ANYI GUDUN GARA PAGE 6

347 20 3
                                    


🌸🌸🌸💞💞💞
🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️

*NA*
*AISHA GALADIMA*



*DEDICATED TO*
*HASSAN ATK*


*PG 6*

________________________________________

Koda ya shiga dakin sa toilet ya wuce yayi kusan 30minutes, sannan ya fito daure da towel a kugunsa da kuma karami yana goge kansa ,

Captain Umar farouk irin cikkakkun mazan nan ne masu Kira da cikar halitta , dogo ne wankan tarwada, me dauke da doguwar fuska hade da dogon hancinsa, yana da madaidai tan idanuwa ,hade da karamin bakinsa, gabansa a bude yake Wanda da'an gani ansan ma'abocin motsa jikin sane 6packs dinsa a fili suke ,se dai bai cika kiba ba kirar da yake da ita ne yasa farat daya baza'a Kira sa siriri ba...

Da sauri sauri ya gama Shirin sa ya sanya kana nan kaya ya fito ,

Kasa ya sauko ya nufi dinning table ya fara bude warmers din abincin da ke kan table , da kansa ya zuba abincin ya zauna ya fara ci ,

Ummi ce ta sauko ta nemi daya daga cikin kujerin falon ta zauna

Yana kammalawa ya taso yazo gefenta ya zauna yana fadar"ummina"

Ta juyar da fuskarta gefe ,hannun ya kama ya rike "say something please my happiness"

Se sannan ta juyo ta kallesa ta Dan sassauto da tsuke fuskarta da tayi

Tace " Babana me yasa Kullum se an neme ka kake dawowa gida bayan kasan daga kai se Al'amin a gidannan?"

"Ummi Ayyukane suka min yawa shiyasa Amma kiyi hakuri yanzu gida zan dinga kwana ,ina cin abincin ummina me dadi" ya kare maganar yana murmushi

Ita ma murmushin tayi
Ya jingina kansa a gefen kafadarta
Ture shi ta fara yi Tana fadar "dagani kar Al'amin ya shigo ya gan ka haka"

"A'a ummina nine fa wanda kika fi ji da shi a cikin ranki fa"

Ture shi tayi ta Mike Tana fadar "marar ta ido dagani Kullum ka girma baka San ka girma

Siriryar dariya yayyi yana fadar "ummi ina little bro Banga sa ba tun da nazo"

"Ai kuwa be dade da fita ba yanzunnan zaka gansa "

Kiran sallar magrib da'aka kirane yasa duk sukan Mike sh ya nufi masallaci ita ma ummi ta wuce sama

____________________

Inspector sadiq lawal ya fito cikin uniform dinsa da ya karbe sa yayi kyau sosai a ciki

Falon gidan nasu ya nufa wow komai na falon ya canza da gani sun Kara samun cigaba a Rayuwa

Wata 'yar matashiyar budurwa ce zaune Tana kallo tv ,hankalinta ya dauku bataji sallamar da yayi ba

Se da taji yana" ke husna ba ki zuwa school yau ne"
Ya fafa cikin tsawa firgigit ta dawo hayyacinta

"Yaya sadiq Ina kwana" ta fada

Yace "da ban kwana ba zaki ganni wuce kiyi Shirin makaranta ko na Saba Miki"

A hankali ta raba ta gefenshi ta wuce Tana gode ma Allah da be dake ta ba!

Tana wucewa mahaifiyar tasu ta fito yana ganinta ya duka yana fadar
"Ummah Ina kwana anstashi lafiya?"

"Lafiya lau dan nan"

Ba ta fadar sunansa saboda alkunya irin ta fulani lol😀

"Zan tafi wurin aiki ne dama"
Tace "to Allah ya taimaka"

Yace "Ameen"

Se ga husna ta fito cikin Shirin makaranta ,dama shi ke kai ta sallama kawai tama umma suka yi ma umma suka fito

Motar shi ya nufa ya bude ya shiga ita ma ta bude dayan bangaren ta shiga

Ya tayar suka fita se da suka danyi nisa a tafiyar ya juyo ya kalleta ai ko suka hada ido ta sauke idonta kasa

"Kina jina ko idan na Kara kama ki kina kallo lokacin makaranta jikinki ne ze fa da Miki ,shashar yarinya"

Husna daga kai kawai,jin dadinta daya yau be mareta ba
Saboda yaya sadiq badai saurin fushi ba
Arzikinta daya Dan ma umma na taka mai burki akanta da Allah dai yasan irin hukuncin daze dinga mata
A haka dai har ta samu ya sauke ya bata 500 tayi godiya ta wuce shima ya wucewar sa aikin gabansa

Husna kanwace a wurin Sadiq Dan itace autarsu tunda ba wasu bayan ta kusan sa'ani ne da amal
____________________

Malam Isma'il ne yayi sallama a gidansa da gudu husna ta fito daga daki Tana "oyoyo Abbah"
Tana zuwa ta karbi ledar hannunsa

Ramla dai ruwa ta debo mai a kofi ta Mika masa ya karba ya Sha

Lokacin umma ta fito bayan gida Tana masa sannu da zuwan

"Malam yau Naga ka dawo da wuri"
Cewar ummah

"Eh dama kayan cefanen gobe ne na kawo dazu yaya lawal ya kirani ,yake sanar Dani gobe zasu zo gaba dayansu sunyi hutun mako su koma"

Ai ko nan suka shiga murna zuwan nasu mussaman Amal da ke son haduwa da husna

Ramla ce tace "Abbah Amma bada yaya sadiq za'a zo ba ko?"

"Dashi za'a zo Mana "
Cewar Abba
Ta sake cewa
Amma Abba bashi ne Dan sanda ba?"

"Shine Mana"

Ai ko Amal murna ta koma ciki

"Abba Dan Allah kace kar ya zo shi"
Ta kare maganar da hawaye duk kallo suka bita da shi

Umma ce ta katse shirun da cewa "ke ban son shashanci anki ace kar ya zo din"
Ai ko se hawaye sharr!!

Ta shige dakinsu Tana kuka! .....................

_Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now