ANYI GUDUN GARA 21-22

255 17 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)



_Wannan shafin naki_ _ne_ *Ummu Muhammad*
_Nagode da Addu'arki kema Allah ya kare ki a duk inda kike_


*PG 21-22*

___________________________

Wayancewa yayi ya raba ze wuce ta gefenta se ta gaida shi ya Amsa ciki ciki ,ita bata ma ji amsawar ta shi ba

Tana fitowa se ga khaleel kallonta yayi da mamaki yace"kanwata kun San su farouk ne?"

Girgiza kai ta yi a takaice ta fada masa alakar ta su ta masa sallama ta wuce shima dakin ya shiga, Koda ta tafi umma na tsaye Tana jiran isowarta, Tana ko zuwa suka fita titi suka nemi  adaidaita suka wuce gida

______________________________

Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda soyayyar Ramla da yaya Sadiq,Wanda cikin qanqanin lokaci wata shakuwa ta shiga tsakaninsu ,Wanda a yanzu ji yake kamar an cire masa Amal a zuciya ne aka saka masa Ramla a zuciyar tasa, Wanda har uwayen nasu sun fahimci shakuwar dake tsakanin 'ya'yan nasu , ba karamin farin ciki su kayi ba kuwa Dan su Abbah har sun saka bikin nasu nan da wata biyu

Koda Amal ta fahimci yayarta ta fada a soyayya ba karamin farin ciki tayi ba har  take cewa "anty Ramla waye yayan nawa Wai?"

Shiru ta Mata se can tace yaya sadeeq ne fa
Dafe kirji Amal tayi tace "Dan sandan Zaki aura lallai bani ba zuwa gidanki"

Se yanayin Ramla duk ya canza Tana kallon kanwarta ta se tace"yanzu Amal saboda kawai yana dansanda Zaki ce baza ki zo wurina ba, dama na fahimci kin gaji da ganina shiyasa kika ce haka se kwallar da ta taru a idonta ta zubo
Take jikin Amal yayi sanyi ta matso ta rungume Ramla ita ma se hawaye Tana cewa"yi hakuri yayata Wasa nake zan zo Allah "

Dago ta Ramla tayi ta goge Mata hawayen fuskar ta ,ita ma Amal ta goge Mata nata

Ramla tace"har kin sa naji dadi kanwata, dan Allah ki cire wannan tsoron da kike ma 'yan sanda , sufa masu kama masu laifine da kuma kula da kiyaye dukiyoyin Al'umma bakamar yadda kika fahimce su ba ,sannan yaya sadiq Dan uwanmu ne ,shi nasan baze iya ko kashe kiyashi ba ballantana mutum" ta kare maganar Tana kallon Amal data natsu Tana saurarenta

Sauke ajiyar zuciya tayi tace "Allah ya gani Aunty bani nasa ma kaina wannan tsoron ba Ammah Insha'Allah zanyi amfani da maganarki zan rage tsoron sosai"

Ramla tace"yawwa ko kefa autar ummah"
Daga nan suka ci gaba da firar su gwanin sha'awa
___________________________

A bangaren gidansu farouk kam tuni  Abba ya warware kamar ba shi ba Dan Asibiti ko sati be yi ba aka sallame shi , ai ko bayan yaji sauki se da ya dauki ummee da kansa suka je gidansu Amal ya Kara yi ma Abba godiya sosai har da bashi kyautar kusan 1million ya ba Abba akan yaja jari ya Kara  fadada sana'arsa fafur Abbah yaki karba yace shi fa duk abunda yayi ,yayi ne saboda Allah ,ai ko nan Abbah ya Kara kima a idanun Abban su farouk

"Hattara Mata da maza Dan Allah mu dinga hade kwadanmu ,saboda a zamaninnan kwadai ya ma mutanen mu yawa, mussaman 'yan matan wannan zamanin Wanda kwadayi kesa suje su zubar da kimar su Dan Allah mu gyara saboda duk Wanda ya shiga motar kwadayi to tabbas zata ajiye shi tashar wahala

Sannan manzon Allah( s.a.w) yace in kana son kaji dadin mu'amula ko zama da mutane to ka kiyayi Abun hannunsu .
Allah ya shiryar damu"

To kunga dai Abbah kyauta ce aka masa be karba ba Ammah kuma rashin Karbar ya jawo masa wani mutunci a idon me kyautar

Sunyi kusan awa daya suka musu sallama Dan se ranar ma ummee taga Amal aiko taji yarinyar ta kwanta Mata arai sosai 

Ko bayan sun koma gida se da ummee ta tayar da firar gidan su Amal ta ke cema Abba "gskya na dade banga mutumin kirki irin Abban su Amal ba ga yaran nashi masu natsuwa da tarbiya"
Abba yace "umeen yara na rigaki a zuci ki ringani fada ,kinsan mutuminnan har kyautar kudi na masa akan ya Kara a sana'arsa yaki ya karba, ba magiyar da ban masa ba Amma Sam yaki karbarsu"
Murmushi ummee tayi tace ai ni naji Ina matukar kaunar wannan ahalin kar kaso kaga yadda yaran nasa suke da tarbiya"
Se Abba yace "ba yarinyar sa daya ba wadda naji yace an kusa bikinta?"
Ummee tace su biyu ne Ramla da Amal

Babbar ce naji ance za'ama aure  karamar kuma kamar s s 1 take Dan na tambayi karatun nasu

Jim Abbah yayi yana wani tunani................✍️

*Aysha galadima ce*

Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now