ANYI GUDUN GARA 61-62

356 26 4
                                    

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*AN YI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)

*PG 61-62*

________________________________

Ko da na koma dakin bayan wasu awwani da suka shude,Yaya farouk na isko rungume da Amal da ko numfashi Bata yi kamar mattaciya ,se sabbatu yake zubawa Yana cewa"princess Allah ya saki Aljannar fiddausi,Dama ance maza ke daga kafa mace ta shiga Aljannah to ni na daga Miki tawa princess ,Jin ko motsin fitar Numfashin ta ba ya ji yasa hannun sa ya Kara a hancinta yaji shiru ,mikewa yayi da sauri ya aje ta ya nufi bathroom ruwa ya debo ya fito da sauri ya zauna bakin gadon ya aza kanta a cinyarsa ya shiga shafa Mata Ammah shiru kake ji take hankalinsa ya tashi ,da sauri ya tashi ya mayar da kayan jikinsa ,ita Kuma wata doguwar Riga ya samo cikin kayanta ya saka Mata,ganin yadda jini ya Bata bedsheet din ba karamin daga masa hankali yayi ba

"Hattara 'yan matan zamani a kula da Kai a rike mutuncin Kai har aje gidan miji Dan shine mutunci ki a idon miji,duk wadda ke cewa Wai ba'a gane wa ko kinyi aure,wannnan karyane Dan mazan yanzu sun San komai, ki kame kanki ,ki tsarkake zuri'ar ki duk macen da ta zubar da mutuncin ta kafin taje gidan miji,to mijin nan baze taba ganin kimar ki ba Allah ya shiryar da mu".

Ameen

Haka Nan ya samu ya saka Mata rigar ,makullin motar sa ya fita ya dauko a daki ,se da yaje ya bude motar da hanzari ya zo ya dauke ta ya sata bayan kujera kafin yaja motar da wani irin gudu,lokacin da ze fita , khaleel ya ga sadda ya fita ,ganin irin gudun da yake yasa yayi tunanin ba lafiya ba bayan sa yabi

Wata private hospital ya nufa da ita Yana zuwa emergency aka nufa da ita
Tsaye yayi a wurin ya Kai ya kawo ji yayi an dafa bayan sa Yana juyowa ya ga khaleel ne ,kalon sa yayi yace farouk lafiya kuwa

Shiru yayi kafin yace "my wife ce Bata da lafiya"

Shiru yayi Yana kallon sa Yana tunanin yaushe farouk ya fada ciki ne har yake kiranta wife ,bangarar da tunanin yayi yace
"Tana Ina ?"

"Sun shiga da ita ciki ne"
Farouk ya fada

Jawo sa khaleel yayi suka zauna kan wasu kujeru dake jere a wurin ,sannan ya ce "ka kwantar da hankalinka insha'Allah zata samu sauki

Amin farouk yace

Shi dai khaleel shiru yayi Yana tunanin meke faruwa

A can ciki kuwa da farko wasu nurses ne suka fara attending dinta ganin abun yafi karfin su  jini kawai ke fito Mata yasa
suka Kira  Dr Kamal ayagi dama shine on duty da sauri yazo ya fara kula da ita har ya samu nasar tsayar da jinin ,sannan ya Mata dinki ,Alluran barci masu karfi ya Mata yasa suka Kai ta dakin da za'a kwantar da ita

Fitowa yayi Yana goge gumin da ya tsatsafo Masa a goshi ,da sauri farouk ya nufi doctor din Yana cewa"Doctor ya jikinta ta farfado"

Kallon sa doctor din yayi ganin sa a Riki ce yasa ya ce "eh ta farfado Ammah ka same ni office Dina"


Ya wuce, bin bayan doctor din yayi shida khaleel ,har sun shiga sun zauna ,doctor din ya kalle su yace"patient din da ka kawo miye alakarka da ita?"

