ANYI GUDUN GARA 33-34

259 18 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)



*PG 33-34*

________________________________

Washe gari da wuri suka tashi sukayi wanka,sannan duk suka yi breakfast da aka aiko husna ta kawo daga gidansu yaya  Sadiq

Bayan an gama nan suka shiga gyara Mata gidan

Ummah me kudi ce ta Dan Kara yi ma Ramla nasiha,nan ta dauko wata leda a Jakarta ta bata tace"yadda za'ayi amfani da komai yana ciki"

Ita dai Ramla se 'yan kwallah ta ke gogewa,Amal tuni Ido ya Rena fata

Ba jimawa kusan 10am khaleel yazo gidan sadiq inda anan ne ze dauki ummah me kudi da Amal su wuce Kd

Ai ko Amal tuni ta saki kuka har suka fito filin gate taki sake Ramla, ummah me kudi se rarrashinta take , khaleel shima ya fito daga mota yana kallon drama da'ake da ita ,se ya ji ta bashi tausayi

Hango Sadiq da ummah me kudi tayi  yasa ta shiga mota ta zauna

Kamar daga sama suka ji ance
" ke sakar min mata"

Duk juyowa suka suka ga ashe yaya sadiq ne

Yana isowa ba kunya ya kama hannun Ramla ya rike,ita dai Ramla sunkuyar da Kai tayi saboda khaleel na tsaye

Ai Amal ba shiri ta saki Ramla Tana kallon yaya Sadiq 

Shi kallon Ramla ma yake yana cewa"ai se ki sa hawayen my wife su kare habah Amal"

Se ya dago kansa yana kallon Amal da hawaye duk suka bata Mata fuska ,se kuma yaji ta bashi tausayi

Kama hannunta yayi ya ce"kibar kuka my sis kinji Allah ya bada Zaman lafiya Amarya"
Ya kare maganar da zolaya
Ai ko se da ta rufe fuska Tana jin kunya

Rike hannunta yayi har zuwa Motar
Ramla na gefen sa na dama

A hankali ta shiga motar se ta juyo Tana kallon Ramla
Ganin zasuyi wani kukan da sauri Sadiq ya rufe motar ya juyo yayi sallama da khaleel da ummah me kudi

Ya ja hannun matarsa suka shige ciki

To Amarya Ramla Allah ya bada Zaman lafiya
_____________________________

Suna shigowa garin kaduna gidansu farouk ya wuce da dasu ummah me kudi,Dan wannan umurnin Abbah ne ,akan Akawo su Amal nan gidan nasa

Tarba ta mutunci ummee tama su ummah me kudi
Daki guda ta basu, su shiga suyi sallah su huta ,har Abinci ma a can ta gabatar musu Dan su samu sakewa

Bayan sunyi sallah ummah me kudi ta zuba abincin,tace ma Amal tazo taci abincin ,Dan har ta kwanta,tasowa tayi Dan tasan ummah me kudi bata da Wasa ,tsab zata iya balbale ta da fada

Tashi tayi taci Abincin bayan ta gama ta Dan kwanta

A bangaren Abbah kuwa tun jiya da ya dawo gida ,ya Kira farouk bayan sun gama gaisawa nan Abbah ke fada masa auren da ya masa

Gumi ne ya dinga tsatsafo masa ya ma rasa abunda ze ce Banda bugawa ba'abun da zuciyarsa ke yi

Abbah ne ya katse masa tunani da cewa "gobe in Allah ya Kai mu Zan turo masu Kaya zasu zo su saka Kaya a gidan naka , khaleel ma yana can shi ze zo da matar taka gobe Insha'Allah

Wani tukuki ne ya taso masa jin cewa khaleel ma ya sani har ma da shi akai komai be fada masa ba

Ummee ce ta katse masa tunani da cewa "kayi shiru ba zaka ce komai ba?"

Wani Abu ya hade kafin yace"nagode Abbah Allah ya saka da Alkhairi"

Murmushin manya Abbah yayi ,saboda ya kula da halin da farouk ya shiga
Yace"Ameen

Nan dai iyayen nasa suka ci gaba da yi masa nasiha Wanda yasa jikinsa ya danyi sanyi ya rage radadin da yake ji a cikin ransa

Fatansa daya ALLAH yasa ba kwaila mahaifin nasa ya aura masa ba,sannan Koma wacece ze koya Mata hankali tunda ta shigo rayuwarsa be shirya ba

Bayan sun gama yi masa nasihar ya musu sallama ya fita

Ummee ce tace Allah ya basu zaman lafiya
Abbah yace "Ameen"

Kai tsaye gidansa ya nufa  Koda yayi parking motar ya shiga gidan bathroom ya wuce ya sakarwa kansa shower  ya dauki kusan minti goma kafin ya fito

Koda ya fito wayarsa na Kara Koda ya Diba khaleel ne aje wayar yayi be dauka ba ya kirasa ya fi a kirga Ammah be dauka ba

A can gidan su Farouk kuwa se bayan la'asar Amal ta falko tashi tayi ta shiga bandakin wanka tayi Koda ta fito ta tarar da an aje Mata Kaya akan gado ,shadda ce ready made doguwar Riga an Mata stone work me kyau
Saka rigar tayi, ta yi sallar la'asar Tana gamawa aka turo kofar dakin
Ummee ce ta shigo da sallamarta Amsawa Amal tayi
Sannan ta gaida ta cikin girma mawa

Amsawa tayi cikin sakin fuska tace" 'yata ya gajiyar hanya?"

Amal tace "lafiya Lau " Tana sunkuyar  da kanta
Ummee ta kalle ta tace" ki saki jikinki kinji ki dauke Ni tamkar mahaifiyarki nan gida ne a wurin ki duk abunda kike so ki fadamin kinji"

"To "
Amal tace
Ummee tace "taso muje falo kici Abinci"

A sanyaye Amal tabi bayanta
.......................✍️

*Aysha galadima ce*

Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now