15

103 8 0
                                    

Zumuncin Zamani

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

(Typing: Fad'ima Isa Dankaka. Allah ya yiwa rayuwar Meena albarka ya tsareta daga dukkan sharri.)

(Not edited.)

Ko a aji tunanin da take kenan sai da malami ya shigo ta bude jakar zata dau littafi kawai ta ga rafar kudi.gabanta ya fadi don ta san dai y Hisham ne ya saka mata.ta shiga uku!!! Yanzu me zata ta ce a gida dazai wanke ta daga zargin cewa ba ita ta gayyace shi ya zo wajenta ba?  Gashi Sam ita ba ta iya karya ba, babu ita a tsarin rayuwarta.
Da aka tashi da wuri ta Sami adaidaita sahu ya Kai ta gida cikin sanyin murya ta yi sallama a tsakar gidansu. Gabadaya har yayyenta suna nan. Jikinta ya Kara sanyi ganin yadda suke zaune jugum_jugum ta tabbatar jimamin talaucin da ya yi musu katutu suke take kwalla ta cika idonta, da kyar ta kokarta ta mayar da ita. Cikin sanyin jiki ita ma ta bi bango ta zame ta zauna.

Bayan ta gaida umma da Abba sannan ta bi yayyenta daya bayan daya ta gaishe su. Su din ma cikin matukar kulawa suka amsa. Tana son ta fito da kudiin amman tsoro ya hana ta,da kyar ta kalli ummanta tace,umma me ya faru ne na gan ku jigum _jigum ?
Umma ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce," saudah kenan,me zai faru? Babu abinda zai faru sai alheri muna dai tunane _tunanen rayuwa ne da yadda take neman tsaya mana. Yau yau khalil dako ya wuni nema a kasuwar singa amman da kyar ya samu wai Shima dakon ,yanzu wahala yake saboda akwai mutane da yawa da suke yinsa,har ma wai sai ka yanki form din kungiya."da sauri saudat ta bude ido ta ce "dakon umma?" Khalil ya yi murmushi yace dakon dai saudah ,shima ya zama wata tsiya sai kana da hanya saudat hawaye ya gama zubo mata a dukkan fuskarta tace innalillah wa inna eelaiyi rajun Allahuma ajirni fi musibati wa akhfil ni khairan Minha
Abba dai Yana gefe Yana laziminsa bai tofa komai ba har sai da aka kira sallar la,asar ya mike ya gabatar da nafila, hakan yasa duk suma suka mike suka yi alwala da hanzari. Abba ya ja su jam,I bayan sun idar sun dade suna gabatar da addu,o'i sannnan Abba ya shafa. Yana idarwa ya ce musu yana zuwa,su jira shi kada wanda ya fita.
Hakan kuwa aka y, tsawon awa suna dakon jiran Abba sai can ga shi ya shigo a dan hanxarce ,ya dubi umma ya ce,ke da sauda ku suturce jikinku mutane zasu shigo yanzu "
Basu kawo komai a ransu ba suka mike . Abba kuma ya fita ya shigo da mutanen. Su ummah da ya,yanta kuwa sai gani suka yi ana ta lellekawa gidan.mamaki ya kama umma tare da tunanin kada dai abban sauda siyar da gidan zai yi?
Bata gama tunanin ba malam mustapha ya shigo gidan Yana murmushi ya dube su, lafiya na gan ku tsiru_tsiru kuna jiran ku ji bayani? Umma ta ce yo ba dole ba malam,ka gan mu haka Allah dai yasa hasashena kada ya zama gaskiyah.

