ANYI GUDUN GARA 13-14

260 18 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(080649333819)


*Dubun gaisuwa a gare ku*

*Aysha humaira*
*Precious*




*PG13_14*

____________________________

Kara rungume ta ummah tayi Tana murmushi tace "to tashi kije ku shirya kar kuyi lattin makaranta"

Tashi tayi ta fita ta shiga dakin su Tana shiga Ramla na fitowa bayi ,tace "da yanzu Zan kwala Miki Kira kizo kiyi wanka kar mu makara, kin San yau Monday fa"

Amal tace Insha'Allah ba zamu makara ba yau"

Ta shiga wankan ita ma , ba ta jima ba ta fito ta shirya sukai breakfast suka wuce.......

___________________________

Haka Rayuwa ta ci gaba da gudana , tun lokacin da su kawu lawan suka dawo kaduna ya zauna yayi nazari sosai akan zancan Auren Sadiq da Amal , se ya samu umman su husna da zancen  ya Mata bayanin komai yadda suka yi da Isma'il  , ajiyar zuciya ta sauke tace" nima abunda na ke gani a hakura da wannan hadin da'ake so ayi,  kawai ya nemi 'yar uwar ta Ramla ya aura , in sun dai dai ta shike nan ,Suma in basu daidai ta kada muce zamu takura akan lamarinnan yanzu zamani ya canza malam"

Yace "nima abunda na yanke kenan Zan zauna da sadiq din na mai bayanin komai "

Tace "to yayi Allah ya taimaka "

Yace"Ameen"

Kwana biyu da maganar ta su Abba ya nemi ganin Sadiq , bayan sun samu kebewa yake masa bayanin komai da komai , ji yayi kamar an buga masa guduma, gashi baya da damar yin jayayya da mahaifin nasa

Se yace"to Abba Insha'Allah duk yadda kace haka za'ayi

Koda Abba ya dubi Dan nasa se yaga duk yanayin sa ya canza, se yaji Dan nasa ya bashi tausayi , se dai baya da  ba abunda ze masa

Danshi kawu lawan duk da be yi wani karatun boko me tsayi ba ya san yanzu an bar yayin auren dole

Sannan yanzu auren  Ina so , kana so ya yakaya ballantana auran dole,  shiyasa yake ganin baza ya takura kowa akan wannan zancen daga cikin su biyun nan ba

A haka Sadiq dai ya ma mahaifin nasa sallama ya fita , dakin sa  ya wuce ya kwanta, take yaji wani zazzabi ya ta so masa ya rufe jikinsa da bargo

Har se da husna  ta shigo kawo masa abinci ta tarar da halin da yake ciki taje ta fada wa ummansu , tasowa tayi ta biyo bayanta suka shigo dakin

Husna ce ta kama bargon Tana Kiran "yaya Sadiq ka tashi "
Tana matsar kwallah Dan Tana matukar kaunar yayan nata duk da zafin da yake da shi ,bata so taga abunda ya same sa

Daurewa yayi ya Mike zaune , idanun sa sun kada ga jijiyoyin kansa duk sun fito Alamun yana jin ciwon Kai sosai

Ummansu ce ta katse shirun da cewa"dama baka da lafiya shine kazo ka kwanta a daki , to
Kasha magani?"

Da kyar ya girgiza kansa Alamar a'a

Abincin da husna ta kawo tace ta zuba masa yaci kafin ya Sha magani

Ita kuma ta fita ta nemo mai magani

Da kyar ya danyi Loma biyar ya aje

Husna ce ta dawo da maganin da ummah ta bata,Dan ita bata  dawo ba karba yayi ya Sha sannan ya kwanta

Husna na ci gaba da jera mai sannu

Ummah ko da taje, daki ta zauna tasan wannan zazzabin nasa ba ya rasa nasaba da maganar da Abba ya masa na zancen janye maganar aurensa da Amal da'a kayi

