ANYI GUDUN GARA17-18

259 20 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*





_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)








*PG 17-18*







_____________________________

Ta saki wayar kan gado ta fita da sauri dakin Tana dafe kirji umma da ke zaune tsakar gidan ta dube ta tace "lafiya kika fito kamar da gudu?"

Zare ido ta fara tace"ummah Aljani Wai ya kirani a waya"

Umma tace" ke banson shirme aljanin lafiya "

"Ummah wallahi da gaske nake"
Tana me rau rau da ido

Ummah tace "je ki dauko wayar na gani taje tadauko wayar ta bata

Se wayar ta dau Kara , umma ta daga tace "Assalamu Alaikum"
Daga jin muryar ummah ya gane ta nan ya gaishe ta ya ce "ummah sadiq ne"

Se ummah ta fadada fari'ar ta nan take tambayar sa mutanen gida yace duk lafiyar su kalau
Sannan ta Mika ma Ramla wayar ta tace "karbi yayanku ne "
Karba tayi ta shiga daki ta gaida shi ya amsa yana me lumshe idonsa
Ji yayi muryarta na masa kama da ta Amal , nan yake taya ta murnar kammala secondary ta ma sa godiya ,suka yi sallama

_____________________________

Abubuwa da dama sun faru har da bikin khaleel da'aka Sha ,tun da akayi bikin khaleel Abba ya Kara yi ma farouk maganar auren sa yace masa ai ya kusa gabatar da yarinyar basu dade da haduwa bane shiyasa

Kuji karya 😀

Yace to yayi Ina sauraron Amsar ka nan kusa bana son abun ya dau lokaci fa ya ce "to Abbah"

A wata ranar laraba
Duk suna zaune a falo, farouk ,ummee da kuma Al'amin dake rike da laptop yana wani assignment a ciki

Abban su ne ya shigo gidan da hanzari  ,duk su ka maida hankalin su wajansa ,yace yana da meeting a Abuja ya zo
Daukar wasu muhimman takaddune

Sama ya haura, ummee ta take masa baya  domin taya sa kimtsawa

Bayan kusan 30 minutes se gasu sun sauko, ummi na rike da brief case din Abbah duk mikewa suka yi farouk ya karbi brief case din a wurin ummee ya fita zuwa parking space
Da sauri driver din Abba ya taso ya bude motar farouk ya saka jakar se gasu duk sun fito har ummee sun takowa Abbah

Cikin alhini sukayi sallama da mahaifin nasu
Ya shiga mota driver ya ja suka fice  daga cikin gidan 

Tafiyar ta su bata yi wani nisa ba suna gab da fita garin kaduna wata babbar mota ta Karawa  motar su , motar tasu ta wani wuntsila gefen hanya

Dai dai lokacin Abba ya fito wani wuri yana kan babur din sa ya ga abunda ya faru da sauri yayi parking ya Kara sa kusa da motar da ya hangi wasu matasa biyu har sun bude motar sun jawo jakar Abba daya ya rataya

Yana zuwa dama be yadda da yaran ba tun da ga yanayi. Shigar su se yace 'yaro bani jakar nan daka dauka "

Basu San da zuwan Abba ba ganin sa kawai yayi , ba kunya ba komai  ya Mika jakar ,  Abba ya karba ya shiga yaga Abban su farouk da ke kwance cikin jini , ga driver shima kwance be San inda kansa ya ke ba

Abba ne ya juyo yace ma dayan ya tare masa taxi  yako tarar masa ,su suka tai makama Abba aka dauki Abbansu Farouk da driver a taxi
Abba ya rufe motar ya dauki makullin ya juya ya kalli samarinnan ya basu dubu biyu su raba suka karba suna godiya

Abba girgiza kansa kawai yayi saboda yaran gwanin tausayi gasu samari ammah sun bata kan su  da shaye-shaye   Allah ya shirya duk masu yi

Da sauri me taxi yaja suka wuce asibiti da kyar abba ya samu aka karbesu Dan se da ya nemo 'yan sanda

Dakin da'aka kwantar da Abban su farouk ya shiga yana kallon inda ya samu raunuka karar waya yaji  na fitowa daga jiki. Abbah zaro ta yayi

Ya Amsa daga  go "ummee tace "Ina me wayar"?
Dan tunda ya tafi gabanta ke faduwa

Nan Abbah ya shiga fada mata abunda ya same shi

"Innaliahi wa'ina ilaihi raji'un "
shine abunda ta fada ta saki wayar , duk su farouk suka Mike suka zo kusa da it , suna tambayar
"Ummee me ya faru?"

Shiru tayi Tana nuna musu waya da sauri farouk ya dauko wayar , ya sake Kiran number. Abbah nan shima yaji abunda ya faru
Tuni gumi ya karye masa da sauri ya dauki key din motar sa ze fita , se kuma ya dawo yace"Al'amin daukowa ummee mayafinta"

Da sauri ya dauko Mata suka fita  duk suka shiga mota ya fice  gidan da sauri
Dama Abbah ya masa kwatancen asibitin da suke

Koda suka isa dakin da aka kwantar da su suka. Shiga, suka nufi gadon da Abba yake Kai  , buguwace yayi akansa an daure wurin da bandeji se a hannu da ya jimu, Allah ya tsare da ba karaya a ko'ina

Tuni Al'amin ya fara hawaye, ummee ma idonta sun kada ammah dai bata yi kuka ba , farouk ne ya matso ya fara diba raunukan da ya samu da yaga ba raunuka sosai kuma ba karaya se ya sauke ajiyar zuciya yace" ummee be ji ciwo sosai ba ku kwantar da hankalinku ya jawo Mata kujera , ya ja hannun ta ya zaunar da ita akai , Al'amin ya kalla da ke kuka se da ya hararesa sannan yace"Kai kuma miye da girmanka zaka zauna kana kuka, so kake ka tayar ma ummee da hankali, hawayen da yake yi ne ya shiga goge wa , turo kofar dakin Akayi , Abba ne ya shigo da sallamarsa 
Farouk ya Amsa karasowa yayi cikin dakin , da ze musu bayani tuni farouk ya dakatar da shi da cewa"Abba Kai kawo su asibiti ko mun gode Allah ya saka Alkhairi

Abba yace"base ka godemin ba"

Shima kujera farouk ya jawo ya Mika masa ya zauna Jim kadan ya zaro makullin motar da jakar da ya rabe a can gefe ya ba farouk bayan ya musu bayanin yadda hadari. Ya afku

Nan ya musu sallama yace ze je gida Amma ze dawo har da iyalinsa nan ummee suka shiga yi mashi godiya......................✍️


*Aysha galadima ce*

Comment
Share

ANYI GUDUN GARAOnde as histórias ganham vida. Descobre agora