ANYI GUDUN GARA 45-46

275 20 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)

*PG45-46*

______________________________

Ya daga hannu ze mareta ,runtse idanun ta tayi jikinta na rawa Tana jiran saukar Mari taji shiru , bude Ido tayi se taga ya dauki kayan ya nufi dakin sa da su ,Ajiyar zuciya ta sauke ta nufi dakinta da sauri

Yana shiga dakin cikin kayan wankinsa ya sasu , ya dauko wasu kayan ya saka ya fita , be koma bi ta kanta ba

Jin motsin fitarsa yasa ta fito  Tana cewa"Wai Allah ya so ni da mugunan ya maran da wannan katon hannun nasa ai se Naga taurari, Allah yasa ma se dare ze dawo , kitchen ta nufa ta dauko plate da cup ta nufi dinning tayi breakfast ta kula shi be ma ci komai ba ya fita

Koda farouk ya fita Kai tsaye office ya nufa ,Yana zama khaleel na shigowa sallama yayi da kyar ya Amsa masa ,zama yayi Yana tambayarsa me ya faru Nan yake sanar masa ai ko dariya ya shiga masa yace "ai wlh Amal ta min dai dai in ba haka Ina ita Ina wankin kaki in Banda mugunta irin taka,ai ta biyani goro da abunda tayi

Kallonsa yayi yace haka kace ai kuwa ka ja Mata se tayi wani aikin Kuma

Ohho dai duk abunda zakayi ka dai ji tsoron Allah ,yawwa Wai yanaga ka fara wani glowing ko har an wuce wurin?

Wani malalacin kallo farouk kema Sadiq din sannan yace"Kai fa Dan iskane  in ba rainin hankali ba wannan yarinyar da ko kwarin Kashi Bata da kake tunani Zan iya wata mu'amula da it?"

Kallon gara khaleel din ke masa yace "a'a jaririya ce ba kwarin Kashi ne Bata da ba,wallahi tun wuri ka shawo kanta a wuce wurin ,idan ba haka ba Ina jima tausayi zuwa Nan gaba Dan yaran da kake rainawa sunfi wasu manyan Mata komai,sannan yanzu ba'abunda basu sani ba"

Tashi farouk yayi ya bude kofar office dinsa yace "malam zo ka wuce ka barni nayi aikina ,tunda Kai baka da abunyi"

Mikewa khaleel yayi Yana dariyar mugunta yace "ai Kai ne zaka zama marar aikin yi Nan gaba kadan ,sannan ya fice daga office din,tsaki farouk yayi sannan ya rufe kofar office din



A haka zaman nasu ya kasance kadahan madahan har aka cinye sati biyu da bikinsu ,Wanda a lokacin Amal duk ta saki jikinta wanna tsoron da take dashi cikin Kashi 100,zan  iya cewa saura Kashi 20 ,tun lokacin abun da ya faru farouk be koma sata wanki ba se dai ita ke gyaran dakin sa, iya karta da shi gaisuwa ,girki Kuma tuni ya aje Mata komai na bukata ita ke dafawa da kanta

Yau Koda ta tashi taji jikinta duk ya Mata wani iri ta fara jin Alamun kamar period dinta ne  ze zo dama Tana Dan ciwon mara Ammah ba me tsanani ba daki ta shiga ta Dan kwanta bacci ya dauke ta ,se kusan Azahar ta tashi koda ta tashi kuwa duk ta bata bedsheet din ,ahankali ta tashi ta shiga ban daki ta wanke jikinta ta fito, bedsheet din ta canza ,sannan ta nufi wadrop  ta dauko wasu kayan ta saka se dai Bata da pad din da zata yi amfani da ita, tunowa tayi da jakar da Anty Ramla tace kudinta na ciki jawota tayi ta bude ,kudine da yawa a ciki Bata tsaya kirgawa ba ta dauko 3k ,ta sa hijab dinta ta fito gate din gidan wani kurtun soja ne ya taso ya nufota yace
"Madam me kake so?"

