ANYI GUDUN GARA PAGE 5

366 26 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞

*NA*

*AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


*PG 5*

____________________

Koda su lawal su kai Shirin komawa kano bayan suna, fafur sadiq ya tubure cewar baze koma ba se dai abarsa wurin Amal

Se da mahaifin nasa ya jawo sa kusa da shi yace "ka fasa zama Dan sandan da kake so ka zama ne?"

Se yace" A'a Abba ban fasa ba"

Yace "to ka yarda mu koma kano har se ka zama Dan sanda se kazo ka ga kanwar ka lokacin ta girma ,kuma zata ji dadi in ta ga ka zama Dan sandan"

Da murmushi akan fuskar sa yace "Abba na yadda mu tafi"

Malam Isma'il da Maryam dai suna gefe suna murmushi da jin dadin yadda sadiq ya damu da Amal

Ai ko se da ya matso kusa da Maryam yace "umma a sake bani ita na rike kafin mu tafi ta ko Mika masa ita ya karba

Se ya kara bakinsa a kunnenta yana mata magana su kansu ba suji me yace ba 😀

Iyayan nasu suna ta kallo nai suna murmushi to a haka dai suka samu suka musu sallama suka kama hanyar kano...

To tun daga wannan lokacin da suka tafi sadiq be sake zuwa kaduna ba a ce warshi se ya zama Dan sanda😀

Bayan wasu shekaru sadiq ya girma ya zama cikakken namiji burin nan nasa na son ya zama Dan sanda ya cika yana matsayin inspector..

A gidan malam Isma'il yara sun girma Ramla anzama 'yan mata Tana s s 3 a secondary school ita kuma Amal Tana j s s 3

Tun bayan haihuwar Amal, Maryam hai huwa ta tsaya mata cak!

Duk wadannan shekarun da'aka dauka su Amal ko sunje kano basu haduwa da sadiq lokacin yana makaranta daga baya ma su ka rage zuwa saboda makaranta. Da suke zuwa Arabi da boko

To kuma ita Amal tun suna 'yan matasa Allah ya Dora mata tsoron Dan sanda, ko kuma duk wani da zata gani da bindiga,

Kasancewar suna kallon yadda 'yan sanda keyi a cikin films

Tun uwayen na daukar abunta wasa har suka zo suka bar daukar sa wasa,

Akwai wani lokaci da take 10years 'yan sanda suka shigo unguwarsu , suku ma suna waje suna wasa,

Se jiniyar motar 'yan sanda suka ji ai ko ta buga kara!
Tana nuna ma Ramla motar 'yan sandan da ta tsaya kusa da su

Se Ramla tace" ta shi mutafi gida" ta ji shiru , se da ta juyo taga yarinya ta mimmike ai ko da gudu ta shiga gida

Abbah !! Ummah!!

Da sauri malam Isma'il ya fito yana fadar "lafiya Ramla?"

Se waje take nuna masa da hannu ,
Da sauri ya fita wajen ya isko Amal kwance a kasa ,

Koda ya tabata bata tumfashi ya dauke ta suka shiga gida

Ya shimfideta akan tabarma ya nufi randa ya debo ruwa yazo yana ta shafa mata a fuska

Tayi kusan minti biyar sannan ta farfado,

Nan ne fa malam yake tambayar Ramla "me ya faru Wai?"

Nan take sanar da shi "saboda taga 'yan sanda ne"

Da shi da umma suka kalli junansu fuskokin su cike da damuwa...


____________________
*Cigaban labari*

Tafe yake cikin mota ya kunna kira'ar shaikh sudai Abdurrahaman yana saurare ya na kuma biyar karatun nasa a cikin suratul Anfal

Unguwar Rimi ya shiga da motar tasa har iso wani katafaren gida ya Danna hon mai gadi ya wangale masa gate ya shige da motar sa

Se da ya daidai ta parking dinsa ya fito

Se ga mai gadin ya tafo a cikin uniform dinsa yana
fadar" wellcome sir"

Daga masa hannu kawai yayi ya nufi cikin gidan

Wani kyakyawan falo ne ya shigo se tashin kamshi yake
Ba kowa a falon Dan haka se ya haura saman bene

Yayi sallama a wani daki aka amsa ya shiga

Wata kyakyawar mace ce zaune bisa dadduma ga alamu kamar sallah ta kammala ya zo ya zauna kusa da ita

"Ummina barka da yamma"
Abunda ya fada kenan
.daga mishi kai tayi kawai Tana lazimi ne
Lura da hakan da yayi yasa yace "bari naje na watsa ruwa ummi "

Yasa kai ya fita.....................

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now