39

126 9 0
                                    

Zumuncin Zamani

Na

Nazeefah Sabo Nashe

Book 3

Pg 2.


A hankali ta mur'da k'ofar da zata sada ta da toilet 'din "Wow" ta furta bayan cin karo da ha'dadden toilet 'din wanda ya Ke mallakinta ne, Babba ne na gaske da Ya sha adon black da ratsin ash ka'dan, Hatta da tiles 'din black ne. Cikin farin ciki ta shiga cikin jacuzzi 'din ya fara wanka.

Tas ta shirya cikin wata simple wear da ta tsaya mata iya idon sahu, ga shi ta 'dafe mata tsam a jikinta kamar tare aka haliccesu. Ba k'aramin kyau ta yi ba duk da ba kwalliya ta yi ba ko kwalli babu a idanunta sai wet lip da ta saka 'dan ka'dan shima, ta kuma yi brushing gashin girarta. Wasu irin turaruka na companyn Oud ta feshe kowane lungu na jikinta da su. Sannan ta kama gashin kanta ta 'd'aure da banda red colour 'din rigar.

K'arar akwai alamar bak'i ce a k'ofa ta farkar da ita daga 'dan barcin da ta fisgeta, ta mik'e a nutse ta fice don bu'de ainahin main door 'din ta shigo.

Tana bu'dewa ta ga Hisham a bakin k'ofa, da kaya nik'i-nik'i a hannunsa, bata masa magana ba ta juya da sauri shima ya bi bayanta yana shak'ar sassanyan k'amshin turaren da yake fisgar sa da wani al'amari daban.

Sam bata San yana bayanta ba don haka tana shiga 'd'aki ta yi hulli da hijabin jikinta gaba 'daya surarta ta bayyana Ya bi ta da kallo yana mamakin sake cikarta a lokacin k'ank'ani duk wata halittata ta mik'e sosai. Ya dinga jin wani magana'disu yana fisgar sa Har bai San sanda ya fisgota jikinsa ba kamar wani mayinwacin zaki haka ya fara sunsunarta. Haka lamarin ya fara tafiya ji da ganinsu ya 'd'auke 'dif kamar wutar nefa...................

____________________

Umman Sauda hankalinta ya fara tashi, musamman ganin har la'asar Saudan bata dawo ba. A da bata kawo komai a ranta ba don ta ayyana ko karatun exams ta tsaya yi. Sai dai ganin magriba ta gabato sai hankalinta ya fara ta shi ga shi ta kira wayarta ta jita a cikin 'dakinta alamar bata tafi da ita ba.

Shigowar Sa'ad da Abban Sauda ne ya sata sakin ajiyar zuciya, da sauri ta bawa Abban Ruwa kafin ta sanar masa rashin dawowar Saudan.

"Malam Sauda fa bata dawo gidan nan ba tun fitar ta makaranta."

Abba Mustafa fuskarsa a 'dan gintse ya dubeta don Har a lokacin Fushi yake da ita ba wai ya gama huce wa da ita bane. Ya ce "Sa'ad mu je makarantar ta su." Suka juya suka fice suka bar Umman cike da jima min rashin Saudan.

Bincike iya bincike a makarantar Babu Sauda ba labarinta, ga shi an sanar musu ma an yi yajin aiki. Don haka jiki a salub'e suka dawo gida da mamakin Ina Saudatun zata shige?

Sai dai suna dawowa gida amsar tambayrsu ta samu don a tsaye suka tarar da 'd'an Aiken Hisham yana shirin turawa gidan a kira masa wani don ya isar da sak'on da ubangidansa ya ba shi.

Abba Mustafa ya dakatar da yaron da fa'din "Barshi ba sai ka wahalar da kanka ba ga ahalin gidan sun dawo." Ya fa'da yana mik'awa bak'on hannu. Suka gaisa a mutunce kafin bak'on Ya mik'a masa envelope mai 'd'auke da sak'on Hisham a ciki. Abba Mustafa ya karb'a yana furta daga Ina?"

"Yallab'ai Hisham ne ya aiko ni." Abba ya girgiza kai yana sakin ajiyar zuciya ga zatonsa takardar shaidar sakin Sauda ce  gabansa Ya dinga fa'duwa don da alamu hasashensa na Sauda tana tare da Hisham ba zai tabbata ba tunda ga shi ta cika alk'awarin sa ya kawo masa takardar saki. Ya masa sallama ya shiga gida.

Yana shiga Umman ta mik'e da sauri tana fa'din "Allah yasa an dace, don wallahi hankalina a tashe yake sosai."

Jiki a mace ya zauna yana furta "Ba a dace ba idan ma gudun ta yi ai ke ce kika ja, ga alamu Sun nuna ba mamaki ba wajen mijin nata ta tafi ba kamar yarda nake hasashe."

Zumuncin ZamaniWhere stories live. Discover now