Abba cikin sakin fuska yace iKon Allah, ya wuce wai umman sauda na san hasashenki ba zai wuce tunanin ko siyar da gidan zan yi ba, haka din ne zan siyar da gidan nan mu koma na haya saboda mu samu abinda za mu dogara da kanmu. Idan aka siyar da gidan adaidaita sahu zan siya guda biyu,sa,ad tunda bai samu dorawa daga secondary ba zai ja daya ni kuwa zan dunga jan daya,kafun mu ga abinda Allah zai yi.
Tsit suka yi gabadayan yaran kowa da irin nasa tunanin oh Allah kenan, yanzu dai dubi dukiyar irin ta dangin su harda kamfanninka da gidajen mai a cikinsu amma ya illahi babu mai iya tallafa wa iyayenta? Amman sun wayi gari abinda za suci ma nema yake ya gagare su, abbanta ne wai yau da jan adaidaita sahu daman ta sani iyayen ummanta sam ba masu wadata ba ne, kowa ta kanwa yake tunanin saudat take kenan hawaye yana kwaranyo mata ga shi ta rasa yadda zata yi ta fito da kudin nan da Hisham ya ba ta.
Da daddare sam kasa rintsawa ta yi a cikin damuwa take ji take tamkar ta gayawa Hisham amman zuciyar ta kwabe ta saboda ta tuno wulakanci da mahaifinsa ya yi musu har asuba ba ta samu ta rintsa ba.don haka da gari ya waye barci ta sha sosai. Umma kuwa ba ta matsa ba don ta san ba ta samu isasshen barci saboda karatu da take yi .koda ta tashi wanka kawai ta yi tsam ta mike ta dau kudin ta isa dakin ummanta, tasan yanzu yayyenta ba sa nan. Har kasa ta durkusa kanta a kasa ta mike wa umma kudi amma ta bi ta da ido cikin makutar razana da tayi tace, sauda mene ne wanan ? Uban waye ya baki.
Sauda kasa magana ta yi saboda yadda ta ga umma tayi.
Ba kya ji ne sauda nace uban waye ya baki? Bayan kin tafi makaranta ashe bin maza kika tafi."
Da sauri sauda ta dago kai tace umma-------
Umma tace me kike so ki ce? Umma ko gaskiya,gaya min ko talaucin mu ya sa kin siyar da mutuncinki? Saudat cikin kuka tace" wallahi umma ba haka ba ne ko za ki bani kur'ani na dafa.
Sai sananan umma ta saki ajiyar zuciya ta ce to gaya min waya baki uhmm saudatu?
Saudat ta share hawayen ta ce y Hisham ne
Umma ta sake zabura ta kai mata duka ta ce Hisham? Hisham fa kika ce? Yanzu duk wulakancin da ubansa yayi mana a gidan nan bakiyi zuciya kin fita daga harkarsa ba saboda kina kwad'ayin sabin hannunsa? Wallahi sam ba ki gado ni ba,da kin gado ni wallahi da ko yinwa zata kashe ki ba zaki karbi ficikarsa ba, bari babanki ya dawo zan sanar masa
Saudat tace wallahi umma ban san ya zuba min ba , cewa ya yi kawai ya ga jakata ina lura da karatu a makaranta? Shi ne na bashi. Wallahi ban san ya saka ba
Umma ta gyada kai tace to sanar dani uban waye ya ce ki hadu da shi a waje ba nan hana ki kula shi ba? Meyasa sauda ba zaki kiyaye mana mutuncin mu ba?
Umma wallahi na daina kula shi
A to idan kin yi haka kin nuna ke yar halak ce, daga haka umma ta mike da kudin a hannunta ta cilla cikin sif ta sake duban yar tata tace sai malam ya dawo na nuna masa na ji abin da zai ce, ki dai kiyaye ina sake fada miki.
Sauda ta daga kai ita ma ta mike ta shige daki kwanciya ta yi sosai ta shiga tunanin shi kenan yanzu ta rabu da Hisham rabuwar da take tunanain ita ce ta har Abada.

