ANYI GUDUN GARA 9-10

293 17 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️

     *NA*
  *AISHA GALADIMA*

*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*





_Muna sayar da  Dubai gowns, laces ,shoes, bags and kitchen utensils_
_Ga masu bukata zaku iya tuntubar wannan number_ (08064933819)




*PG 9-10*

________________________________________
   

Umman su husna da isowar su kenan a wurin ta saki salati Tana kallon Amal da ke zube a kasa, da sauri  ta Kara sa ta dago ta su Abba duk tsaye sukayi suna mamakin me ya faru

Kawu lawan ne ya juya yana kallon Sadiq da yayi tsaye yana kallon umma yace "Kai Abubakar me ya faru ne?"

"Abba nima ban sani ba ta na ganina Naga ta fara kuka se kuma ta fadi"
Sadiq ya fada

Ruwan da husna ta kawo ne umman su ta karba ta shafa mata a fuska ,sannan fa ta sauke wata irin Ajiyar zuciya Tana bude idonta a hankali, se  da ta fara bin mutanen dake zagaye da ita da kallo daya bayan daya ta na zuwa kansa ta saki wata Kara!  ta boye fuskarta a jikin ummah Tana cewa"ummah Dan Allah kuce ya fita ,se kuka take!

Kawu lawan ne ya dubi Sadiq yace "kaje dakin zaure abincinka na can"

Juyawa kawai yayi al'amarin duk ya daure masa Kai dagata umman su husna tayi sukayi cikin gida ,su Ramla da husna na biye da su ,dama ita umma tuni ta wucewarta Tana me jin haushin abunda Amal din ta aikata.

Daki ta shigar da ita ta ce mata "kwanta ki futa kinji"
Daga mata Kai, kawai  tayi

Ita ma fita tayi ta shiga dakin ummah

Kawu lawan ne ya ja Abba da jikinsa yayi sanyi suka fita kofar gida suka zauna kan dakali
Ya kalli Abba yace "Isma'il Wai me ke damun Amal ne ko wata rashin lafiya ta same ta ba muda labari?"

Shiru Abba yayi sannan fa ya shiga bama kawu lawan halin da husna ke shiga duk taga Dan sanda ko masu wani kaki da suke rike bindiga

Abun ya girgiza kawu lawan sosai
Ya jima yana nazari sannan yace" Ai ko akwai matsala in har haka ne ,dole alkawarin Dana yi na warware shi na zancen aurenta da Abubakar ,Dan wannan in muka takura zata iya rasa ranta ma in har ta aure sa, tunda yanzu ma da ganin sa kawai tayi har da Suma fa tayi"

Abba yace"yaya ayi haka kuwa tunda kasan Sadiq fa yasan da maganar nan"

Kawu lawan yace "ai wannan me sauki ne ban son abunda za muyi muzo mu bata zumunci mu"

Shi dai Abba duk jikinsa yayi sanyi akan wannan lamari

Umman su husna ma se da ta tambayi umma meke damun Amal nan ta fada mata duk abunda ke faruwa shiru tayi ta kasa cew komai..
________________________________________

Yana dinning yana breakfast Kiran Khalil ya shigo wayar sa  dauka yayi ya Kara a kunne daga can Khalil yace " hello kana Ina gani a kofar gidan ka Amma a rufe"

"Eh bani jaji Ina gida , kamar kasan nemanka nake kuwa"
Cewar Sadiq

Daga can Khalil yace"Allah ya sa ta samu ne, yanzu da na shirya Zan zo gidan"

"Ok seka zo"
Ya sauke wayar a kunnen sa ci gaba da latsa wayarsa

Befi 30 minutes ba se ga shi ya shigo gidan , hango sa da yayi ne yasa ya tashi daga kan dinning ya ja hannun sa suka fita zuwa  wani wurin shan iska dake gidan ,anyi masa irin bukkar nan da ake yi an zagaye suka ne mi kujeru suka zauna

Tun lokacin da ya jawo hannun khaleel , khaleel din ke ta kallon sa da mamaki yadda ya jawo sa kamar wani yaro

se da suka zauna kuma yayi shiru ,se da khaleel ya ji shirun yayi yawa se ya kama hannun sa cikin nasa yace. " Captain Wai lafiya kake ko wani Abu ya faru ne?"

Ajiyar zuciya ya sauke!
Sannan ya bude Baki A hankali ya fara fadar" Baka yi mamakin ganin ban kwana barrack ba , jiya Abba ya kirani yace na same sa a gida, bayan nazo ne yake min zancan aure fa, ya wani zare idon sa akan khaleel , kuma Kai kafi kowa sannin ban kawo aure a raina ba yanzu, gashi ni har yanzu bani da wata budurwa da  Zan nuna wadda nake so ,sannan idan har nayi wasa Abba me iya zuwa ne can zamfara cikin dangin sa ya laka min wata..

Shiru khaleel yayi na 'yan sakanni sannan yace maganar gaskiya fa farouk ya kama ta kayi aure fa shekarun 32 ace baka zancan aure , koni Dana ke 30 ai kasan dai bikina kwanannan za'a yi shi fa, sannan da kake Zan can baka da budurwa ai ko kana da su da yawa , gama Maryam cikkakiyar mace kamar yadda kake son matarka ta kasan ce ,ga ilimin boko Dana Islamiyya ga kuma kirar da Allah ya mata komai zam-zam kawai ka gabatar da ita , kuma Tana matukar sonka fa

Dan duka ya Kai masa a kafada Kai fa khaleel Dan iska ne fa ,har yaushe ka kalle ta kasan komai zam-zam ,

Yace "ai ko makaho ya ganta yasan ta isa mace "

Farouk yace"se dai ni tamin kadan ,yarinyar da iya karta 20years kake son hadani da ita, kawai kaja min Raini Allah ya kiyaye na aureta .

Ya fada yana ya mutsa fuskarsa

Sororo khaleel yayi da kansa yana masa kallon mamaki ,

Se yace "to ai shi kenan ka tsaya neman warinka se ka aura kaga ita ba zata Raina ka ba ko?"

Ni malam kaga tafiya ta ya Mike ya nufi wajan motar sa yana mamakin son girma Irin na abokin  na sa
Fatansa daya Allah yasa ya tsaya ruwan ido har Abban sa ya hada sa da duk wadda ya ga dama ya ga yadda zeyi......

_____________________________________'___

Koda Sadiq ya shiga dakin kayansa ya cire ya shiga bathroom ya yi wanka ya fito ,ya shirya cikin wani danyan voile sky blue da ya karbe sa sosai ko Dan yana farin namiji
Kamar Atk lol🤣

A cikin gida kuwa se la'asar Amal ta farko a baccin da ya dauke , bayi ta shiga tayo Alwala tayi sallah sannan ta fito
Tsakar gidan taga su umma zaune suna hirar su ,sunku yar da Kai tayi tace"umma Ina su husna?"

Hararar ta ummah tayi ta dauke kanta
Se umman su husna ce tace" sun shiga makwabta gidan su ko bilkisu kawar Ramla"

Koma wa tayi ta dauko hijab dinta ta sa tace "bari na bi bayan su "

Har Sadiq ya fito dakin ya hango ta zata shigo zauren komawa yayi cikin dakin seda tazo Dab da dakin taji an fizgota da karfi

Ta bude Baki zata yi kuwa taji an rufe bakin................  .......




*Aysha galadima ce*

Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now