ANYI GUDUN GARA 47-48

285 24 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*

'''Follow me on #wattpad @Ayshagaladima666'''



_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)

*Rayuwa ba tsere bace*, *kar ka taba damun kanka Akan se ka wuce wani*
*Duk Abunda Allah ya rubuta ma baza ka iya canza shi ba*


*PG47-48*

______________________________

Jin an turo kofar dakin cikin sauri ya maza ya zauna ya rungumota ya na fadar "menene ya shiga idon naki ?"

Ita dai Amal tuni ta saki Baki Tana kallonsa da mamaki fal a ranta
Gyaran murya kakus tayi Tana iyar da shigowa dakin Tana cewa "me ya shiga idon nata ne Naga fuskarta tayi shabe shabe da hawaye?"

Juyowa yayi yace
" nima haka na iskota tace min wai wani Abu ya fada Mata a ido"

Ita dai kakus kallon tuhuma take ta binsa da shi ,ganin irin kallon da take masa yasa ya waske yace "to kije kiyi wanka , ki wanke fuskar taki Kuma"

Ya tashi ya fita ,bayansa kakus tabi da kallo ,sannan ta shigo Tana kallon Amal din tace "ya Miki wani Abu ne"

Da sauri tace"A'a ba abunda yamin"

Tabe Baki tayi tace "to yayi ke kika sani Ni ki fito ki bani abinci ta juya ta fita , Amal tashi tayi a hankali ta dauki ledar pad din ta bude ta dau daya ta kimtsa kan ta ,Tana yi Tana tuna yadda  ya wani rungumeta Yana shirya zance, lallai mutumin Nan Dan duniya ne, Kiran da kakus ta Mata ne yasa ta fita da sauri

Har yanzu suna falon harshi ,kitchen ta wuce ta fito da kulolin abincin ta Dora kan dinning seda ta gama jera komai sannan tazo wurin kakus tace
" ga abincin can na shirya"

sannu ta mata ta tashi suka nufi dinning ga mamakin Amal harshi biyo su yayi dinning din ,shi Kuma yayi haka ne Dan kar kakus ta zargi wani Abu ,yasan tsab zata fada ma Abbansa ,Abincin ta fara zuba ma kakus,white rice ce da miyar dage dage data ji kaji se salad da ta yanka  bayan ta zuba Mata ne

shima ta zuba masa ba sosai ba ta tura gabansa,a yadda yake ganin abincin da Kuma kamshin da ya cika masa hanci ransa ya biya sosai Yana Kuma fatan yasa yayi dadi

Kakus ce tace"ke Amali Kara masa abincin wannan Dan tsiton abincin Zaki ba mijinki ?"

"To Wai ke me ya dame ki da matata ne har kike wani Bata Mata suna"
Cewar farouk

Amal ji tayi abun wani banbarakwai Ammah a yadda yama kakus maganar se taji ya burge ta🤣

Kakus tace
" nayi maganar har wani zaka nuna ma Mata bayan se da aka gaji aka ma auren tazuru kawai"

shi dai abincinsa ya ci gaba da ci be kulata ba ,abincin ba Karamin dadi ya mai ba Nan yake cewa Ashe dai ta iya girki har ka dama

Nace to da ya ka dauke ta🤣

Kakus yini daya ta musu ya mayar da ita Amal ko sabbin kayan da ta gani a drawer da ba'a Dinka ba ta dau Atamfa daya da turare taba kakus ,Aiko kakus godiya Tai ta Mata har farouk se da ta nuna ma,shima yaji dadin hakan da tayi Kuma ta Kara kima a idonsa

______________________________

A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah yanzu har sunyi wata biyu da aure ,Aunty Ramla har an samu karuwa kasancewar cikin nata tun yana wata daya take ta laulayi tun basu gane ba har suka shirya suka je Asibiti Nan fa aka ce ciki ne da ita ,murna wurin yaya Sadiq ba'a magana ai ko ba kunya ya Kira gidansu ya fada,ita Ramla kunya tai ta ji ,shi Kam ko a jikinsa ,yau suna shiri ne zasu je kaduna ta gano gida da Kuma Amal

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now