ANYI GUDUN GARA 59-60

326 23 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)

*Dubun gaisuwa a gare ku*

*ANYI GUDUN GARA FANS GROUP*

*HOUSE OF NOVELS1*

*UMMU SAFWAN FANS GROUP*

*JATTAKO NOVELS GROUP 2*




*PG 59-60*

________________________________

Kiran sallar farko yasa farouk farkawa da ga bacci, tashi yayi ya nufi bathroom ya dauro Alwala ,farar jallabiyya ya dauko ya saka ,dadduma ya shimfida ya gabatar da Raka'atanil fijir, kafin ya fita zuwa masallaci ,har ze ficewar sa ya kuma dawo ya kwankwasa kofar dakinta, cikin bacci taji kamar ana kwankwasa kofa Jin shiru da yayi yasa yace "kin tashi"

Farkawa tayi taji da gaske ne kwankwasa ake Jin abunda aka ce yasa tace "Eh"

Wucewa yayi zuwa massalaci ,ita ma mikewa tayi ta shiga bathroom tayo alwala tayi sallah,bayan tayi sallah Bata koma bacci ba karatun Qur'ani tayi har zuwa 6:00am ta gama,tashi tayi ta gyara dakin duk da ba yada wani datti ,wanka ta shiga bayan ta fito ta shirya cikin wasu Riga da skirt na Atamfar Holland ,sun karbe ta sosai batayi wata kwalliya ba powder kawai ta shafa se lipstick data shafa

Gajiya tayi da zaman dakin Dan haka ta Mike ta nufi kofa,budewa tayi a hankali ta fito ,se dai tayi rashin sa'a Tana fitowa ta tarar da shi zaune a falon Yana kallon news din safe ,ba yadda ta iya ya Riga yaji motsinta, A hankali ta ida karasowa Dan nesa da shi ta duka tace "Yaya Ina kwana"

Kallonta yayi na wasu sakanni se ya ga ta mishi kyau sosai
Kafin ya dauke kansa ganin Tana Shirin dago kanta yace" lafiya Lau"

Shiru falon ya Kuma dauka kafin yace "ki shiga kitchen ki Mana breakfast,daga yanzu ke Zaki ci gaba da muna girki
Kasa daurewa tayi
Se da tace"Yaya zaka iya cin jagwalgwalo kuwa?"

Shiru yayi duk da yaji abunda tace Kuma ya San magana ce ta mayar masa

mamakin karfin halinta da har ta masa wannan tambayar yake, ya kula fa yanzu kan mage ya waye
Ganin ya share ta yasa ta tashi ta nufi kitchen bayanta yabi da kallo dama kayan sun ka Mata ,mamakin sauyawarta yake yaga Kaya ta ko'ina kallonta yake kamar wani maye har ta bace masa, Tana shiga ya sauke wata ajiyar zuciya

Nace to fa🤣

Ruwan tea kawai ta dafa se dankali da Kwai da ta soya ,saman dinning table ta jera abincin ,kamar jira ya ke dama yazo zauna,komawa tayi cikin kitchen din ta dauko plate da tea cups da sauran kayan shayin ta aje Akan table,zama tayi ita ma se dai duk ta tsargu da irin kallon da yake Mata

A hankali ta dauko cup ta hada tea din ,sannan ta dauko plate ta Zuba dankalin ,ta jawo gabanta ke Nan taga ya dauke tea din ya matso da plate din gabansa ya fara cin abun sa

Taji haushin abun Amma Bata da yadda zata yi wani ta sake hadawa ta fara sha a hankali

Ya Riga ta gamawa ,sannan ya juyo ya kalle ta yace"Naga alamar Baki iya komai na kula da miji ba har yanzu,kije ki koya"

Mikewa yayi be sake kallonta ba ya nufi dakinsa duk da daurewa kawai yake  yi amnah Yana bukatar Matarsa a kusa da shi

Haushin maganar da ya Mata tayi sosai,to Wai ma in Bata iya ba Ina ruwansa da ita ,ita fa Bata son takura

ANYI GUDUN GARADonde viven las historias. Descúbrelo ahora