23

106 7 0
                                    

Zumuncin Zamani

Na Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387

Cikin mamaki Hisham yake kallonta a rud'e ya ce "Lafiya Saudaty na ga kin canja lokaci guda?" Saudat ta d'an fitar da numfashi kafin ta kalleshi da idanunta da suka kad'a ta ce "Please Y.Hisham idan muna tare da kai ka daina min zancen matarka yana hurting heart d'ina kana sawa kuma ina jin tsanarta."

Hisham dariya ya yi sosai don ya hango zallar kishi da tarin k'uruciya a idanun Saudat d'in ya ce "Kishi kumallon mata, Sauda me yasa kike da zafin kishi? Ba kya son ina zancenta alhali zaku zauna tare gida d'aya kuna auren miji d'aya ki sassautawa zuciyarki."

A fili Sauda ta d'an ja tsaki ta ce "Dad'in abin kowa gidansa daban ba abinda mai zai had'ani da ita sai na shekara ma ban ganta ba." Da sauri Hisham ya  zare ido yana kallonta "Kai haba sai kace ba y'ar musulmai ba, yanzu dai mu bar wannan maganar mu yi wacce za ta fishshemu kin ji My heart." Tana kallonsa ya dire mata rafar kud'i y'an dubu guda uku akan cinyarta. Da sauri ta d'ago tana kallonsa a d'an razane ta ce "Y. Hisham wannan kud'in na menene? Me zan yi da su haka har dubu d'ari uku?" "Kud'in k'unshi ne kya bari na gama kafin ki tsayar da ni, baki san babu kyau tsayar da miji idan yana abu ba." Ya sake d'ebo wasu kud'in sun kai d'auri bakwai yace "Na hidimar kwalliya d'inki da sauran abinda za kiyi." Da sauri ta tura masa kud'in "Please Y. Hisham Ka barsu wallahi Abba fad'a zai yi." Ya gintse fuskarsa sosai yana kallonta kafin ya ce "Akan me Abban zai yi fad'a don na miki kyauta a matsayin iyalina don na miki abu kawai sai ya yi fad'a don dai fad'an ba wuya. Duk kin bi kin firgice tun ban gama bayani ba." Saudat ta d'an yi kasak'e tana kallonsa har sai da ya yi kamar zai tsokane mata ido sannan ta yi saurin k'iftawa ta saki nauyayyiyar ajiyar zuciya kafin ta ce "Yaya Hisham ai dole na firgita abin ne abin saka fargaba." Hisham ya had'e ransa sosai ya zama serious yana kallonta ya ce "Menene abin tsoro anan? Ko kina tunanin ta wata mummunar hanyar nake samo kud'in?" Da sauri Saudat ta girgiza kai "Ka yi hak'uri idan ranka ya b'aci ni ba haka nake nufi ba." Ya sake gintse fuskarsa ya ce "To kada ki sake min irin wannan, duk abinda ki ka ga na yi, na yi shine don zan iya ba wai fariya ba, kin gane?" Ta d'aga kanta da sauri tamkar ta saka kuka ganin yarda ransa ya b'aci b'aro-b'aro.

Ya sake zaro rafa uku na y'an dubu-dubu ya manna mata a cinyar. "Kud'in anko da hidimar k'awaye lalle k'unshi da sauransu." Shiru ta yi bata sake magana ba illa sun gode da ta ce. Ya janyo wani kwali mai d'an girma ya d'ora mata a cinya "Wannan sak'o ne ki kaiwa Abba katinan d'aurin aure ne, ni zan tafi saura kuma ki kashe wayarki, ki tabbata kin saurari kira na komai dare, bana son mace kasa kin ji?" Ta d'an lumshe idonta tana son kawar da hawayen da yake son zubo mata. Jikinta a sanyaye ta sa hannu zata bud'e k'ofar, tausayinta ya kama shi ganin yarda duk ta razana kanta, cikin wata iriyar murya ya ce "siye Sweetheart y'ar haka ne abin ba sallama?" Ta yi k'asa da kanta ta ce "Am sorry, nagode Allah ya saka da mafificin alheri da arziki madawwami." "Ameen matar Hisham" ya fad'a da sakakkiyar murya. Ta d'an saki ta ta fuskar tana fita da sauri.

A tsakar gida ta tarar da su gaba d'aya har iyayensu. Dukkansu tunani d'aya ne a ransu ta yarda za'a samu kud'in hidimar auren kawai. Saudat ta shiga da nannad'adden kwalin da kud'ad'en da ya bata duka ta dire a gaban Abba.
Gaba d'aya suka d'ago suna kallonta. Abban kuwa idanuwansa ya kafa mata da neman k'arin bayani. Lamarin da yasa Saudat ta shiga rawar murya da jiki ma gaba d'aya ta ce "Wallahi Abba shi ya bani, kuma sai da nace ya barshi ya k'i wai na kwalliya ne da gyaran jiki da kud'in k'awaye duka."Abban murmushi ya saki ya ce "Hisham kenan, wato duk ta yarda ka b'ullo masa sai ya baka mamaki da nace ya bar kud'insa shine ya juyar da kud'in akan hidimarki, shi da kansa ya san hidimar da za
Ki yi ko kwatan kud'in nan ba su kai ba, shikkenan yanzu kam ba ni da ta cewa sai dai Allah ya saka da alheri, ke iyalinsa ce ba zan hana ya miki hidima ba, ki ciri dubu d'ari sun isheki yin duk abinda za kiyi ragowar sai a had'a a miki kayan d'aki. Shi kuma kwalin menene a ciki?" Cikin jin kunya Saudat ta ce ya ce "Kati ne a ciki." Da sauri saeed ya ja kwalin ya farke don d'iban nasa katin. Wani irin zare ido su ka yi gaba d'ayansu suna duban kud'in da suke zube a cikin kwalin. Y'an dubu ne bandir ashirin sabbi fil a ciki. Sa'eed ya ce "Miliyan biyu kenan cif idan ban yi kuskure ba, to su kuma na menene?" Ya zaro takardar da ya gani a jikinsu ya mik'awa Abba.
Abba Mustafa zubawa Sauda ido ya yi ya ce "Kika ce kati ne  a ciki? Bafa na son zubar da
kima da mutunci Sauda. ba kuma na son mutum ya raina inda Allah ya ajiyeshi." Sauda ta yi rau-rau da ido ta shiga rantsuwa "Wallahi Abba shi ya sanar da ni kati ne a ciki da ba san kud'i ne nima ba zan karb'o ba. ka kira shi ka tambayeshi ma ka ji."

