ANYI GUDUN GARA 25-26

262 19 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)

*PG 25-26*

________________________________

Nan dai suka yi sallama da Ramla har ya karbi number wayarta , ta shiga gida inda ta tarar da Amal ta nade kafafu Tana cin Abinci ,harara ta dalla Mata ,ai ko se ta kyalkyace da dariya ita dai Ramla dakin ummah ta shiga ta nunnuna Mata kayan da suka sawo da kuma dinkunan da ta karbo

Ana saura kwana biyu su wuce  kwankiyal Abbah ya Kira Abbansu Farouk ya ke shaida masa bikin da kuma tafiyar da zasu yi

Abban su farouk nata jin dadin sanar masa da Abbah yayi nan yace masa anjima ze shigo Dan yana da muhimmiyar maganar da yake son suyi , nan dai suka yi sallama

_______________________________

A bangaren farouk kuwa yana cikin damuwa saboda gaba daya Abbah ya dauke masa wuta ,Dan haka a gaggauce wannan weekend din yayi shi ,ranar Sunday ya tattara kayan sa ya koma barrack ko Abbah be ma sallama ba

Ko da ya koma Kullum cikin Damuwa yake ,yau dai khaleel ya tasa shi a gaba akan se ya fada masa damuwar sa , nan dai ya fada masa yadda sukayi da Abba
Ajiyar zuciya khaleel ya sauke, sannan yace "Captain gaskiya duk laifinka ne tun yaushe Abba yake ma maganar aure Ammah kayi ko oho da maganar nan , sannan nayi biyar ka ka zabi cikin masu sonka kaki yanzu ya kake so ayi?"

Farouk ya kalli khaleel yace "wallahi nima ban San ya zanyi ba ni fa na fada ma bazan taba auren yarinyar da ita tace Tana so na ba , na fi son Naga wadda nake so da Kai na"

Sororo khaleel yayi yana kallon shi can yayi murmushi yace "to ai shi ke nan se ka shirya zuwa maradun ya ganmu se muje ka zaba"

Wani naushi ya kawo masa ya kauce
Nan khaleel ya ci gaba da dariyar sa se da ya gaji Dan kansa yace "to naji yanzu dai ka shirya gobe mu fara yawo cikin garin kaduna ko za'a da ce "

Tashi yayi ya barsa falon ya shige bedroom

Mi ze yi khaleel kuwa in ba dariya ba ,se da ya gaji Dan kansa ya tashi ya fita daga gidan

________________________________

Washe gari Abban su farouk ya je gidan su Amal  yau dai har cikin gida ya shiga , su ka shiga daki da shi da Abbah

Sun fi awa daya suna magana ban San Abunda suka tattauna ba , Abbah ya fito suka yi sallama ya tafi

Tun Asuba ummah ta tada yaran nata suka shirya Koda 7am tayi sun kama hanyar kwankiyal  koda 5pm na yamma  tayi sun isa kasancewar garin na da nisa sosai, ko da suka isa sallah kawai suka yi suka nemi dakunan gidan Kawu suka shige su Dan futa saboda gajiyar tafiya da suka kwaso

Abbah ko da suka iso ya nemi kawu da kuma yayansa lawal suka kebe sun dade suna magana Sannan suka fito Allah dai yasan abunda suka tattauna ,

naso shiga Esher maradun ta hana ni 🤣🤣

To haka dai Aka ci gaba da gudanar da shagulgulan biki
Su yaya sadiq sun Riga su Ramla zuwa kwankiyal danko da suka zo sun isko su

Ai ko dare nayi yaya Sadiq ya matsa akan Ramla ta fito yana son ya ganta ta rasa yadda zata yi ta fita waje ita dai

Se tace "Amal muje ki rakani waje "

Sun fito ke nan suka ganshi har Amal zata juya Ramla ta rike ta. Tace "muje ki gaisa da shi Mana"

Ranta be so ba tabi ta suna zuwa
Se da Ramla ta matsi Hanunta sannan da kyar tace "Ina wuni"

Se da ya kalle ta sannan yace "lafiya lau kanwata me tsorona "
Dan murmushi tayi tace "ai na Dena"

Yace "da ya fiki ai zamu ga karyar tsoro"

Da sauri Ramla tace "kamar ya yaya "

Ya wayance ya ce "ba komai "

ita dai Amal barin su tayi ta shige gida

Haka dai aka ci gaba da hidimar biki 'yan uwan ummah na gombe duk sunzo sunyo Mata Sha tara ta arziki.

can a gidan wata goggonsu dake wani Dan kauye da ake Kira gangalawai  aka sa Amarya Ramla lalle ,ranar ko Tasha kuka su Amal  da sauran dangi se tsokanar ta suke

Ita ko se kuka take gwanin tausayi

Rana bata karya yau dai ake daurin Aure karfe biyu aka sa saboda Baki masu zuwa ne sa

Na Sha mamaki Dana ga har da su khaleel da wasu abokan aikin su amma ba da farouk ba se Abbah da Al'amin

Can cikin taron daurin naji me sanarwa yana cewa An daura auren *Abubakar sadiq lawal da Amaryar sa Ramlatu Isma'il*

Dana kuma *Umar farouk  Bashir* *maradun*  
*da amaryarsa* *Amal Isma'il*
ai se na yarda Alkalamina.............✍️

*Aysha galadima ce*

Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now