ANYI GUDUN GARA 27-28

248 20 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)

_Yau bana jin dadi fans ,ban yi tunanin ma zan iya typing ba,damuwar da kuka nuna tasa_ _nayi  Dan farin cikin ku
Nagode_


*PG 27-28*


________________________________


Da kyar na samu na dau Alkalamin nawa cikin mutane da ya fadi

Khaleel se kallon Abbah yake da ya fito daga massalacin da aka daura auren ,saboda ya yi mamakin abunda yaji marokin na fada ,tun jiya yake mamakin Kiran da Abbah ya masa akan cewa ya gayyaci wasu abokan aikun su zasu raka shi daurin Aure, shi khaleel duk tunanin sa tare da farouk zasu zo , se da suka taso yaga bada shi ba tun nan ya fara Shan jinin jikinsa.

Abba na dago Kai suka hada Ido yafito shi yayi da hannu  , khaleel ya matsa kusa da Abbah

Abbah yayi gyaran murya yace"khaleel kaji an daura auren abokinka ko, Khaleel ya kalli Abbah yace "Eh Abbah Ammah banga farouk din yazo ba kuma be fada muna ba"

Jawo hannusa Abbah yayi suka fito  cikin mutane ,sannan ya kalli khaleel yayi murmushi yace" eh ai bada sanin sa ba ma na masa wannan auren , a matsayina na mahaifinsa na zaba masa macen da na ga yafi da cewa ya aura tunda shi ya kasa nemar wa kansa "
Cikin fushi Abbah ke maganar
khaleel dai sai cewa yayi "Abbah kayi hakuri Insha'Allah farouk ze karbi wannan auren da ka masa da hannu biyu"

Abbah ya nisa yace "ai dolen sa ma ya karbe shi"

Wucewa Abbah yayi ya bar khaleel tsaye da jikinsa ya gama yin sanyi akan wannan auren

Abokansu ne suka katse masa tunani, dayan ya ce "khaleel dama auren farouk za'ayi shine ko ku sanar Mana ka kwaso mu mukazo?"

Khaleel se karya ya musu akan abun ne yazo kurkusa shiyasa be musu damar yi masu  bayani ba
Dayan ya kuma cewa"to Ina angon?"

Yace baya jin dadi ne ,Ammah yanzu zamu juya se mun Isa kd za'ayi reception

Acan cikin gida kuwa suna ta hidimar bikin su har se da wata Mata ma ta shigo gidan take sanar da har an daura auren

Ummah ce ta fito tsakar gidan wasu Mata da suka shigo nan suke tayata murna suna cewa"Ashe kuma matar Isma'il duk 'ya'yan naku kuka aurar to Allah ya basu zaman lafiya"

Tace "Amin"
Yaro take nema ta tura a kirowo Mata su Amal da suke makwabta, bata so 'yar tata taji labarin auren da aka daura Mata tafi so ta fara ji a bakinta

Dan ita ma tun lokacin da Abbah ya tare ta da zancen abunda Abban su farouk yazo da shi ta kasa samun natsuwa Dan dai mijin nata da 'yan uwansa sun Riga sun yanke hukuncin ne ,sannan 'yan uwanta sun taushe ta da bata yadda Anma 'yarta aure cikin hanzari haka ba

Da kyar ta samu wata jikanyar gidan ta tura ta ta Kira Mata su Amal

Da sauri yarinyar ta fita,ita kuma ta koma dakin matar kawu

Ba jimawa ko su Amal suka fito suka nufo gidan bikin suna shigowa abokan wasan su na ta tsokanarsu ita dai Amal bata kawo komai a ranta ba

Dakin matar kawu suka shiga inda ummah take zaune tare da 'yan uwanta na gombe da suka zo da sallama suka shiga suka gaida su ,da fari'a duk su ka amsa

Yayar ummah ce ta yafito su da hunnu tace"kuzo nan 'ya'yana ta nuna kusa da ita kasancewar Tana kuryar dakin

Se da suka zauna ta fara masu nasiha me ratsa jiki ,ita Amal ma mamaki take da'aka hada da ita wurin nasihar aure se rufe fuska take , har ta Mike

Umma me kudi tace"dawo zauna ja'ira Ina Zaki kika Mike?"

Dawowa tayi ta zauna kallonta ummah me kudi tayi tace "Amal Nasan dai Kuna zuwa Islamiyya ko sannan kunsan muhimmacin iyaye a wurin 'ya'yansu ko?"

Daga Kai tayi gabanta ya fara faduwa
Ciga ba tayi da cewa"Idan iyaye suka ba 'ya'yansu umurni me ya kama ta suyi?"

Tace "biyyaya ya kamata suyi akan umurninsu "
Cewar Amal

Ummah me kudi tace "to Iyayenki yau dai sun daura Miki aure da Wanda suke ganin ya cancanta da fatan Zaki yi masu biyayya kamar yadda kika ce"

Amal rasa wane yanayi take ciki tayi ,se wata zufa ke karyo Mata ita kanta Ramla ta shiga shock din Abunda ummahe kudi tace se kallonta  take

Shiru dakin ya dauka

Se can ummah me kudi ta kamo hannun Amal ta rike tace " 'yata kinyi shiru"
Dukar da kanta tayi wasu hawaye na zubo mata da kyar  tace " Zan musu biyayya"

Wata ajiyar zuciya ummah ta sauke ,tasowa tayi ta rungume Amal din tata ita ma Tana goge kwallar data tarar Mata a Ido

Nima aje Alkalamin nayi nafara ta ya su kuka😭...............✍️

*Aysha galadima ce*

Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now