Fatan ta daya Allah ya cire masa ita a zuciya ya zaba masa wadda ta fita

___________________________

   Farouk ma a daddafe yayi weekend din a gida ya tattara ya koma barrack , saboda duk lokacin da ya hadu da Abba se ya tuna maganar da su kayi

Shi kam dai be sake bi ta kan maganar ba saboda har yanzu be ga wadda ta masa ba ,lokaci bayan lokaci maganar na fado masa a Rai

Yau ma yana zaune a cikin office din sa se yaji an kwankwasa kofar duk zatonsa khaleel ne se ya bada umarnin a shigo

Kamshin da yaji ya tabbatar masa da ba khaleel bane Amma be dago Kai ba yaci gaba da abunda yake

Ji yayi ance " well done sir"

Ya dago kansa ya kalle ta , wata 'yar kabilar ibo ce tsaye taci kitson attach ,fara ce har wani doruwa-doruwa take Wanda ke nuna har da mai take shafawa, Tana sanye cikin uniform dinsu na sojoji

Ya dau sakanni be amsa ba se can yace"thanks"

"Sir Ina son magana da Kai"
Ta fada

Yace "am busy now"

Shiru tayi ta jawo kujera ta na son zama yace "please can you excuse me"

Se ta Mike jiki a sanyaye ta fita

Shi kuma ya bita da harara da tsaki

Monica sunan ta ta dade Tana mutuwar son farouk tun Tana boyewa ,har ta fada ma khaleel ta ce ya fada masa ,lokacin da khaleel ya fada masa har fada suka tashi yi ma

Daga lokacin khaleel be sake tayar masa da zancen ta ba , bawai  Dan bata yi bane

Ita ma kyakyawa ce kunsan kabilar ibo akwai masu kyau da farar fata a cikin su

Ka Wai dai shi ya tsani macen da zata ce tana sonsa da kanta , yana daukar su Mata marar kamun Kai, sannan uwa uba gata ba musulma ,shiyasa be taba bata fuska ba

"Hattara 'yan matan zamani Kuna ganin kamar wayewa ce kije ki ce ma wani namiji kina sonsa , to ba wayewa bace face rashin kunya da kuma Rashi aji,. 'yan matan hausa fulani da'aka sani da alkunya, koma bashi ba kunya adon mace, Amma ba kunya ba komai ki tunkari namiji kice Wai kina sonsa habah sisters gaskiya ku Dena ba Abu bane me kyau, saboda namijin nan ko ya aure ki yana Nan yana kallon ke kika ce kina sonsa ko Abu ya hadaku tsab ze goranta maki , babban tashin hankalin ma duk macen da ke zuwa Tana cewa Tana son namiji ana daukarsu marassa kamun Kai ko mutanen banz, Allah yasa ku gyara"

___________________________

Yau ta kama Wednesday dai dai da antashi su Amal daga makaranta ga garin hadari ya hadu sosai ,Wanda ko da wane lokaci Ruwa na iya saukowa

Sauri kawai suke yi kar ruwan ya dake so ai ko se ga ya an sako su

Tafe suke shida khaleel a mota tasowar su daga wurin aiki kenan yace muje gidan kaka mu Sha fura
Dariya kawai khaleel ya yi ya shiga mota  suna tafe suna fira har sun gota su khaleel ya sake yowar baya yana kallon su Amal  ya gane su

Farouk yace" lafiya ka dawo?"

Yace wasu kannena nagani bari mu dauke su Naga an fara Ruwa shi dai be ce komai ba

Yana fitowa yasha gabansu yace "kanenna barka kuzo na rage muku hanya ,ga Ruwa har ya fara sauka
Har Amal zata ce A'a
Ramla ta rigata tace
"Muje mun gode fa"

Yace "ba komai " yana murmushi

Jawo hannun Amal tayi suka nufi motar suka shiga, har sun zauna dago kan da zata yi ta kalli madubin motar numfashinta ne ya fara sama sama da kyar ta kwato maganar"aunty Ramla da karfi"!
.....................✍️

*Aysha galadima ce*

Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now