ANYI GUDUN GARA 63-64

318 21 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)

*PG 63-64*

________________________________

Ummee da kanta ta tayar da Amal a hankali ta taimaka Mata suka shiga cikin bathroom ,cikin ruwan zafin tace ta zauna,zaunawa tayi tayi wata irin zabura saboda azabar zafi,ta tashi lallashinta ummee Tai tayi har ta zauna cikin ruwan hawaye kawai take yi ba bakin maga, ummee ba karamin tausaya Mata tayi ba sosai,har dai Tai Mata hakan kusan so ukku sannan suka fito tare ,ba karamin Jin dadin wankan Amal taji ba Dan ta rage Jin Abubuwan da ta ke ji sosai, doguwar Riga ummee ta bata ta saka ,sannan ta samu ta Rama sallolin da ke kanta

Bayan ta gama tana zaune kan dadduma sallama Akayi aka turo kofar dakin , ummee ce ta Amsa
Matar khaleel ce ta shigo Tana dauke da kwandon Abinci

Gaisawa tayi da ummee,sannan ta jiyo kan Amal ta na Mata ya jiki,da sauki tace Mata
Cup ummee ta dauka ta hada Mata tea ta  Bata karba tayi Tana Sha a hankali,Sallamarsa ce tasa duk suka dago suna kallonsa

Wata irin sarkewa Amal din tayi da tea din da take Sha da sauri ya karasa shigowa dakin

Har ya Mika hannu ze taba ta ummee ta masa wani irin kallo tuni ya dauke hannun sa,ita Amal Kara shigewa jikin ummee tayi ,ita Kuma ummee ta dinga bubbuga bayanta

Har tarin ya Dan lafa Mata,sannnan ta Bata ruwa ta Sha,shi dai farouk ya na gefe a tsaye

Bayan ta gama Shan tea dinne ta Sha magungunata ta kwanta da sauri ta rufe idanunta Dan kar ma su hada Ido

Ganin hafsa na Nan matar khaleel ,yasa ummee tace muje ka kaini gida Zan dauko wasu Abubuwan mu dawo tare

Tuni jikin farouk yayi sanyi Dan tunda ummee ta masa wannan kallon ya tabbatar da ta San komai

Hafsa suka Bari da Amal suka fita ,tunda suka shiga mota yaga ummee ta Sha masa toka sosai har suka isa gida

Fita tayi ta barshi a motar ,dole ya rufe mota ya biyo bayanta ,ko da ya shigo tana zaune a daya daga cikin kujerin falon

Shigowa yayi jiki a sanyaye ya zauna

Kallonsa tayi kafin tace"Babana miye Amfanin abun da ka aikata fissabillilahi ,me makon kabi matar ka a hankali shine za kayi Mata wanna aika aikar ,irin wannan abun fa ake Kira fyade,runtse idanunsa yayi Yana me takaicin abunda yayi ,ci gaba tayi da masa fada sosai,sannan ta dawo da masa  nasiha akan ya dinga bin komai a sannu ,in ba cin ma zalamarsu ta 'ya'yan yanzu ai da mace na shekara gidan miji be bi ta kanta ba

Shi dai farouk kansa na kasa duk kunya ta kama sa,se hakuri yake Bata Ammah ya ki dago kansa

Ganin yadda duk ya zama wani kalan tausayi yasa ummee ta bar maganar tace to"ka tashi kaje Kuma ka ba matar ka hakuri ,ka Kuma lallashe ta Allah ya maku Albarka ,anjima Zan sa driver ya mayar da Ni"

"To " yace ya Mike ya fita

Bayan sa ta bi da kallo Tana me jin kaunar Dan na ta🥰

Bayan fitar su Farouk ,Amal mikewa tayi zaune dama ba bacci ta ke ji ba,suka fara Dan firar su da hafsa,Nan hafsa ke cewa "Amal ko dai mun samu karuwa ne,Naga ummee ma ke jinyar taki"

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now