsarin musulunci ba sai dai idan aka bi son zuciya" da sauri Mommynsa ta ce "Kai Hisham saurara rashin kunya zaka mata? Saboda an tab'a zuciyarka d'iyar gwal." Ya sake b'ata rai ya ce "Ni ba rashin kunya zan mata ba gaskiya ce zan fad'a mata." Daga haka ya mik'e zai fice daga d'akin Mommynsa cikin b'acin rai ta sake kiransa ya juyo kad'an sai dai bai dawo ba saboda suyar da zuciyarsa ta ke masa Ko Falamata baya son gani, tunani yake yau da ya na da damar da zai sake Iyaye tabbas da ya sake na sa iyayen da ba komai a ransu sai son zuciya. Ita kam sam bata lura da yanayin da yake ciki ba ta ce "Sai ka kawo dubu d'ari ukun da za'a had'awa y'ar gidan Malam Musty lefe." Muryarsa a shak'e ya ce "Zan kawo" akwai kud'in a jikinsa amma ba zai ba su ba, zai je ya had'a da kansa akwai matar abokinsa da take siyar da komai na mata tafkeken shago ne ma da ita a can zai je ta had'a masa kuma ko k'yalli daga cikin kayan ba za su gani ba, idan sun san wata ai ba su san wata ba, ko kud'insa kaf za su k'are itama sai ya mata irin lefen da suka yi wa y'ar mai kud'in. Inna Falmata ta tab'e baki kafin ta ce "Laraba kin yi sake an gama miki da d'a tsaf kamar yarda Matar Mustafa suka tsubbaceshi a allunan almajiran makarantar Ubanta,sai kin tashin kin yi da gasken gaske Hisham ya yi nisa baya jin kira." Hajiya laraba ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce "Ai kuwa sun yi a banza idan a tsaye suka kwana ni a tafe na kwana. Mu zuba ni da su a yi auren dai mu gani sai sun gwammaci kud'i da karatu wallahi."


Daga Taskar Jikar Nashe.❤️❤️❤️

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now