ANYI GUDUN GARA PAGE 1

1K 52 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞🙆‍♀️

*NA*
*AISHA GALADIMA*

*DEDICATED TO*
*HASSAN ATK*

*Tukuici*
Ga
*BATUL ADAM JATTAKO*
*HAJ MARYAM SAKATARIYA*

Bissimillahi Rahamani raheem


*PG 1*

zaune take a cikin dakin nasu Tana shafa powder a kyakyawar fuskar ta bayan ta kammala ta dauki lipstick ta shafa a madaidaitan labbanta ta dauko turarenta meena me sayyayan kamshi ta shafa daga nan ta kara kallon madubi tana ma kanta murmushi se ta Mike tsaye ta nufi wardrobe din kayanta ta fiddo gogaggun uniform dinta ta saka kalar purple and white daga can waje naji wata murya ta na fadar "Amal mun fa yi latti ki fito mu tafi ko na wucewa ta dan bazaki sani shan na jaki ba,

Shiru tayi bata amsa ta ba har se da ta dago labulen dakin Tana kallonta tace " Amal mun fa yi latti ki fito mu tafi" .

Ta shi tayi ta dauko Jakarta tana murmushi Tana "yi hakuri Ramla ai na shirya yau da wuri zamuje ko?"

fitowa sukayi gwanin sha'awa duk da uniform din nasu ya tsufa amma saboda kula da wanki da guga da suke sha farat daya baza ka ce tsoffin kaya bane suna fitowa suka nufi wani madaidaicin kitchen wata matsakaiciyar mace zaune akan kujera tsuggune tana suyar kosai ga bokitin kunu a gefenta duk'awa sukayi suna fadar "umma ina kwana"

tace "lafiya lau har kun shirya?

Suka ce eh tazuba ma kowa kunun a karamin kofi da kosai a plate ta Mika musu

Da sauri sauri suka gama suka wuce saboda har takwas ta wuce

Suna tafe suna tunanin haduwarsu da malam bala

Har suka isa bakin makarantar suna sauri suna shiga kuwa suka tarar da shi rike da bulala me baki biyu a hannu

Tuni Amal ta fara fidda kwallah!!!

*IN NAGA RUWAN COMMENT INCI GABA*

*DAGA AL 'KALAMIN AISHA GALADIMA*

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now