ANYI GUDUN GARA 37-38

245 18 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)

*DOMIN JIN DADINKU*

Raleeyer
Ummu Afef
Fatima shehu
Aysha humaira
Leemat
Ummu sadiq
Maman sultan
Ummu Muhammad
Aysha zannah
Zahra MD

*PG 37-38*

________________________________

Sautin Takun na matsowa Tana Kara runtse idanun ta  se kuma taji kamar takun gaba yayi ba'a kofar dakin da take ciki aka nufo ba.

Shiru gidan ya kuma dauka tamkar babu wata hallitta a cikinsa

Ita ma Amal shirun da taji yasa ta tashi taje ta sama kofar key ta dawo ko kayan jikinta bata cire ba ta kwanta bayan ta shafa Addu'a a dukkanin jikinta, a yanzu ta Dan samu natsuwa sanin cewa akwai wani mahaluki a kusa da ita ,ita hakan da yayi ma shine dai dai a wajenta

Tuni bacci barawo ya  dauke ta

A bangaren farouk kuwa da kyar khaleel ma ya nemo sa bayan shawo kansa da yayi akan fushin da yake da shi ,duk se da ya fada masa shima be San komai ba

Nan yake Kara basa shawara akan yayi hakuri da zabin da iyayensa suka masa ya karbi wannan auren hannu bibbiyu Insha'Allah ze yi Alfahari da shi

Ya ci gaba da cewa
"Kuma kasan me captain? Yarinyar ba karya akwai kyau"

Wani kallo yake bin khaleel da shi yace

"Yanzu baka ji kunyar cewa yarinya ba, ai ni duk da bani da ra'ayin auren Mata biyu dole nayi wani auren gaskiya"

Kallon mamaki khaleel ke biyarsa da shi ,yana me tunanin wane irin tsatsauran ra'ayi Abokin nasa yake da shi, Dan shi in shine hakuri kawai ze yi a wuce wurin

Ajiyar zuciya khaleel ya sauke yace"what ever Ni dai yanzu kazo muje na kaika Ango"

Harara ya watsawa khaleel din

Yace "look captain ya kamata ma na Kira abokanmu a raka ka, kawai dai na kyale su ne Ni kadai ma na isa ka tashi muje

"Bazan je ba"

Amsar da ya bashi ke nan ,tashi ma yayi yaja motarsa ya barsa
Ba karamin takaici Abun ya ma khaleel ba.

Shiyasa kawai yazo ya dauki matarsa suka wuce , farouk kuwa yawon sa kawai ya ci gaba da yi a cikin motar
Sannan ya nufi gidan nasa yana me ayyana abubuwa da yawa a ransa

Yana shiga Kai tsaye dakin sa ya nufa ,wanka yayi ya kwanta gaba daya ma ko tunanin Amaryar tasa be yadda zuciyarsa ta bijiro masa da shi ba

Kiran sallar Asuba ne ya tada Amal daga bacci A hankali ta sauka akan gadon ta nufi bathroom  Alwala ta dauro ta fito ta gabatar da sallar Asubah bayan ta gama zama tayi akan daddumar tayi Azkar dinta daga nan wani baccin ya dauke ta

Shima farouk massalaci yaje bayan ya dawo Kuma ya nufi dakinsa

Misalin karfe takwas na safe aka fara kwankwasa kofar shigowa falo
Cikin bacci Amal taji ana kwankwasa kofar falon

A hankali ta tashi ta nufo falon jin ta inda ake kwankwasar yasa ta nufi kofar, budewa tayi se taga wata Mata rike da basket dake dauke da wasu kyawawan kuloli gai sawa su ka yi  sannan ta Mika Mata kwandon tace"ummee tace a kawo muku breakfast"

Karba tayi tace "angode"

Juyawa tayi cikin falon ta nufi inda ta hango dinning ta aje kwandon zata juyo taji takun tahowar mutum tsaye kawai tayi a wurin

Farouk ne ya fito cikin kakinsa na sojoji Wanda ya karbe sa , office ya ke sauri ya wuce akwai abunda zeyi da safen nan

Fitowa tayi dai dai da ya kawo wurin shima ai kuwa karaf suka hada Ido
Wata irin Kara Amal ta saki har se da ya dafe kunne , se Kuma tayi luuu ta fada kan kujerar dake bayanta
Tsaye yayi kawai yana kallonta ,tunani ya fara wannan meke damunta ,har ya taka ze wucewarsa se Kuma yaga Alamar kamar bata motsi da sauri ya dawo har ya Mika hannu ze taba ta se Kuma ya fasa tsaye yayi na few seconds se Kuma wani tunanin ko Suma tayi ya zo masa da sauri ya shiga kitchen fridge ya bude ya dauko Ruwa yana zuwa a tsaye ya fara zuba Mata su gasu da matukar sanyi Numfashin da ta fara ne yasa kawai ya nufi hanyar fita gidan...............✍️

*Aysha galadima ce*

Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now