52

191 18 2
                                    

Zumuncin Zamani.

Last page...

Godiya gareku ba zata yanke ba, musamman masoya litattafai na Jikar Nashe Real fans, da na group 'din zauren jikar Nashe. Jinjina ga duk makaranta na whatsapp groups nagode k'warai da ha'din kan da kuka bani.

Sai y'an k'ungiyar Elegant ina jinjina gareku k'warai da gaske musamman ga wacce ta dawo Dani rubutu tsundum wato Nimcyluv nagode k'warai Allah ya sake ha'da kawunanmu.

08033748387.

______

Hisham ya yi parking a tamfatseten gidan Abba Mustafa Wanda Khalil ya siya masa a tudun yola, suka kuma tare a cikinsa a daren jiya. Gida ne babba na gaske da yake 'dauke da babban gate babban fili da bishiyu a jikin katangun gidan.

Kusa da motar Khalil ya yi parking da ta Abba Mustafa da Khalil 'din ya siya masa babba ce sosai k'irar avensis.

Hisham ya dinga bin gidan da kallo farin ciki fal a tare da shi na jin da'din warwarar matsalolin wannan ahalin, ga shi yanzu cikin k'udirar Ubangiji komai sun fi k'arfinsa sai dai ma su bawa wani tabbas bahaushe ya yi gaskiya da ya ce Bayan wuya sai da'di.

A babban falon gidan da yake k'asa ya tarar da ahalin gidan suna zaune suna hira da cin abinci hankalinsu kwance.

Da murmushi Ya shiga idanunsa a kan Muhammad yana tsokanarsa "Babban Yaya ya kamata fa ka shiga daga ciki, ko sai little Sa'ad Ya tashi Ya fara kiranka da Baba na soro?"

Gaba 'd'aya aka tuntsire da dariya, Khaleel ya ce "Abinda nake fa'da masa kenan, Ya samu Ya matsa ko mu ma ma matsa."
Hisham ya zabga masa harara "Kai 'din ma ai ka kusa tashi daga saurayi ka koma tuzuru, ji uwar k'asumbar da ka tara a fuska kamar wani balarabe, dole sai ka nuna mana ka yi zama a cikin larabawa."

Khalil ya gyara zamansa murya can k'asa yake ra'da masa "Ni Ai na kusa azimin bana In sha Allah ina 'd'akina sai dai a bani abinci a baki." Hisham ya girgiza kai yana dungure masa kai "Allah ya shiryeka, maza Umma ta ji ka ni baruwana na yi nan." Ya fa'da yana hayewa sama inda Sa'eed ya ce masa Saudan tana sama.

A kwance ya tarar da ita cikin kwalliya da rantsatstsan lace coffee colour sai zabga k'amshin turaruka take Wanda ta turara su a gabbasa. Ta kafa 'd'auri irin 'd'aurin Zahra Buhari Little Sa'ad yana cinyarta tana shayar da shi. Hisham ya ja ajiyar numfashi yana zube idanunsa cikin nasu, soyayyar Sauda kullum sake huda shi take tan sabunta kanta. Ya k'arasa daf da ita yana rab'a jikinsa a nata yana shak'ar k'amshin turaren Har da lumshe ido. Kafin ya karb'i little 'din ya kwantar da shi "Haka kawai yaro ka bi ka nainaye min mata ka hana ni samun kulawa" Ya fa'da yana jan filo ya kwantar da ita sannan ya bata kyakykyawar runguma wani irin missing 'dinta yake ji. A hankali ta dinga 'dan tureshi "Yaya Hisham ka manta ba gida muke ba gidan surikai ne." Bai kulata ba so yake ya ji ya 'dan kawar da abin da yake ji.  Kukan Little ne Ya ankarar da shi Ya janye jikinsa yana tsaki murya a shak'e ya ce "Ba haihuwar ba yaro ya hanaka hutawa kai da iyalinka kamar ma Sun San me ake sai su wani canyara kuka." Sauda ta k'unshe dariyar da take cinta son ta San yanzu sai ya sauke a kanta.

Ya 'dauko Little 'din ya saka shi a cinyarta kafin ya janyo ledodin da ya shigo da su manya ya ce "Bu'de kiga kayan fitar sunanki, idan da abinda bai Miki ba sai ki gaya min."

Ta mik'a masa little tana jan ledojin idonta a kan kayan ta ce "Yaya Hisham Amma ban so ka wahalar da kanka ba, ka San sarai ina da kayan da Har yanzu ban saka su ba, balle ma ni ba suna zan yi ba." Ya zuba mata ido Har ta 'd'an razana da kallon da yake mata, sai kuma ya yi k'wafa Ya ce "Wahala ko? Ai shikkenan nagode, ki tashi mu je ki duba Daddy kamar Yarda Abba ya ce•" ya fa'da fuskarsa a ha'de sosai don ya ji haushinta ba ka'dan ba, menene amfanin samunsa matuk'ar ba zai kyauttawa iyalinsa ba.

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now