11

129 7 0
                                    

Kusan mintuna biyar suna knocking a bakin k'ofar sashen nasa bai bud'e ba, kamar ya san da ita aka zo ya d'au lokaci kafin ya bud'e, fuskarsa a d'aure yake dubanta, yana mamakin yarda lokaci d'aya ta birkice masa kamar ba Hamdan da ya sani ba, mai son sa da jin maganarsa, ta bi ta hau maganar Didi ta zauna a kai kamar wani fad'ar annabi, idanunsa cikin nata yana k'are mata kallo, kallon da ya takurata ta sunkui da kai, gaba d'aya kallon ya saka mata wata irin nutsuwar da bata shirya yinta ba, ita kuwa Sa'ada dariya ce take son kamata ganin yarda ma suka manta da ita a wajen har sai da ta yi gyaran murya sannan Hammad ya ankare ya saki wata malalaciyar ajiyar zuciya kafin ya mik'a hannu ya amshi basket d'in abincin da yake hannun Sa'ada ya ce "Je ki abinki Sa'ada akwai aikin da
Zata min yanzu zata taho." Hamda tayi raurau da idonta kafin ta ce "Wallahi Didi tace min kada na dad'e ka ga fad'a zata min." Ya watsa mata wani irin kallo da yasa Sa'ada wata irin dariya ta so kub'uce mata ta juya da sauri ta wuce don ba su saba y'ar wasa da Yaya Hammad d'in ba, amma kallon da yake jifan Hamdan da shi abin so ne ga kowacce mace mijinta ko saurayinta ya dinga mata shi, kallo mai nuna zallar so da nuna kewa ga wanda akewa shi, hannunta na rawa ta mik'a masa flask d'in kunun "Please Yaya Hammad ka karb'a kafin kasa Didi ta tara min mutane..." "Masifar Didi da tsinuwar mala'iku wanne kika fi gudu? Idan ba zaki shigo ki je kawai." Hawaye ne ya fara k'ok'arin zubo mata kafin ta saka k'afa cikin falon gabanta na fad'uwa, ta tsaya cak a bayan kujera shi kuwa tab'e bakinsa ya yi ya cigaba da zuba abincinsa lura da yayi da ko cewa ya yi ta zuba masa yarda take a tsorace ba zata zuba ba, shi har mamakinta ma yake kada fa ta zamo masa bagidajiya ba irin Nanna da take kanainayeshi ba, da sonsa da ba son ransa take fincikar ra'ayinsa sau tari. Ya fara kurb'ar kunun idanunsa suna yawo a kanta ta ji yace "Wani sabon salo kika samu? Sai kace sabon aure ba zaki dawo nan kusa da ni ki zauna ba? Saboda kina tsoron Didi ko?" Ya taune leb'ensa d'aya kafin ya furzar da huci ya ce "Idan kika ce haka zaki min wallahi a gadon Didin zan zo na karb'i hak'kina haka kawai saboda wata bidi'a ta banza da wofi ki yi ta d'aukan zunubi da azimin nan, ke kika jiyo ni ina da wata matar yau ma rashinta ne yasa nake binki duk da ba ni na jawoki ba, ke zaki je ki yi ta kwana rungumar filo ai dama Sabonki ne tun kina budurwa."
Wani irin kallo take jifansa da shi kamar ta zunduma masa ihu jin abinda yake ce mata, ita zai gayawa wani yana da mata ai ta fisa sani dama ita ta kawo kanta har da zai tsaya ci mata mutunci, haushi da takaicin kalamansa yasa ta juya a zuciye ta fice daga falon duk da tana ji yana k'wala mata kira. Ya saki ajiyar zuciya yana jin takaicin yarda bakinsa ya ja shi ya sake b'allowa kansa ruwa ya santa sarai da d'an banzan kishi, ba waya a hannunta balle ya kirata.

