ANYI GUDUN GARA 57-58

350 26 1
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*
_
*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)

'''Nayi typing me tsawo ya goge,naso na Bari se gobe nayi wani,ammah saboda damuwar da kuka nuna fans yasa nayi wannan Dan jin dadinku

*PG 57-58*

________________________________'''

Bude marfin motar yayi ya  fito, tunkarar su yayi duk da akwai tazara a tsakanin su ,ita Amal Bata hango sa ba Amma shi gayen ya hango sa, ammah be Taba tunanin wurin su ze zo ba,se zuba yake kamar kanya 🤣

Cewa yake "Yanzu baby kamarki Zaki ce min kinyi aure ,ai bazan yarda ba ki kalli kanki yadda kika hadun Nan komai yah.... Ai be karasa ba se saukar Mari yaji,kafin ya tantance yaji naushi a hancinsa ,Amal ai mutuwar tsaye tayi na ganinsa , dukan sa yake ta ko'ina baji ba gani da sauri driver da ya kawo sa ya karaso Yana fadar"sorry sir"

Tuni cikin Amal ya duri ruwa,hankalinta ya tashi da irin dukan da ta ga Yana masa
Allah ne ya jefo Yaya Sadiq da sauri yazo da kyar ya kwaci saurayin Nan a hannun farouk

Aiko hancinsa jini kawai yake fitarwa duk ya fita hayyacinsa kamar ba shine dazu tsaye ba cikin kamalarsa

Ai tunda Amal taga Yaya Sadiq ya karbi saurayin da sauri ta fada cikin gidan gabanta na faduwa ,duk da tabar tsoron farouk din a yanzu ba karamin tsoro ya bata ba

Da kyar Yaya Sadiq ya taimaka ma saurayin Nan ya wanke fuskarsa da har ta kumbura ,se sannu ya ke masa Yana basa hakuri

Farouk har yanzu zuciyar sa tafasa take ,bayan Yaya Sadiq ya karbi saurayin Nan, juyowa yayi inda take tsaye yaga babu ta,ya tabbatar da cikin gidan ta shiga  har ya bude gate din gidan yaji hayaniyar mutane dawo wa yayi Yana tsaki Dan ya manta da biki ma ake

Yaya Sadiq ne ya dafa kafadar sa yana cewa"Farouk Dan Allah kayi hakuri ,Ni nasan wanna abun da ya faru akwai rashin fahimta ,Dan ban taba ganin Amal tana magana da wani ba,to yau din ma nasan ba'abunda kake tunani bane "

Shi dai farouk jinsa kawai yake ,se dai ya Dan saki jikinsa ganin yadda sadiq din ya damu
Murmushin yake yayi yace "ya wuce"

Murmushi yayi ya Sara masa irin na girmamawa da ake ma soja ,shima murmushin ya mayar masa,kafin yace muje ciki

Bin bayan sa yayi suka shiga Nan cikin gate din an shimfida carpet a Nan ya ce ya zauna Bari yaje ciki ya turo Amal din

Yana shiga ciki ya Kira Amal ,Tana ganin yaya Sadiq ta fara sunkuyar da Kai a hankali ta karaso kusa da shi

Hararta yake har ta karaso kafin yace "kin kyauta abunda kika yi,kina matar aure har zaki tsaya kina magana da wani a waje ko?

Murya na rawa tace"ba haka bane Yaya Sadiq"

Rufe min Baki,Kuma har su Abbah se na fada ma abunda kikayi

Kuka ta fara Tana rokonsa Akan Dan Allah kar ya fada ma su Abbah

Tausayi Kuma yaji ta basa ,se yace "wuce ki dauki ruwa da Abinci ki Kai masa Yana filin gate inda muka zauna dazu

Hawayen fuskar ta ta goge tace "to"

Ciki ta koma ta dauko hijabin sallar Aunty Ramla ta sako har kasa yake Kai Mata,sannan ta shiga kitchen ta dauki Ruwa da lemu ta fito waje tazo fitowa gabanta na faduwa

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now