38

128 9 2
                                    

Zumuncin Zamani

Part 3..

08033748387.

Ga mai neman sa complete daga farko ya danna wannan link 'din zai samu.

https://www.wattpad.com/1326143648?utm_source=ios&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Nazeefah381&wp_originator=vN8yhkTgvkG79FD7P8g%2B8QdvQVOSpRT2VWhGFEfjPLJt98qVYhGfWCF3NlVNN%2Bf0AYbiFUyU4V5qxl1T21VwcwfUZsJAWfQjWmqzhggjbTIA9%2BG8LVeqZFBzXRwAbzJ5

Book
3.

1.

Washe gari da wuri ta farka daga barcin da ya 'daukeshi. Wanka ya shiga Ya yi ya shirya tsaf da shi sai baza k'amshi yake.

Yau ne yake tunanin gabatar da k'udirinsa na k'arshe Wanda yake tunanin shine mafita tsakaninsa da Sauda.

Lallausan yadinsa ruwan madara ya kwanta ya bi lafiyar jikinsa, sai ya sake fitar da ainahin kyawun fatarsa ta chocolate colour. A bakin mudubi ya tsaya yana kallon kansa, shi da kansa ya amince ba k'aramin kyau ya yi ba, duk da Ya 'dan rame ka'dan. Da sauri ya zura hularsa bayan ya kalli agogo ya ga lokaci yana ja.

A falo ya samu Fareeda a zaune ba tare da Ya kalleta ba ya yi hanyar waje, hakan yasa ta bi bayansa da sauri tana k'wala masa kira.

"Hisham! Hisham!!"

Cak ya tsaya yana jin kiran na
Amsa kuwwa cikin majiyansa. Bai juyo ba, itama kuma bata damu da juyowar tasa ba, don yanzu sam ba shi ne a gabanta ba, da tana da iko ma da ta juyar da igiyar aurensa ta koma kan Mahmud, don shine Type 'dinta wanda yake tunanin Ya yi daidai da tsarin rayuwarta da burinta na auren miji masanin Soyayya da iya sarrafa mace, wanda a nata tunanin duka Hisham ya gaza ta wannan b'angaren.

"Na gaji Hisham da wulak'anta ni da kake idan har ka ga zuciyarka bata aminta da ni ba kawai ka sawwak'e min na samu daidai da ra'ayina na aura."

Cikin sauk'in murya ta yi furucin da alama kuma har k'asan zuciyarta iya gaskiyarta kenan.

Cak ya tsaya yana k'are mata kallo kafin ya saki malalacin murmushi murya a sauk'ak'e shima ya ce "Ki jira lokaci."

Daga haka ya saka kai ya fice da sauri Ya bar Fareeda da sakakken leb'e na tsananin mamakin furucinsa me yake nufi da KI JIRA LOKACI? Lokacin me? Shine maganar da ta dinga mata kaikawo a zuciyatrta ba tun yau ba ta San Hisham wani irin bau'dadden mutum ne da ba kowa ke iya fuskantar furucinsa kai tsaye ba.

Tun a mota yake gwada kiran numberr Sauda, amma tana ringing sai dai Saudat 'din ta yi burus da shi. Da alama rabuwar take so da gasken gaske kamar yarda ta tura masa a waya.

Ya sani zuwa lokacin tana makaranta don haka Ya isa makarantar tasu kansa tsaye.

A k'asan bishiya Ya yi parkinga
Motar tasa yana kallon agogo Ya San zata kai 1 hour kafin su gama lectures.

Cikin shigar ta ta nutsuwa da kamala ta fito daga lectures 'din, a gajiye suke sai dai gaba 'd'aya b'acin rai Ya bayyana a kan fuskokinsu sakamakon yajin aikin da aka tafi yau suna shirin zana jarrabawar k'arshe na last semester.

Sam bata lura da shi ba kasancewar ba da motar da Ya Saba zuwa ya zo ba. Ganin tana niyyar wuce shi hakan yasa ta fito da sauri yabi bayanta, hannunta Ya rik'o dalilin da yasa ta juyowa ta ga mai rik'e mata a zatonta ma K'awarta ce Shatun Imran.

Sai dai tuni k'amshin turarensa na yau da kullum Ya ziyarci hancinta ta juyo da sauri idanunsu cikin na juna suna kallon kallo. Ita ta fara janye nata idanun fuskarta Sam ba annuri ta fisge hannunta amma ya masa rik'on da ba zata iya k'waya ba. Fuskarsa babu alamun wasa ya ce "Ko ki tsaya ki bi ni mu shiga mota, ko na 'daukeki cak na saka ki ta dole.. kin san hakan ba zai min wuya ba."

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now