ANYI GUDUN GARA 41-42

279 19 2
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


*NA*
*AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


'''Follow me on #Wattpad
@Ayshagaladima666'''

'''When you're down ask help from Allah
When it gets fine, don't forget to call Allah again and''' '''say''' *ALHAMDULILLAH*




*PG41-42*

_______________________________

tafe yake cikin mota yana tunanin Wai kamar shi farouk ne aka ma wata dole ta auresa bayan shine Wanda 'yan Mata ke rububi lallai wannan yarinyar zata San ta shigo gonar sa

Kai tsaye gidan ya nufa ya Danna hon me gadi ya wangale masa gate , da sallama ya shigo falon direct dakinta ya nufa ya sanya Kai ciki ,dai dai da ta fito bathroom daure da guntun towel pink colour a jikinta wurin madubi ta nufa

Tuni gogan naku yayi mutuwar tsaye ganin wannan kyakyawar fulawar a gabansa

Ba ta San da shi ba duk da kamshin turaren da taji ya gauraye dakin saman stool din madudi ta zauna ta warware ribbon din dake kanta, gashin nan ko ya zubo Masha'Allah ,dama Allah ya Mata baiwar gashi ,sannan kafin suje kwankiyal har saloon se da suka je ita da Aunty Ramla

Dago kan da tayi ta cikin madubi ta hangi mutum ta cikin madu , wata irin razananniyar kuwa tayi ,wadda ita ce ma ta dawo da farouk hayyacinsa Tana Shirin tashi tsaye ya buga mata tsawa tare da cewa"sit down Joe"

Jiki na bari hawaye na zubar Mata ta zauna Tana kama towel din dake barazanar barin jikinta

Matsowa ya fara yi yana tunkaro ta ganin haka ya sa gabanta ya ci gaba da faduwa ta sunnar da Kai hawaye na zu ba

Gaban madubin ya zo ya tsaya dab da ita , ganin yadda jikinta ke rawa yasa yace Mike tsaye

A sanyaye ta Mike ko Ina na jikinta na bari,kalon sama da kasa ya Mata ya yamutsa fuska ,yace "dago kanki ki kallan"

Kasa dagowa tayi har se da ya sake daka Mata wata tsawa sannan ta kalle sa Tana rufe Ido

Cewa yayi "je ki sa Kaya ki same ni falo"
Ya juya ya fita yanayin jikinsa duk ya canza se yamutsa fuska yake

Daya daga cikin kujerin falon ya zube ya na sauke ajiyar zuciya tamkar Wanda yayi gudu

Ai Tana ganin ya fita da sauri ta nufi wadrop ta jawo wata doguwar Riga data gani a sama ta saka ,Tana ja masa Allah ya isa,Tana Kuma kuka

Hijabin sallar ta ta saka ta nufi hanyar fita tana matsar kwallah

Koda ta fito dakin bango ta kama biya kamar marainiya

Shi Kuma idonsa a lumshe suke kamar me bacci ,a darare ta nemi nesa da shi ta zauna akan carpet,sannan ta boye fuskarta a tsakanin kafafunta

duk abunda take yana kallonta , ganin yadda ta boye fuskarta ,wata zuciyar ta ce masa ai Kai ne bata son gani ,tunda ta tsani masu kaki, ai ko Mike wa yayi ya nufi dakinsa,

Lokar gefen gadon sa Naga ya bude ya dauko karamar bindiga irin ta hannu, rufe lokar yayi ya fito dakin

jin motsi yasa ta dago kanta shine dai da sauri ta sake sunkuyar da kanta gabanta na faduwa

Kujerar kusa da ita ya zauna yace "matso nan gabana"

Kasa take kallo ta rarrafo kusa da kafafun nashi

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now