46

128 12 1
                                    

Zumuncin Zamani....

A bakin gate 'din gidan su Saudan Ya tsaya, saboda dama ya san gidan tun sanda ya siyeshi kuma Abban ya yiwa sha'awarsa sai dai ya san ko zai mutu Abban ba zai karb'a ba sai da wannan dabarar ta zo masa.

Gidan tas tun daga harabar gidan yake ji k'amshin girki, da gani babu tambaya suna cikin walwala sab'anin wancan lokacin, hakan ya sa ya ji da'di a ransa, fiye da lokutan baya da yake jin 'daci cikin ransa idan yazo ya tarar da su cikin k'uncin rayuwa.

A filin ya tsaya yana kwarara sallama, Wanda hakan yasa Umman Sauda ya fito da azama jin Muryar Hisham 'din tana ganin shine kuwa ta saki fara'a "Lalala! Maraba da Hisham, Abban Sauda fito kaga bak'o daga sama."

Abban Sauda shima da sauri ya fito daga falon sanye cikin wani yadi fari tas da shi, jikinsa ya yi tas fuskarsa har ta 'd'an washe ka'dan ba wannan duhun na bak'in talauci da ya yi musu dabaibayi.

"Maraba da Hisham, daga ina haka kamar an jefoka daga sama?"

Hisham ya zube gwiwoyinsa a k'asa yana gaishesu cikin tsantsar ladabi. "Daga Abuja Abba, Sauda ma tana can tana gaisheku ba zata iya doguwar tafiya bane shi yasa.."

"Dama Ina ita ina doguwar tafiya ai ina jin watan gobe ne watan haihuwar ta ko? Idan lissafin bai b'ace min ba." Umma ta fa'da tana kau da
Kai alamar y'ar kunya ka'dan na bayyana a saman fuskarta. Hisham ma cikin kunyar ya 'daga kai.

Kitchen ta shiga ta ha'dowa Hisham 'din kunun gya'da da na ayar da take siyarwa har da fura. Sai sinasir da miyar taushe Allah yasa ta gama shi da wuri da zafinsa shi ta musu da rana. Ta ajiye tray 'din a gaban Hisham. Ya dinga kallon kwanukan kamar dama ta San yunwa yake ji. Ba kunya ya ja kwanukan ya ci abincin sosai a ransa yana fa'din "Dole Sauda ta iya girki ashe gado ta yi." Sai da ya ci ya k'oshi nak kunun ayar mai sanyi ya sha ya bar kunun gya'dar a flask da zummar sai zai tafi ya tafi da shi da furar.

"Ya muka ji da hak'urin mu?"

Maganar Abba ta shiga kunnuwan Hisham a bazata. Da sauri Hisham 'din ya 'dago yana kallonsa gabansa ya fa'duwa ya ce "Hak'uri kuma Abba? Waye ya mutu?"

"Sa'adu 'dan uwanka." Hisham bai San sanda ta waro ido ba Yana fa'din "Sa'ad fa kace Abba? Yaushe ya mutu? Ya aka yi kuma ba mu sani ba?"

Ya fa'da k'wallar idonsa na gangarowa. Abban ya dake sosai baya son shima ya saki kukan kamar yarda Hisham da Maryama suke yi.

"Sa'adu baya buk'atar kukan ku Hisham, addu'a kawai yake so. Satinsa uku da rasuwa. Ciwon kwana biyu kacal ya yi Allah ya 'dau abin sa Allah ya ji k'ansa ya gafarta masa. Abinda ya sa ban sanar da kai ba Saudatu nake ji, bana son 'daga mata hankali saboda shine mafi soyuwa a wajenta a cikin y'an uwanta. Idan ta haihu sai a sanar da ita Amma yanzu kam ina jin tsoro. Allah ya raba lafiya yasa ita zata haifa min wani Sa'ad 'din."

Hisham Ya share k'wallarsa yana amsawa k'asa-k'asa.

"Ya aka yi ka samun labarin mun dawo nan?"

Abba ya yiwa Hisham tambayar da ta saka shi saurin 'd'ago kai.
Ya yi azama ya ce "Na je can gidan, sai suke sanar da ni kun ta shi su suka bani kwatancen nan 'din."

"Haka ne Khalilu ya fansheka ya siya mana gida don na San tuni kake da wannan burin... bakomai Hisham Allah ya baka ladan niyya." 

"Ma sha Allah" Hisham ya ce kamar bai San komai ba. Tsawon lokaci suna sake jima min rashin Sa'ad kafin su yi sallah da Abban ya kuma yi musu sallama, don ganin lokacin tafiyarsa zuwa Abuja ya yi don ta jirgi zai bi ya san kuma zuwa lokacin jirgin ya zama ready.

Har waje Abba ya rako shi yana sake jaddada a gaisar min da autata. Hisham ya dinga amsawa yana murmushi ha'de da saka ledar tarkacen Sauda da Umma ya ba shi na su kuka kayan ka'di dai da su Daddawa. Kamar ta San yanzu Sauda 'din tuwo ne kawai abin marmari a wajenta.


Zumuncin ZamaniTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon