51

120 8 2
                                    

Zumuncin Zamani.

*****

Da daddare Umman Sauda ta shirya rantsatstsen abinci mai rai da lafiya. Suna gama cin abincin dare ta dubi Baba da take zama da Sauda "Baba, bari na tashi na tafi dubiyar nan kafin ABBAN Sauda ya yi fushi da ni don tun safe yake jaddada min zancen zuwa dubiyar nan." Ta fa'da tana sanya hijabinta da ya rufe mata har k'afafu dama yanayin shigar tata kenan." Baba ta ce "Ki je ai zuwan naki yafi rashin zuwan amfani ko ba komai kin watsa musu aniyarsu."

Ta fice da sauri bayan ta saka Khalil ya 'dauki Kwan don data zuba manyan filasan da ta zuba abinci Wanda Khalil ne ya taho mata da su daga Dubai, irin Royal flask d'in nan ne masu tsada.

Asibitin cike da 'y'an dubiya kamar me kasancewar lokacin ba'a San bai lashe zab'en ba, ba kuma a San ya k'arar da kadararsa ba ko da yake ko da Sun sani za su zo don Hisham.

Abba Mustafa yana zaune a wajen, ba Wanda ya masa koda kallon banza dalilin an gan shi da shiga mai kyau Wanda ko gidan gwamna zai iya zuwa a haka. Yana ganin Khalil y'a saki murmushi ya ce "Mu je daga waje Khalil. Dama tun 'dazu nake jiran k'arasowarka mu je ka yi aikin lada." Ya tasa shi a gaba suka fice direct wajen biyan ku'di suka je, sai da suka isa sannan ya kalli 'dan nasa ya ce "So nake ka biya ku'din asibitin nan Khalilu, bai kamata a bar Hisham da 'dawainiya shi ka'dai ba." Khalil bai yi musu ba ya karb'i bill 'din asibitin ya gani ba wani jinkiri ya zaro ATM ya basu suka zari iya adadin ku'dinsu. Suka bashi shaidar biya.

Suna komawa 'dakin Hisham ya dawo bayan Sun gama gaisawa da jama'ar 'dakin ya juya da sauri ha'de da fa'din bari na je na biya ku'di na dawo Daddy." Da sauri Khalil ya zaro takardar ya mik'a masa "Ba sai ka wahalar da kanka ba Yaya Hisham na biya ku'din ai ga receipt." Ya fa'da yana mik'a masa takardar Hisham ya zaro ido "Haba dai Khalil ku'din da yawa ai bai kamata na bar ka da biyan ku'di har 280k ba." Gaba 'daya 'dakin sak su kayi jikinsu ya yi sanyi musamman da suka ji Khalil ya ce "Haba Yaya Hisham ai ku'din basu da wani yawa kada ka ji komai ai Nima Baba nane. Allah dai ya bashi lafiya."

Abba Mustafa shi ya goge Alhaji Hamzan tas da towel da ruwa mai 'dumi yana yi yana masa nasiha da yarda da k'addara mai kyau ko mara kyau shine cikar imanin mutum." Alhaji Hamza dai ba magana sai bin Mustafan yake da kallo yana mamakin zuciya irin ta Mustafa mai manta Sharri. Hawaye ne kawai suke zuba a idonsa, ba bakin da zai nemi gafarar Mustafan.

***********

Fuskarsa a murtuke take yana tsaye yana zagaye su da idanunsa a karo na biyu idanuwansa Sun sake masa mummunan gani. Jikinsa na rawa ya isa inda Mahmud da Fareeda suke a tsakiyar gadon Fareedan sai shek'a dariya suke suna buga soyayyarsu. Ganinsa ne ba zato ba tsammani ya ka'da y'an hanjinsu, Fareeda da sauri ta ja bargo ta rufe jikinta sai zaro ido take tana mak'yark'yata. Mahmud 'din ya janyo cikin wani mummunan yanayi ya fara jibgarsa. Dukansa yake kamar zai Kai shi lahira a yarda yake Jin zuciyarsa zai iya hallaka Mahmud 'din wato bai damu da rashin lafiyar ubansa ba yana nan yana holewarsa. Jibgarsa yake sosai har sai da ya ga ya suma sannan ya dawo kan Fareeda da duk jikinta yake rawa a tunaninta Hisham 'din ya kashe Mahmud ne. Kallonta kawai yake ya ma rasa wani irin hukunci zai mata, idanunsa sun ka'da Sun yi jajur sai kawai ya juya da sauri ya ja k'ofar 'dakin ya kulle da 'd'an mukulli, dama wancan karan rashin takamaimai shaida ne ya saka ya k'yalesu yau kuwa ya samu. Ya Zare 'd'an mukullin yana danna kiran wayar Baban Fareeda ya zama dole ya sanar da shi, don kada ya zata don ya yarda Babansa a zab'e ne ya yiwa y'arsa sharri.