Tana zuwa falon ta tarar da bak'i a falon Didin atamfofine da laces da shaddodi take ta bud'ewa, sai wasu akwatina biyu da kit a gefe, kasancewar zuciyarta ba dad'i yasa ta yi k'ok'arin shigewa d'aki bayan ta gayar da bak'in mazan da suke zaune. Didi ta ce "Ke Hamda zo nan ai sak'on naki ne, KK ne ya aiko ko da yake wannan ni ya aikowa ya ce a rabawa dangi, wancan akwatinan dai su ne naki." Hamda ta koma ba don ta so ba ta hau bud'e kayan sabuwar wayar tafi tafiya da imaninta wacce take cikin kit d'in sai dantsatsetsiyar sark'ar gold wacce da gani babu tambaya dollars ta sha kuka wajen siyanta, akwatinan kuwa laces ne dandatsa-dandatsa da atamfofi super sai mayafansu HD Veils da jakunkuna uku da takalmansu, a ranta ta yi farin ciki da kayan amma yarda zuciyarta take tunzira da kalaman Hammad yasa fuskarta bata nuna ba, Sa'ada kuwa sai tsalle take tana d'aga Iphone 14 pro max tana cewa wallahi yarinya kin shigo gari. Bata tab'a komai a kayan ba ta mik'e ta shige d'aki, tana shiga ta yi wurgi da d'ankwalin kanta gashinta ya wargaje, sai sannan wani kuka mai k'arfi yazo mata, ji take da tana da hali da ta fasa auren Hammad d'in don ita tana daga cikin jinsin mata masu zafin kishi. Kuka ta yi sosai bata fito falon ba har sai da Sa'ada ta shigo kiranta Didi ta tara ayarin gidan wai zata yi rabon kayan sallahr da KK ya kawo.

Fuskarta a kumbure ta fita, duk wanda ya kalli idanunta  ya san ba k'aramin kuka ta sha ba, shi kansa Hammad hankalinsa a tashe yake dubanta ji yake da da hali da ya kai mata runguma ya rarrasheta, amma ina ko arzikin kallo bata samu ba, sai ma harara da ta wurga masa ta yi k'asa da kanta. Abbu ne ya lura da yanayinta ya ce "Zo nan Hamda me ya sameki haka? Naga kamar kin yi kuka?" Girgiza kai kawai ta yi tana k'ok'arin mayar da hawayen da suke son sake zubo mata, murya a dashe ta k'arasa kusa da Abbun tana girgiza kai ta ce "Bakomai had'e da gallawa Hammad harara." Didi ta ce "Kaima dai Ummaru da shirme ka ke, kukan me zata yi banda na farin cikin samun uba kamar KK ga uban kaya da ya d'and'aso mata ga shegiyar waya." Hamda ta zabga mata wani kallo kafin cikin takaici ta ce "Ni ba kukan da nake ba kenan, ke wannan ya dameki ai dama tun kafin Ya zo Abbu yana mana duk abinda muke so." Sosai Abbu da Ammi suka ji dad'in amsar da Hamda ta bawa Didi, idan ita ta manta gwara Hamdan ta mata matashiya kuma ya san ko nan gaba Hamdan ba zata gujeshi ba. Didi ta ce "Y'ar banza mai ido a tsakar ka, duk tsiyar Ki dai da KK d'in zaki tunk'aho.." ta sake zunb'ura baki "Ni wallahi da Abbu zan yi tunk'aho tunda shi ya yi d'awainiya da ni har na girma." "Ke kika jiyo, ba wannan yasa na tara ku ba, kai Hammad tunda Sadiya ta k'i zuwa bak'in cikin duniya ya isheta kaje ka kira min ita ko zuciyarta zata buga sai ta ga wannan kab'akin arzikin, don ina lura da ita tunda lamarin nan ya faru shikkenan Sadiya halin uwarta ya fara bayyana tare da ita, yo uwarta banda dai idan taso mutuniyar kirki ce ai da ba ta zama aminiyata ba, don ko farar k'asa aka shafe min d'aki da ita sai hassadar ta ta nuna, ta dinga nurk'ufanci kenan, sai dai Akwai kyauta, kawaici da alkunya sumumu kasau ce ta gaske.." Hammad ya datsi leb'ensa banda idanuwan su Abbu yau kam da ya ganar da Didi kurenta. Ya saka kai ya fice yana ji tana fad'in "Sai dai hararar duka dai ba zan daku ba, ja'iri mai idanuwa kamar na muzuru."

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now