Alhaji hamza da sassafe ya tashi ya yi shigar alfarma saboda yana son ganin senator da wuri don jiya ya samu wayar senator akan Yana son ganin sa a kan maganar auren ya,yansu. A guest house dinsa ga same shi, kamar koda yaushe senator cikin fara,a ya tare shi tare da yi masa kirarin tsokanar da yake masa, kansancewar senator Mai son barkwanci ne,  cikin barkwanci ya ce hamza maso kudi ina kaje kudi ina zaka kudi.
Alhji hamza ya saki murmushi hade da cewa fadi kanka tsaye, honourable kudi kam za mu neme su ko da ya_ ki Haram ya_ki halak. Wallahi ko a ina suke sai mun nemo su
Senator yace," a yi addaua' dai Allah ya ba da masu amfani.
Gaskiya ne yallabai Amman marasa amfanin ma da ranar su.
Dariya senator ya yi a zuciyar sa Yana mamakin son kudi irin na alhaji hamza.bayan ya tsagaita da dariya yace hamza ka san dalilin da ya sa na nemi son ganin ka?
Alhji hamza ya girgixa Kai.
To daman ba wani abu bane jiya na koma gida sai na tarar fareeda tana ta kuka na tambayi ba,asi ka san mata nan da mahaifiyar ta shiga rattabo min bayanin wai Hisham ya ce ba fareeda zai aura ita kadai ba,har da yar kaninka haka ne batun?
Alhaji hamza tsit ya yi kamar ruwa ya ci shi
Har senator ya kosa ya sake tambayar haka din ne hamza.
Alhaji hamxa yace wallahi yallabai halin yaran zamani ne sai su. Yanzu ma maganar da nake maka an janye batun yarinyar don har gida na je naci wa mahaifinta mutunci na kuma sanar da shi ba Hisham ba yarsa don haka yanzu batun fareeda ne kawaii.
Sosai senator yake duban sa, baki a bude don tsananin mamaki yace hamza kaciwa dan uwanka mutunci saboda me? Akan danka na son yarsa yanzu har ka fi kaunar bare fiye da danuwanka na jini? Wal iyazubillah , zamani ya lalace wallahi.
Da sauri alhaji hamza ya gyra zama,aa yallabai ba wai ina kin sa bane Allah ya sani talaucinsa nake gudu.mustapha  kashin tsiya ne dashi duk cikin gidan mu shi ne ba shi da kashin arziki . Shi ya sa nake tsoro kada Hisham ya rabe shi arzikinsa ya nukurkushe. Don duk wanda ya rabe shi wallahi tamkar iska haka arzikinsa ya ke zama. Ko sama ko kasa a neme shi a rasa sai dai ka wayi gari ka ga mutum ya dawo talaka. To kaji dalilin da yasa na hana Hisham ya rabe shi.
Cikin matukar takaici senator ya sake zuba masa ido Yana sake mamakin yadda a yanzu duniya ta susuce ta zama sai lahaula wala kuwwata. Cikin takaici yace hamza saurareni da kyau . Wallahi ka bani mamaki haka Ina ganin ka wayayye ashe jahilci ne damkam a kwakwalwarka don Allah ka taba halartar islamiyyah kuwa? Haba har yaushe jininka jininka hamza kake gudu saboda talauci? To tsaya ka ji, fareeda ta fasa auren Hisham makutar ba su biyu zai hada ya aura ba don haka shawara  ta rage gamai shiga rijiya daga haka ya mike ya fice daga gidan inda ya bar alhaji hamza cikin zuzzurfan tunani amuncewa ko akasin hakaa?
Jikinsa a sanyaye ya yi parking a harabar gidan daidai lokacin Hisham shi ma yayi parking .wani kallo mahaifinasa ya watsa masa yana yi masa sannu da zuwa ma ko kallon sa bai yiba ya shige gida Hisham ya dan saki murmushi don ya lura ya bata wa mahaifinsa rai.
A falo ya samu Haj laraba ita din ma ba ta samu fara,a wajensa ba. Har sai da ta ga yanayin mijin nata sam babu walwala hakan ya sa ta ce alhji lafiya kuwa Allah yasa dai ba cewa yayi an fasa ba?
Alhaji hamza ya yi tsaki yace yo kusan hakan ya ce mana tunda kiri_ kiri ya rantse ya sake rantsewa sai dai Hisham ya hada su duka biyun idan ba haka ba shi ba zai ba da auren yarsa ba.ni kuwa da ya je ya jajibowa kansa talauci wallahi gwara na hakura da auren yar tasa.
Hajiya laraba ta zaro ido tace wai kasan me kake cewa kuwa alhji ai ina ga haka ba mafita ba ce, ka bari kawai ya aure ta idan ya so mu san hanyar damuka biyo mata, wanda dakanta sai ta gudu ta bar auren,amman ai sam ba za mu ga samu mu ga rashi ba...
Alhaji hamxa ya sake zabga tsaki kafin ya ce wallahi Hisham akwai yaron banza,duk shi ya jawo mana wanan matsalar.
Hajiya ta sake cewa haka dai za ka hakura a lalla'ba ayi kafin daga baya mu samo hanyar dafawa.
Alhaji hamza ya sake zabga tsaki.
Shi kuwa senator sule Jami'i ba abinda ya dinga yi a ranar irin tunanin yadda aka wayi gari mutane sunyi wa xuminci rikon sakainar kashi abin da yake tunawa kenan kawai. Yana kuma sake mamaki a ransa to daman haka Al,amarin ubangiji yake a duk inda aka samu gurbacewar Al,umma ba a rasa na gari.
Shi kam sule Jami,I ya riki zuminci rikon kwarai a rayuwarsa. Kuma yana matuk'ar girmama zuminci, ya kuma riki duk Yan'uwansa a matsayi daya, masu wadatar cikin su da talakawan cikinsu,har ma ya fi taimakawa talakawan fiye da masu kudin, saboda a cewarsa ba zai Kara wa mai karfi karfi ba..
Shi ya sa ma yan uwan nasa suke matukar son sa, kuma suke ji da shi sam ba sa shayin kai masa matsalarsu, don sun san zai share musu hawaye, ya riki zuminci sosai a kowanne wata takalawan cikin su yakan kai musu kayan abinci matan cikinsu kuwa yakan raba musu dubu ashirin _ashrin wanann a xaune take a cikin record dinsa. Koda yaushe kuwa shine mai biyan kud'in registration ko school fess ya kai samari da yawa cikin danginsa k'asashen waje don su yi karatu boko su kuma ko a
Samu su taimakawa iyayensu a duk lokacin da suke zama wani abu.

Jikar Nashe...

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now