24

112 7 0
                                    

Zumuncin Zamani...

Na Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387

Wattpad @Nazeefah381

Daga k'ungiyar Elegant Online✍🏽

****************

Haka dai lamarin biki ya kankama daga b'angaren amarya Fareeda. Sauda kam babu abinda take shiryawa da ya wuce harkar walimarta da saukar Alkur'ani.

Fareeda dai tanadi sosai ta yiwa bikin. Events biyar ta shirya na kece raini akwai Rainbow day, Ladies Night, Dinner, Mothers Night, da kuma Bridal shower.

Ita kuwa Saudat walimar ma sai ranar da za'a d'aura auren sannan zata yi ta, saboda su gajartawa kansu hidima.

Babu wanda yake bibiyarsu a sha'anin bikin da y'ay'an Inna Sahura sai na Inna Maryam, duk danginsu kowa yana can gidan su Hisham inda ake son zuwa bikin kece raini.

Su Zainab d'in Inna Sahura ne suka dubeta cikin takaicinta ta ce "Wallahi Babyn nan kin kwafsa mana, da tuni muna nan muna hidimar biki amma kin ce wani nan Dinner kawai ke za ki yi. Ni dai yau wallahi Dinner Fareedah zan tafi na je na kashe kwarkwatar idona, wannan wajen na kece raini a Amani event center fa za'a yi." Sauda da murmushi a fuskarta ta ce "Sai kun dawo, ni kam ba da ni ba gad'a a kabari. Bana ra'ayin wad'annan bidio'in banzan. Ba abinda suke janyowa sai kwashe albarkar aure, tunda Allah ne kad'ai ya san Fasadin da ake aikatawa a wajen. Cakud'uwar maza da mata haramun ba da ni ba."

Tab'e baki Zainab ta yi kafin ta ce "Kanki ake ji, baki da aikin yi sai wa'azi, lokacin abu ayi shi wallahi bikina sai an gwangwaje." Saudat da mamaki take kallonta ta ce "Wa'azin ne rashin aikin yi? To Allah ya kyauta A dawo lafiya ai ban hanaki ba."

K'arfe 8:00 na dare Hisham ya kirata daidai lokacin yana ta shirin dinner a gaban dressing mirror da yake gabansa. Tana d'agawa ya saki murmushi had'e da cewa "Uwargidana ya aka yi?" Ta d'an lunshe idonta kad'an kafin ta ce "Bakomai Y.Hisham." Ya saki murmushi ya ce "Ban yarda ba da komai, ni tunaninki ne ya cika min k'irji yasa na kiraki, ke ba kya missing d'ina?" "Mhmn" kawai ta ce tana sake k'ank'ame wayar a kunnenta jin yarda husky voice d'insa ke neman tafiya da nutsuwarta. "Menene Hmnnm, feel free ki yi magana Malama bana son k'aiyanci fa." Ya fad'a cikin sigar tsokana. Ta marairaice murya ta ce "Just tunanin ka." "Ya wuce just." Ya fad'a yana dariya "Me kake yi?" Ta samu kanta da jefo masa tambaya ya d'an yi Jim kamar ba zai gaya mata ba, sanin halin mutuniyar tasa sai dai ya na son ya ga wannan kishin nata, wani irin farin ciki yake ji ya san son da take masa ne yake janyo wannan zafin kishin don haka ya ce "Kin ganni nan ina shirin tafiya Dinner.." Tsit ta yi wani abu ya tokare mata a k'irji ta kasa had'iyeshi d'if ya ji ta kashe wayar.
Hisham ya bi wayar da kallo yana sakin murmushi ya sake dialling numberr sai dai bata d'aga ba daga k'arshe ma sai ya ji ta kashe wayar gaba d'aya. Ya girgiza kai yana jijina zafin kishi irin na Saudat.

********.        ***********.

Mak'il wajen dinnerr ya cika, kai daga ka shiga ka san biki ake na girma harkar ta manyace, Naira ta sha kashi a jikin mutane da dama kowa ya sha shigarsa ta kece raini.

Hisham zaune kawai yake a wajen dinnerr amma hankalinsa gaba d'aya yana kan Saudat, duk da ga Fareeda a gefensa kuma ta sha matsanancin kyau kamar y'ar tsana. Mintuna kad'an ya sake dialling numberrta amma stiil a kashe take.

Ita kuwa Saudat tana can zuciyarta na wani irin turirin kishi don ta san tabbas yanzu suna tare yana can ba mamaki yana zuba mata kalaman soyayya. Ko ma har ya rik'e hannunta oho.... Ta d'au wayar a zafafe ta shiga kiransa, sai dai an samu Akasi har ta gama ringing bai ji ba bai d'aga ba, hakan ya k'ara hura mata tunaninta na yana can ya manta da ita ya luluk'a duniyar masoya ya za'a yi ya ji kiranta?

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now