Shiru tayi Tana kallonsa ,Tana tunanin ai bari ma ta aike sa , kudin ta Mika masa tace "akwai chemist Nan kusa?"

Cewa yayi "yes"

Tace to idan kaje kace a baka pad pack din gaba daya

Karba yayi ya fita,
Ita Kuma ta koma cikin gida
Iya ka minti biyar taji karar hon da'ake tayi ,Ammah Bata yi tunanin nan ake hon din ba ta cigaba da aikinta a kitchen

Ganin shiru Emmanuel be bude masa gate ba ya sa ya fito daga mota ya nufo gate din karamar kofar ya bude ya shigo ya bude gate din ya shigo da motar sa sannan ya rufe ,dakin Emmanuel din ya shiga ya ga ba kowa

Tunani yake to Ina ya tafi ,muryar kakus ce ta katse masa   tunani da cewa" Wai bazaka zo ka bude Ni ba kabar Ni a mota"

Juyowa yayi yazo ya bude Mata  ta fito Tana kallonsa tace "lafiya kake ta dube dube?"

"Me gadi nake nema"

Ya fada Mata a takaice ,rufe motar yayi yace muje to gaba ta shiga ya biyo bayanta knocking ya fara da sauri ta fito ta nufo kofar ta bude ganin sa da tsofuwa yasa ta basu hanya Tana fadar "sannunku da zuwa"

Shigowa sukayi kakus na "sannunki 'yar Nan sannan suka wuce kakus ta zauna kan kujera shima zaman yayi ,gaisawa sukayi sannan ta Mike ta nufi kitchen ruwa da lemu ta azo bisa try da cups ta fito a hankali ta je inda kakus take ta duka ta aje Mata tace"babah ga ruwa"

Dagowa kakus tayi tace"wace Babar ,Ni karki sake kirana babah ,kakarki ce Ni tunda kakar mijinki ce "to " Amal tace

Yawwa "ya bakunta Kuma 'yar Nan "
Tana murmushi ta kare maganar

A Dan sake Amal tace "lafiya Lau "

Tashi tayi ta shiga daki Tana Dan kakkame jiki gudun kar tayi staining

Duk abunda ke faruwa Yana jinsu yayi Shirunsa ,lumshe Ido yayi har se data tashi zata shiga daki ya bi bayanta da kallo ,Yana tunanin kamar taki sakin jikinta har yanzu  ga Kuma yadda yaga Tana tafiya

Knocking da Akayi ne ya katse masa tunani tashi yayi ya nufi kofar Yana budewa yaga Emmanuel ne ,kallon mamaki yake binsa da shi

Sosa Kai Emmanuel yayi yace"oga na madam send me"

Yana mikawa farouk leda karba yayi ,emmanuel ya tafiyar shi  bude ledar yayi yaga miye aciki idanun sa suka fada Akan VIRONY  PAD

Ranshi ne ya baci Nan take ,tunani ya fara me  wannan yarinyar ta dauke shi ,Dan rashin tunani me gadi zata aika sawo pad , mi yasa ba zata fada mishi ba juyawa yayi ya ya rufo kofar da karfi har se da kakus ta saki Baki Tana kallonsa, fuuuu ya wuce ya nufi dakinta Yana shiga Tana kan gado da sauri ta Mike zaune

Nufota yayi ya jefa Mata ledar a  jikinta yace"ke Wai wace irin marar kunya ce da har zaki aiki me gadi ya sawo Miki wannan abun saboda Baki dauki aurena da mutunci ba ko" ya kare maganar yana huci kamar wani Zaki

Dama kanta banye yake ,matsowa yayi ya kama gashin yaja yace "ko Baki jina ne?"
Tuni ta fara hawaye
Kofar dakin aka turo...........  .✍️

*Aysha galadima ce*

Vote
Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now