"Matata ce"
Yace,kallon khaleel  yayi yace wannan fa

"Abokina ne"

To ko zaka Dan bamu wuri doctor yace ma khaleel

Har farouk ze yi magana da sauri khaleel ya katse sa yace"Bari na fita ,ai doctor gaskiya ya fada "

Fita yayi kafin doctor ya juyo kan khaleel yace "yawwa matar ka ce kace ko,me yasa baka bita a hankali ba ,ba ka San irin wannan zuwan da ka Mata ze sa ta tsorata da Kai ba har ma ta fara gudunka,kaga yanzu ba karamin rauni ta ji ba Dan har dinki se da aka Mata

Farouk se yanzu yake Jin haushin abun da yayi na kin binta a hankali da be yi ba,shi Kam Ina ze sa ransa in ta guje sa saboda wannan dalilin


katse masa tunani doctor yayi ganin yadda duk ya ji kunyar abunda ya faru cewa yayi ya sunanka

"Captain farouk Bashir maradun"

"Kai soja ne"

"Eh"

Doctor murmushi yayi Dan farouk ya saki jikin sa yace"to ba filin yaki bane fa ka dinga binta a hankali ,Mata se da lallashi,sannan yanzu mun Bata gado har se ta fara jin sauki zamu sallameta,Kuma ko kun koma gida ka Bata lokaci har se ta warke sosai"

"To " yace,sannan suka yi musabiha da doctor din suka fito tare ya nuna masa dakin da'aka kwantar da ita

Shiga dakin suka yi shida khaleel Tana kwance tayi wani fayau da ita har Rama yaga ta masa ,ganin dare yayi yasa khaleel ya Masa sallama akan gobe zasu dawo da Matarsa ,saqo ya basa akan akawo mishi wasu kayansa da bargo sallama suka yi ya tafi

Dawowa yayi gafen gadon ya dauki hannunta ya saka cikin nasa ji yake wata zazzafar kaunar ta na shigar sa, dukawa yayi ya sunbaci goshinta kafin ya tashi ya nufi bathroom din dake dakin wankan tsarki yayi ya fito,Koda ya fito ya tarar an kawo Masa kayan daukar jallabiyya yayi yasa,ya shimfida dadduma ya tada sallah ,ya dade Yana nafila har kusan 2:30 sannan ya kwanta

Da Asuba massalacin asibitin yaje yayi sallah sannan ya dawo ,har lokacin Bata farka ba Dan se da ya leka ta
Zama yayi ya dauko wayar sa ya Kira ummee bayan sun gaisa ne ya ce Mata suna Asibiti Amal Bata da lafiya
Nan ta balbale sa da fada akan me be Kira tun jiya ba ,Nan yace ai da Daddare ne ,Nan ta tambaye shi wane Asibiti ya fada Mata sallama suka yi ya aje wayar

Har yanzu akwai bacci a idon sa Dan haka ya kwanta a dayan gadon Nan take bacci ya dauke sa

Karfe bakwai na safe ummee ta iso Asibitin ita da Al'amin da ya dauko Mata basket din abinci dakin suka shiga suka tarar da harshi me jinyar bacci yake

Al'amin ne ya fara taba sa yana cewa "Yaya"
Firgigit ya farka dama ba yada nauyin bacci tashi yayi ganin ummee Nan ya gaida ta ta Amsa tambayar sa me jiki tayi yace taji sauki Ammah har yanzu bata farfado ba

Ummee ce tace "me ke damun ta ne?"

Shiru farouk  yayi ya rasa me ze ce ,ganin yadda ta tsare shi da Ido ya tsinci kansa da cew"zazzabi ke damun ta"

"Allah ya Bata lafiya" ummee tace yace Amin

Yawwa to ga breakfast Nan kayi se ka koma gida kayi baccin anjima se ka dawo "to " yace, ya hada tea ya Dan Sha ,sannan ya masu sallama ya fita

Shima Al'amin be dade ba ya mata sallama ya  fita

Tana Nan zaune ba jimawa taga hannun Amal kamar Yana motsi,can Kuma A hankali ta fara bude idonta,dakin ta fara bi da Ido ,Nan ta gane Asibiti ne

Ummee ta karaso bed din tace"ya jikin ki 'yata ?"

Da kyar tace da "sauki"
Duk ji take jikinta kamar ba na ta bane

Nurses biyu ne suka shigo ,Nan suka ce ma ummee zasu taimaka Mata ne su gasa Mata jikinta

Da mamaki ummee tace "gashin lafiya zaku  Mata"

Nan nurse ta shiga ma ummee bayanin abunda ya same ta"

Ita dai Amal ta sunkuyar da Kai kamar kasa ta bude ta shige take ji

Nan ummee tace to su hada ruwan ita zata taimaka Mata

Cikin ranta kuwa ta shirya fadan da zata ma farouk kan wannan abun da yayi,Akan mi baze bi matar sa ahankali ba,har se ya ji Mata ciwo............✍️


*Aysha galadima ce*


Vote
Comment
Share

ANYI GUDUN GARAWhere stories live. Discover now