18

112 6 0
                                    

Zumuncin Zamani

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

Not edited.

(Jazakillah Fad'ima Sabi'u Dankaka da ki ka yi jumurin typing book one Allah ya saka miki da mafificiyar aljanna ya alabarkaci rayuwar aurenki da tarin zuri'a masu alfanu.)

Mamaki ya kama Abba ya dubi Baffa Ya ce "Dama tare ku ke?" Baffa ya d'aga kai "Wallahi tare muke takanas ya je ya d'auko I mun zo gyaran zumuncin Allah." Umma tana masa sannu da zuwa kuwa ta juya ta d'auko musu ruwan randa mai sanyi, wanda pure water ne aka saka shi a randar. Abba ya mik'a musu ruwan. "Baffa ka sha ruwa kun d'auko hanya." "Bar ruwan nan Ka ji abinda yake tafe da ni ya fi shan ruwan." Abba ya girgiza kai "koma menene Baffa ka yi hak'uri ka sha ruwan za'a san Abin yi."
Baffa ya girgiza kai yace shi kenan ba a kin ta mutum ba ni ruwan na sha, umma ce ta dawo dauke da ruwa a kwanon sha ta ajiye masa ruwan sannan ta sake gaishe shi tana tambayar iInna Habi da Yara, "Duk suna lafiya" baffa ya amsa mata sannan ya dau kwanon ruwan ya kai bakinsa ya sha, ya ajiye ya dubi Abba mustapha yace ina jin ka mustapha,me yasa ka hana wannan yaron dan albarka auren yar wajen ka?"

Nan da nan Abba mustapha ya shiga zayyana wa baffa abubuwan da suke faruwa kafin ya gama baffa fuskarsa ta yi murtuk ya hau girgiza kai yana fadin, hukumullah la,ajaban. Sam banji dadi ba tabbas zuminci ya yi karanci,yanzu a dangin nan ace don Allah ya jarrabe kada rashin sai kowa ya juya maka baya har a dunga gudun hada zuri,a da kai? Ba komaii mustapha ka godewa Allah ya bakar ka da lafiya abin da nake so da kai ka dubi girman Allah ka kai zuciyar ka nesa,ita rayuwa duniya da kake ganin ta ba komai a cikinta sai rudani Kuma idan zaka yi abu kayi don Allah kada ka taba yin abu don mutane, don girman zatin Allah kayi hakuri ka ba Hisham auren yar nan don sadar da zuminci,ka san annabi ya umarce mu da sada shi Allah yana fushi da mai yanke shi. Ka dubi girman Allah ka bashi tunda dai shi ka tabbatar ba shi da wani Hali da za a guji hada aure da shi da fatan zaka yimin wannan alfarmar ka san dai ban taba Neman alfarma a gurinka ba.

Abba mustapha ya yi kasa da kai yace baffa ka daina roko na na amince na ba shi auren saudat, Allah ubangiji ya sa hakan shine mafi alkairi.
Cikin farin cikin baffa yace to na gode mustapha lallai na amince yau uba ka dauke ni ashe kuma bayan gobarar nan nan aka dawo.
Abba yace wallahi kuwa baffa,naso zuwa na gaya maka to Al,amura ne sai a hankali,rasa mafita na yi na sayar da nawa gidan,na sai adaidaita sahu biyu, sa'eed na jan daya ni kuma ina jan daya.
Baffa cikin matukar tausayawa ya girgiza kai yace humullah la,ajaban to ubangiji Allah yasa hakan shine mafi alkairi kayi hakuri mustapha wannan abin duk mai wucewa ne wata rana sai labari
Abba mustapha yace haka ne sanan ya kalli Hisham yace to Hisham,hankalinka sai ya kwanta na amince maka auren sauda
Hisham ya sunkuyar da kai yana murmushi
Daidai lokacin sauda ta shigo gidan dawowarta daga makaranta magariba kenan, durkusawa ta yi sosai ta gaida baffa cikin murmushi yace amaryar Kenna
Bata kawo komai a ranta ba ta shige daki Tun da safe da ta tashi ta yi wanke_wanke gabanta yake faduwa sosai, ta rasa dalilin,har ta gama wanke _ wanken kafin ummanta ta dan dube ta tace sauda sana,a nake so na fara amman na rasa me zan dunga sayarwa
Sauda ta dan yi jim kafin tace duk layin nan umma babu mai awara da safe ina ga ita za ki dinga yi,
Umma ta daga Kai tace haka ne, ke ma kin ce wani abu bari abbanku ya dawo na sanar dashi idan ya amince shi kenan sai na fara don gashi bikinki ya matso tunda sunce jibi xaa kawo kudin aure.
Da sauri sauda ta dago kai tace biki kuma umma.

Umma ta dan saki fuska tace to ya zaayi sauda kana taka ne Allah yana yasa abbanki ya amince wa Hisham aurenki saboda takanas ya dauko baffan wudil,kuma ba komai yaron nan Hisham ya cancani a bashi aurenki don ya yi mana halacci,ke kanki kin sani sai dai ki bawa wani labari don haka don Allah kada ki sa komai a ranki ki yi addaua Allah yasa hakan ya zamo alkairii a rayuwarki...
Turus sauda tayi,hawaye male_male a fuskarta yanzu shi kenan ta tabbata Hisham zata aura? Ta sani shi kenan tayi sallama da farin ciki a rayuwarta matukar ta shiga cikin danginsu inda ba a son su ba a san darajar da kimarsu ba.

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now