ANYI GUDUN GARA 49-50

287 23 0
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)

*DUBUN GAISUWA A* *GARE KU*

_Nazeefi yarima_
_Aunty hassy Atk_



*PG49-50*




______________________________

Bata wani jima ba a ciki ta fito tace ka shigo, tsaye tayi har ya fito daga motar suka shiga cikin gidan, ko da suka shiga ummah na zaune tsakar gida akan babbar ta barma da suke shimfidawa Tana sanye da hijab dinta

Da sallama ya shigo gidan ,Amal dai wucewa tayi wurin Anty Ramla da ta shiga daki
Durkusawa yayi ya gaida ummah ,ta Amsa a kunyace Nan yake cewa Abbah fa tace be dawo ba , shiru su ka danyi na minti biyu ,saboda rashin sabo ,kudi ya Ciro be San ko nawa bane ya aje da sauri yace ummah se da safe,cewa tayi ka dauki kudin ka Allah
Yace A'a ummah wadannan ma ba yawa ai,godiya ta mishi ,ya fita gidan

Amal ta kwalawa Kira se gata ta fito Nan ummah tace "wuce Yana can Yana jiranki, Kuma ki masa godiya wannan hidimar tayi yawa ma ga kayan da ya siyo ga kudi Kuma ya bayar ,ita dai Amal tuni ta turo Baki saboda Bata so tafiya yanzu ba ko Abbanta Bata gani ba

Lura da yadda ta Bata fuskarta yasa ummah ta dauko talkamen da ke gefenta ,ai da gudu Amal ta nufi hanyar fita ,ummah tace ja'ira da ki tsaya Mana

Koda ta fita Yana cikin mota ,zagayowa tayi ta shiga dayan bangaren ta zauna sannan ta rufo kofar waya yake koda ta shigo katse wayar yayi ya juyo Yana kallonta duk ta wani hade Rai,cewa yayi

"Lafiya kika fito Rai bace?"

Cike da shagwaba Amal tace "to ba ummah ce ta koro Ni ba bayan ko Abbah ban gani ba"

Gani yayi shagwabar ta Bata kyau sosai har yaso ya saki murmushi ganin Tana kallon sa sai ya kanne be yi ba , se cewa yayi

"Shine kike wannan fushin ,ai kuwa kinja ma kanki da Zan kawo ki kafin Ramla ta koma Ammah na fasa "

Da sauri ta wani rike mai hannu tace

"Dan Allah yaya kayi hakuri na Dena fushin ma"
Tunda ta rike mai hannu ya jisa wani iri, itama ganin yayi shiru se ta dago taga yadda ta wani rike masa hannu se ta saki hannun ta gyara zamanta a kan kujerar,shima daidaita kansa yayi yaja motar suka nufi gida Koda suka je gida kowa dakinsa ya nufa kasancewar tun kafin Anty Ramla ta tafi sukayi dinner..

Haka dai zaman nasu ya ci gaba da kasancewa ,a yanzu dai Amal Bata da wata damuwa , kasancewar yanzu Tana da waya Tana debe Mata kewa sosai,shima farouk tun Yana karyata kansa har yazo ya yadda da ya fada son matar sa se dai har yanzu ya kasa fada Mata,
A ganin sa har yanzu yarinya ce Bata gama mallakar hankalin kanta ba, Ana cikin haka ne kuwa tafiyar shi zuwa Cairo yin wani Kos na dabarun yaki ta taso ,Allah da ikonsa a lokacin har ya nemar ma Amal wata makaranta da ake Kira *BETTER QUEEN INTERNATIONAL SCHOOL*.
Anan sardauna creasent , kasancewar Basu da nisa da gidan mahaifansa duk wani Shirin school babu Wanda be Mata Dan har ta fara zuwa ma

Ita dai Amal taga shige da fice da yake yau a gidan yayi yawa,Ashe Yana ta kokarin daidaita abubuwa ne yau jirgin karfe Tara ze bi ,Ammah har zuwa wannan  lokacin Amal Bata San bidirin da ake ba ,ta na zaune bayan tayi sallar la'asar a falo se gashi ya fito ya nemi kujera ya zauna ya tsura Mata Ido Yana ta kallo , ta kasan Ido taga Yana kallonta Dan haka taki kallon sashin da yake,saboda ta lura a 'yan kwanakin Nan da sun hadu wani mayen kallo yake binta da shi

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now