21

112 7 0
                                    

Zumuncin Zamani..

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

Wattpad
@Nazeefah381

Daga k'ungiyar Elegant Online Writers.

_______________

Ranar da za'a kai kayan lefen, gidansu Hisham a cike yake dank'am da jama'a, dangi cike kowa ya hallara tamkar gidan biki kai kace ranar ake auren, ba mamaki don ganin gidan Senator za'a kai kayan shi yasa kowa ya zo don an san za'a samu tarba mai kyau da kuma tukwuici, don haka kowa baya son a ce an barshi a baya.

Hajiya Laraba ta fito falon cikin wata shiga ta alfarma sai taku take d'aid'aya cike da izza da ginshira take musu kallon sama da k'asa. Cikin murya mai nuna zallar tak'ama ta ce "Lallai ba shakka gida ya d'au jama'a, to amma fa da sake don dole a tantance masu tafiya gidan senator da kuma masu tafiya gidan Mustafa."

Gaba d'aya gurin ya hau tsine da hayaniya kowa a fili ya nuna zilamarsa ta son zuwa gidan Senator. Muryoyi ne kawai ke tashi da gunaguni "Aa Wallahi gidan Senator za mu, ni don haka ma na fito sai dai idan an dawo daga gidan Senatorn wanda ya dubi Allah ya dubi zumunci ya je gidan Mustafa fisabilillahi fa, ke ma Hajiya zance ki ke wa zai hak'ura da zuwa gidan da za'a dagargaji kaji ya tafi gidan da ba mamaki cincin da cofe za'a bayar." D'aya daga cikin y'an uwanta ta fad'a, ai kuwa kowa kamar jira yake suka bata goyon bayan zancenta d'ari bisa d'ari.

Inna Falmata ma murmushi ta saki, ta ce "Ai na san za'a rina an saci zanin mahaukaciya sai ki kira Hisham ya kawo lefen y'ar gidan Mustafan idan muka dawo mu ma yi shahada ko mu biyar ne mu mik'a, ko bakomai ka samu ladan zumunci don dai ba abinda za mu tsinto a gidan Mustafa suna ta kansu."

Hajiya Laraba ta d'aga waya ta kira shi. Bugu uku ya d'aga wayar don yana bayan gidan kuma duk wata tattaunawa da suke a kunnensa suke yinta, ransa a b'ace cizar lab'b'a kawai yake yi. Sai da ya bari ta gama sanar da shi sannan ya ja hucin numfashi shima ya gaya mata abinda ya girgiza zuciyarta don direct ya ce "Ai lefe ya dad'e a gidansu Saudat na hutar da kowa ba sai an je ba, su je inda suke da tukuici mai kyau..." cikin dukan zuciya Hajiya Laraba ta ce "Ka yi me ne? Kai ne ka kai lefen da kanka saboda  a garin gab'a gab'a ake? Ba fa na son k'arya ko dai kud'in suka buk'aci ka basu?"
Cikin b'acin rai ya ce "Ko d'aya Mommy na ga dai hakan shi yafi cancanta."

Kafin ya sake cewa komai ta danne makashin wayar cikin b'acin rai ta kawar da wayar a kunnenta, kada dai zancen Falmata ya tabbata da gaske an shanye mata d'a tunanin da ta dinga yi kenan, kafin ta kalli Falmata ta ce "Kin ji yaron nan wai ya kai musu lefen tun d'azu" Falmata ta d'an zare ido ta ce "To Allah ya kyauta, amma menene abin b'oyewar?" Cike da takaici Balaraba ta ce "Zai wuce dukiya ya narka musu baya son a gani, kai ni wannan wace irin k'addara ce ta auren y'ar nan?" Caraf k'anwar Laraban ta ce "Kwantar da hankalinki Yaya, ai ya yi a banza za muje har gidan mu ga abinda ya sa ya k'i ya kawo mana lefen idan kuwa dukiya ya narka mata tsaf za mu rago su mu dawo miki da su."

_____________________

K'arfe biyar daidai na yamma masu kai lefen suka bayyana a tanfatsetsen filin gidan Sule Jami'i, haka aka dinga d'iban kayan ana shiga da su, su kuma suna tururuwar shiga babban falon na gidan. Dama dai an ce gaba da gabanta tuni kallo ya koma sama. Haka suka cika falon nan taf.

Hajiya Sa'ar na zaune a hakimce saman Babbar kujera, gefe da gefenta kuwa manyan Aminanta da suke take mata kaya sun sha adon gwalgwalai a jikinsu da laces masu uban kud'i. D'ayar kujerar kuwa Yayyan Alh.Sulen ne su biyu suma a hakimce cikin tasu shigar su kenan masu karb'ar lefen, amma su sun yi uban gayya. Tsaf Hajiya Sa'a ta dinga musu kallon d'aya bayan d'aya tana nazarinsu a tak'aice. D'aid'aiku ne a cikinsu ta san sun kai daidai yarda take son surukan yarinyarta su kasance irin su Hajiya Falmata, sauran kuwa duk daga yanayin surutun da suke jikinsu ta tantance a level d'in da zata ajiye su. Ta yamutsa fuska tana mamakin irin ayarin da suka yiyo wai kawo lefe a zuciyarta ta dinga ayyana masu shegen son abin duniya, dubi haukan da suka yi wai kawo kayan lefe kawai da sannu duk zan yi maganinku.

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now