ANYI GUDUN GARA 29-30

258 18 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)

*WANNAN SHAFIN NAKU NE*

*ANYI GUDUN GARA FANS GROUP*

*DUNIYAR MAKARANTA*

*ATK HAUSA NOVELS*

*FEENERH FANS GROUP*

_Ina jin dadin comments dinku_

*PG 29-30*

______________________________

Sun dauki tsawon mintuna kamin ummah ta dago kan Amal da hawaye ke ta zubo Mata ,hannu tasa tana goge Mata su Tana cewa" ki bar kukan hakanan 'yata ,idan kika ci gaba da yin kukannan zan dauka kamar ba kiyi na'am da zabin mu ba"

Ajiyar zuciya tayi bayan wasu sakanni tace "ummah ai nasan ba za ku zabar min abunda ze cutar Dani ba"

Wani tausayin ta ne ya kama ummah ,se ummah me kudi ce da wata kanwar ummah suka matso su ka shiga rarrashin Amal din har ta yi shiru , nan suka shiga Yi masu nasiha me ratsa jiki
Har dai suka Dan saki jikinsu

Hakan ba karamin natsuwa ya Dan saukarwa ummah ba Dan tun da maganar auren nan na Amal  yazo kunnenta ta kasa samun natsuwa

Abunda ya faru kuwa shine
ranar da Abban su farouk ya je gidan Abbah a can kd , bayan sun gaisa ,nan fa ya  nemarwa Dan sa auren dai daga cikin 'ya'yan Abbah, nan Abbah ke ce masa babbar ai aurenta za'ayi dayar kuma ko secondary school bata gama ba , nan Abban su farouk ya shiga magiya akan Abbah ya taimaka masa saboda yana son hada iri da shi kasancewar sa mutumin kirki , kuma yana da tabbacin 'ya'yansa duk masu tarbiya ne

Be boye masa komai akan farouk ba har da damar da ya bashi na ya fitar da matar aure be yi ba ,shiyya sa yake ganin ya da ce a matsayin sa na mahaifinsa ya zaba masa, a karshe yake cewa zancen karatun Amal kuwa zata ci gaba ko bayan auren na su , nan dai ya ci gaba da yi ma Abbah magiya , Wanda hakan yasa Abbah ya kasa musanta masa, saboda ya na jin nauyin sa da kuma girmansa Dan ko a shekaru ya fisa

Se da ya Dan yi shiru na wani lokaci ,sannnan yace"To Alh a yanzu bazan iya yanke hukunci ni daya ba ,Ina da yaya da kawuna da yake can bauchi ,Zan fada musu duk abunda suka yanke nima shine nawa , anan kafin Abbansu Farouk yama Abbah sallama se da ya karbi number wayar kawu lawal a wurinsa

Dama washe gari akwai abunda ze Kai Abbansu Farouk kano ,Dan haka Koda yayi waya da kawu lawal bayan sun gaisa nan  yake ce masa gobe ze shigo kano yana son su hadu

Washe gari ko Abbah ya nemi wani Amininsa suka je kano ,tarba ta mutunci kawu lawal ya musu ,se bayan sun zauna ne Abbah yaga Ashe yasan kawu lawal shi ma kawu lawal nan ya gane Abbah nan suka Kara gaisawa ,

Can baya akwai wani taimako da Abbah yama kawu lawal

Bayan gaishe gaishe nan Aminin Abbah ya gabatar da bukatar da ta kawo su ,Dan Jim Abbah yayi saboda shi ya San Alh Bashir maradun mutumin kirki ne ,ga taimakon Al'umma dan shi shaida ne
Kuma a yadda yadda yadda sansa tsayayyan mutum ne Dan haka ko 'ya'yan sa ya San suna da tarbiya

Murmushi yayi yace to Alhamdulillah ba laifi na amince se dai bari na Kira kawun mu kuji ta bakinsa ,waya ya daga ya Kira kawu ya saka ta handsfree

Nan dai Aka tattauna bayan tambayoyi da kawu ya sake ma Alh Bashir.
Nan dai kawu shima ya amince

Fadar farin cikin da Abban su farouk ya shiga baze misiltu ba
Cikin farin ciki ya dawo kd ,se dare yake sanar ma ummee ita ma tayi farin ciki sosai, se dai tana tunanin yadda farouk ze daukin auren ,se dai bata nuna ma mijin nata ba kasancewar ta da sanin ya ka Mata
Da tayi wani tunani ma se take ganin wannan hukuncin da Abbah ya yanke ma farouk shi ne dai dai da shi

Bayan su Amal sun Dan natsu kanwar umma ce ta tirsasa musu cin abinci sama sama suka danci se ga kawu ya aika kiransu dakin sa , tashi sukayi suka nufi dakin nashi  , Koda suka shiga kawu ne da kawu lawal da Abbah dake gefe
Se sadiq dake kasa zaune , Suma gefe suka samu suka zauna

Nan kawu yayi gyaran murya , ya shiga yi masu nasiha me ratsa jiki , tuni su Ramla suke ta kukan su a cikin mayafi se bayan ya gama ne yake kara Jan kunnen Sadiq akan ya kula da 'yar uwarsa ,kasancewar  a ranar za'a Kai Ramla a can kano

Nan fa Amal ta turje akan da ita za'a Kai Ramla nan fa Abban su farouk yace to tazo a tafi da ita daga can su wuce kd , kasan cewar Abban su farouk yace baya bukatar komai na kayan daki ko gara

Da kyar dai aka samu aka banbaro su Amal daga jikin ummah aka wuce dasu cikin mota ,ita ma Amal tafiyar kenan daga ankai Ramla za'a wuce da ita kd

Motar da khaleel ze ja Amaren suka shiga tare da ummah me kudi

Sauran motoci kuma suka dauki mutane Ammah ba sosai aka je da mutane ba kasancewar gari ba kusa ba

Se bayan tafiya ta fara nisa ummah me kudi tace "to ku bude fuskokin ku , kusha Iska Mana "

A hankali suka Dan daga mayafin nasu  suka yi  shiru  suna  kallon hanya
Khaleel da ke tuki kamar Wanda aka tsikara yaji yana sha'awar ganin matar Abokin nasa

Ta madubi ya kalli bayan motar, zaro ido yayi, in ya kalli Ramla ya kalli Amal........................✍️

*Aysha galadima ce*

Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now