35

121 9 0
                                    

Zumuncin Zamani...

Na

Nazeeafah Sabo Nashe.

08033748387.

____________________

Bayan fitar su Fareeda, Hisham Ya mayar da kallonsa kan Usman yana sakin ajiyar zuciya. "Usman taimako na zaka yi, don Allah wallahi Sauda nake son gani ka je ka 'd'auko min ita Sam bana jin daidai kwana uku ban gan ta ba fa." Usman yana dariya Ya ce "Idan yaso ta zo ta sake saka ni wahalar ciccib'arka zuwa toilet wanka ko? Har yau hannuna bai daina ciwo ba haka kawai a gadon asibiti don masifa ka jawowa kanka wankan tsarki, wai ma duk ba wannan ba ranar da ban zo ba ya za'a yi ka yi wankan? Kai ba k'afa ba." Hisham ya zabga tsaki "Gori zaka min mara mutunci, baka san zafin so bane don har yanzu haka 'dan'dana soyayya ba tunda auren ha'di aka muku da matarka. Ka bari sai ka samo wacce kake so zan baka amsa, yanzu dai ka taimaka min ka je kace mata don Allah ta yi hak'uri ta zo na gan ta, na san kishi ne ke damunta na rasa yarda zan yi da kishin Sauda." Usman ya harareshi "Yanzu nufinka na barka kai ka'dai kenan?" Ya 'daga masa gira kawai don ya lura jan magana Usman 'din yake so.

A k'ofar layin su Usman 'din ya yi parking ya samu wani yaro ya tambayeshi gidan su Sauda 'din.

Har k'ofar gida yaron ya raka shi. Usman 'din ya dinga bin gidan da kallo yana mamakin zamantowarsa wai na K'anin mahaifin Hisham Wanda yake auren 'yar sa, alhali Ya San Hisham 'din yana da gidaje to me zai jawo Ya hana surikin sa? Ya kalli yaron da Ya rakoshi Ya ce "Ka tabbata nan ne?" Yaron ya 'daga kai "Nan ne ba gidan su Sauda ka ce ba, Babanta da wanta suna jan adaidaita sahu." Rasa mai zai ce da yaron Ya yi kawai ya 'daga masa kai don shi sam ba shi da masaniyar Sana'ar da suke yi.

Daidai lokacin Abba Mustafa ya yi parking a k'ofar gidan da Adaidaita sahunsa. Ya dinga bin Usman da kallo ganin bai shaida shi ba. Usman ya durk'usa har k'asa yana gaisheshi. "Yaro ban waye da kai ba?" Abba Mustafa ya fa'da yana kallon Usman 'din.

Usman ya gya'da kai "Ba zaka gane ni ba, ku San ma in ce wannan 'din shine ha'duwarmu ta farko, ni abokin Hisham ne. Sak'o ya bani na kawowa Saudatu."

"To To, yana dai samun sauk'i ko? Sai zuwa yamma nake son sake komawa."

Usman ya ce "Da sauk'i Alhamdlllah."

Abban ya gya'da kai "Ma sha Allah, haka ake so bari na turo maka Sauda 'din." Ya fa'da yana saka kansa cikin gida.

Usman ya sake bin kwatocin da suke layin yana Allah wadarai da tarin arziki irin na ahalin Mai shadda  da suka yi burus da wannan bawan Allah, ko mai kuwa ya musu a ganinsa hakan bai dace ba.

Saudat ta fito sunk'uf cikin Hijabi Har k'asa bayan ta samu sak'on Hisham da ta turo mata a waya.

"Na aiko abokina wajenki, idan za ki fita ki saka hijabi Har k'asa kin ji na gaya miki."

Usman yana murmushi Ya tareta "Ranki Ya da'de Gimbiyar Hisham, kin hana abokina sukuni."
Ta sunkuyar da kanta ha'de da cewa "Ina yini" tana murmushi.

Ya amsa yana fa'din "Gaskiya koma meye laifin abokina Ya kamata a masa afuwa haka, Ya jigata da yawa, madadin ciwo ya ragu kullum k'aruwa yake. A yi hak'uri don Allah."

Ta saki murmushi, murmushin da ace Hisham yana nan sai ya kusa mutuwa da bak'in ciki saboda kishi ta ce "Bakomai, kace masa komai ya wuce, kuma In sha Allah zan zo."
Yana murmushi ya ce "Yauwa ko ke fa, to ga shi in ji mai gidan."
Ya fa'da yana mik'a mata wani envelope da Babu tantama ta San ku'di ne a ciki. Hannu biyu ta saka ta karb'a tana masa godiya.

Usman ya juya ya tafi a zuciyarsa yana ayyana dole Hisham ya mace a kan yarinyar nan, kunyar ta ka'dai abin burgewa ce."

Ko da ta shiga gida b'oye ku'din ta yi bata nunawa iyayenta ba, don bata manta kashedin Abbanta akan ba zai sake cin kwanon Hisham ba ko yunwa zata kashe shi.

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now