Sule jami'i ganin wayar surikin nasa sai gabansa ya fa'di ya fara tunanin ko Hamza ya rasa rayuwarsa ne da sauri ya amsa yana fa'din "Hisham ne ya jikin Babanka?" Hisham murya a raunane ya ce "Da sauk'i" Sule Jami'i ya saki ajiyar zuciya Jin ba abinda yake tunani bane, sai kuma ya cigaba "Hisham Babanka ne baya Jin magana, ka ga yarda ta kaishi sai mu ce Allah ya kiyaye gaba." "Ameen Daddy, Don Allah idan ba matsala ina so ka biyo ta gidana akwai abinda zan nuna maka game da iyalina." Gaban Sule Jami'i ya fa'di ya ce "Allah yasa dai lafiya shikkenan bari na zo yanzu dama muna shirin zuwa duba babanka ne." "Okey sai kun zo ya fa'da yana kashe kiran." Gumi duk ya zubo masa ya dinga jin zuciyarsa na wani irin 'daci da zafi. Da kyar ya samu ya ja sawayensa zuwa cikin falon ya zauna a saman carpet kansa a kan cinyoyinsa.

Har sa da ya ji bugun k'ofa ya tabbata kuma Mahaifin Fareeda ne jikinsa a salub'e ya isa don bu'de musu k'ofar falon.

Tunda suka shigo Alh. Hamza yake rarraba ido haka kawai ya ji hankalinsa bai kwanta da wannan kiran na Hisham ba. Balle ya zo ya ganshi firi-firi da shi ba alamar kwanciyar hankali tattare da shi. "Kai Hisham lafiya kuwa? Me ya faru? Ina ita Fareedan?" Bai musu magana ba illa komawa k'ofar 'd'akin da su Fareeda suke ya saka key Ya bu'de k'ofar sannan ya ce "Ku k'araso Daddy idanunku su gane muku irin badak'alar da ake yi a gidana." Ba Daddy ba wannan karan Har Mommy sai da ta ji muguwar fa'duwar gaba. Suka k'arasa k'ofar 'd'akin in da suka tarar da Fareeda hankalinta tashe ga Mahmud yana kwance y'a farka bayan Fareedahn ta shek'a masa ruwa.

Alhaji Sule ya na ganinsu Ya San mai suka aikata ba sai ya buk'aci k'arin bayani ba, Innalillahi kawai yake ja yana jin kamar zai kifa saboda tsananin ru'dewa da ya yi. Hisham Ya ce "Ba na kiraku don na 'daga muku hankali bane, ba kuma yanzu na fara ganinsu ba, sau biyu kenan ina kama su, ina kuma da k'wakkwarar shaida don tuni na kafa na'urorin camera a gidan ba tare da saninsu ba idan kuna da buk'atar gani zan iya saka muku. Don haka Daddy ka gafarceni Amma na saki Fareeda saki Uku..." ya fa'da wasu hawaye na zubo masa. Mommyn Fareeda cikin takaici ta zubawa y'arta ido kafin ta shak'ota ta fara jibgarta "Zina da aure Fareeda? K'in cuceni Sam ba irin tarbiyyar da na baki na kenan na shiga uku yau ni Sa'a ina zan saka kaina?" Hawaye wani na bin wani. Alh. Sule kuwa ji ya yi da wannan mummunan labarin da ya ji har gwara a gaya masa bai ci zab'e ba y'arsa ta cikinsa da aikata zina.. Zinar ma da aure "Kin cuceni Fareeda? Kin cuceni yau ina tarbiyyar da na bak? Kika zi zuga da ru'din shai'dan kika aikata son ranki..." Da sauri Fareeda ta zube a gabansu tana wani irin kuka nadamar duniya yau ta shigeta "Ka yi hak'uri Abba idan ma da laifina shima Hisham da laifinsa tunda ya aureni bai damu da ni ba balle ya sauke min hak'kina?" "Shi yasa kika zab'i zina akan ki zo ni ki gaya min idan ta kama a raba auren ma sai a raba da wannan ba'dala da kika aikata ko kin zo kin gaya min?" Ta girgiza kai tana sake sakin kuka tana jin ina ma k'asa ta tsage ta shige. Shi kansa Mahmud tarin nadama ne a tare da shi da kunyar mutanen wajen ya dinga da na sani.."