Abba ya girgiza kai yana kallon Sa'eed ya ce "Ware takardar nan ka karanta min menene a ciki."

Sa'eed da k'arfi ya fara karantawa kamar haka:

Assalamu Alaikum Abba.

Dafatan ranka ba zai b'aci da wannan sak'o nawa ba, ba kud'inka bane kud'in sadakin Saudat ne. Na tabbata ba zai zama aibu ba tunda ubangiji bai iyakance yawan sadakin da mutum zai bawa matarsa ba. don haka don girman Allah kada kace komai ka saka mana albarka kawai a cikin auren.

                Nagode Hisham Hamza Maishadda.

Abba murmushi ya saki yana jinjina mamakin hali irin na Hisham da ya barranta da na iyayensa, ya dinga girgiza kai kafin ya ce "Allah kenan mai fitar da rayayye a cikin matacce, wato samun mutum mai hali irin na Hisham a cikin maza dubu sai an tona. Allah ya yiwa aurenku albarka ya sa ace gwara da aka yi ba zan mayar ba, Saudat sadakinki ne d'auki ki adana ke kika san me za ki yi da su." Umman Saudat na murmushi ta ce "Ka ji Abban Sauda da wani zance, yo mai za ta yi da su ban da a had'a
su cikin hidima abinda ake nema kenan kuma Allah ya kawo. Kayan d'aki kawai za'a gwangwaje ta da su na zamani. Gobe idan Allah ya kaimu sai a kira Sahura da Maryam ni kuma daga b'angarena na kira Faty k'anwata su je su siyo mata abinda ya dace." Ta fad'a tana dariya don ta yi farin ciki da kud'in nan ba d'an kad'an ba, don ko d'azu da Hisham yazo zancen yana son ya taimaka ta ji haushi da Abban Saudan ya ce masa baya buk'ata. Abba ya kalleta ya ce "Sam wannan ba huruminki bane ki barta ta yi magana da kanta. Ke Sauda ba ki ce komai ba." Saudat kanta na k'asa ta ce "Ni dai Abba da za'a bi shawarta a cancacana kud'in a rage miliyan d'aya a bawa Y.Sa'eed ya ja jari." Abba ya girgiza kai "Lalala, shikkenan shi kuma Hisham d'in sai ya d'aukemu k'ananan mutane ko? To ba za'ayi wannan da ni ba, tunda haka ne zan bi ta zancen Ummanki na siya miki duk abinda ya dace a zuba a d'aki da parlour da kitchen kawai."  Saudah bata sake magana ba, ganin Abban yana son ya d'au zafi. Ta ja bakinta ta tsuke. Ranar dai kam hankalin kowa a kwance ya kwanta a gidan an yi matsalar abinda ya tsaya musu suke kwana suke ta shi da shi.


____________________

Kashegari kuwa Inna Sahura da Inna Maryam da suke Uwa d'aya uba d'aya da Abban Saudat suka bayyana a gidan sai Faty k'anwar Umman Saudat suka bayyana a gidan, da yake tun a daren jiyan Abban ya sanar musu. Suna zuwa ya damk'a musu kud'in. Inna Maryam ta ce "Na menene Yaya Mustafa?" Nan ya sanar da su duk yarda suka yi da Hisham.
Inna Maryam ta ce "Yaron kirki kenan, ai Hisham ya haifu d'an albarka, ai Hamza kai ya haifawa d'a Mustafa don gaba d'aya halayenka ya d'ebe sanda kake da arziki haka ka dinga d'awainiya da dangi amma ji yanzu da kake cikin yanayin talauci kowa ya juya maka baya. Ni ban san ma za'a yi haka dama nan tafe nake da kud'i na miliyan guda nace a siya mata gado da kujera saiti d'add'aya sai a had'a gaba d'aya ai siya mata masu kyau y'an waje. Su kuma yaran wajena dama na ce su siya mata electronics daga na falo har na kitchen Insha Allah yarda suke so ka kunyata Allah ba zai kunyataka ba Mustafa." Sosai Abba ya shiga mata godiya har da hawayen farin ciki d'an uwa kenan mai dad'i. Inna Maryam tana girgiza kai ta ce  "Kayya Yaya Mustafa bar min godiya, sanda kake da shi wace irin moriyace ban maka ba, ai dole nima na tashi tsaye na ga ka fita kunya. Yanzu bari mu tashi da azama mu je mu fita kasuwar." Gaba d'aya suka mik'e UMMA ta bi su har zaure tana sake jaddada godiyarta.



Jikar  Nashe ❤️❤️✍🏽

08033748387

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now