Alhaji Sule ya juya kan Hisham "Kai ma Hisham da naka kwamashon zunubin a cikin zunubinsu, me yasa zaka sarayar da hak'kin matarka? Da ka bata hak'kinta na tabbata ba zasu tsunduma kansu a wannan 'd'abi'ar banzar ba, ka yi kyan kai da baka sanar da kowa ba don da ban san da wani idon zan kalli jama'a ba.."

Hisham Ya sunkuyar da kai yana jan istigfari a zuciyarsa don tabbas Ya yarda shima da nasa laifin kamar yarda ya ce "Daddy ina ganin wannan maganar ta zama sirri tsakaninmu ba sai an gayawa kowa ba, saboda kare Martaba da mutuncin ahalinmu idan yaso sai taje ta yi idda a 'daura musu aure.."

Alhaji Sule ya ji da'din wannan shawarar ta Hisham ya dinga kuma girmama zuciya irinta Hisham idan wani ne ai ba zai tab'a yafe musu ba, Tabbas Hisham Ya cika 'dan albarka ya taimakeshi k'warai ta hanyar rufe wannan babban sirrin ya tabbata da sai ya shafi siyasarsa. Godiyarsa ya dinga zubawa Hisham kamar zai Goya shi.

Cikin jin nauyi Mommynta ta dinga juya girman Ubangiji a ranta a da auren y'arta da Hisham ma ba son sa take ba ta raina arzikinsa ta fi son yarinyarta ta auri wani k'usan gwamnati sai ga shi Allah ya juya lamarin ta auri k'asa da Hisham ma, tabbas hukumullahi la ajabun Allah yasa mu dace.
Ta saki ajiyar zuciya tana kallon mijinta da yake jiran cewarta "Tabbas hakan ya yi shine kuma marufin sirrin mu, dafatan Wannan zai zama izina gareku da ku da masu hali irin naku, ita duniya yanzu ita take gyara mutum, kai kuma Hisham Allah ya saka maka da alheri ka k'ara hak'uri a kan Wanda kake yi."

Bakomai" Ya fa'da yana mik'ewa takardun gidansa ya mik'awa Mahmud a cikin wani dogon file murya a raunane ya ce "Ga shi nan ka rik'e tunda dama ka mayar min da gida naka."

Da sauri Mahmud Ya fa'da jikinsa yana sakin wani irin kuka mai tsima zuciya "Ni Butulu ne Yaya Hisham na maka sharri ka saka min da alheri da wani irin ido kake so na dubeka Yaya Hisham." Hisham ya 'dan bubbuga bayansa a hankali kafin ya ce "Ka dubeni da idon da kake duba na koda yaushe Am still Hisham ban canja ba, kuma rama alheri da sharri halin Manzon Allah ne ina fata na dawwama a haka. Kuma na San ba Wanda yafi k'arfin ya fa'da komar shaid'an Allah ya kiyayemu." Daga haka ya mik'e ya ce "Daddy zan koma asibiti sannan na manta in sanar da ku Saudatu ta haihu." Fareeda sak ta yi tana kallon Hisham tana jin wani irin yanayi a tare da ita dana sani take da na sani mata amfani musamman da ta ji ya ce Sauda ta haihu ashe har yanzu suna tare da sauda?


(Waye zai iya abinda Hisham da Abban Sauda suka yi? )

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now